'Yan Biyafara Sun Taru Sun Harzuka bayan Daure Nnamdi Kanu a Sokoto

'Yan Biyafara Sun Taru Sun Harzuka bayan Daure Nnamdi Kanu a Sokoto

  • Wasu kungiyoyin gwagwarmayar Biyafara sun yi taron manema labarai a Imo kan hukuncin da aka yanke wa Nnamdi Kanu
  • Kungiyoyin sun yi zargin cewa gwamnatin tarayya ta karya yarjejeniyoyin ƙasa-da-ƙasa kan 'yancin dashugaban IPOB, Kanu ke da shi
  • A yayin taron, sun ce tsare Kanu a jihar Sokoto ma ya ƙara musu kuzari wajen ci gaba da neman ‘yancin kafa kasar Biyafara

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Imo - Gamayyar kungiyoyin gwagwarmayar Biyafara ta bayyana cewa hukuncin da aka yanke wa jagoran IPOB, Nnamdi Kanu, na zaman gidan yari har abada, ba zai raunana muradinsu na neman kafa kasa ba.

Kungiyoyin sun bayyana hakan ne yayin wani taron manema labarai da suka gudanar a ranar Juma’a a birnin Owerri na jihar Imo.

Kara karanta wannan

Kuɗin da yawa: Gwamna Zulum ya faɗi biliyoyin Naira da ya kashe kan tsaro a 2025

Nnamdi Kanu a wani zaman kotu
Kanu a kotu a ranar da aka yanke masa hukunci. Hoto: Omoyele Sowore
Source: Twitter

Vanguard ta wallafa cewa kungiyoyin da suka shiga wannan gamayya sun haɗa da MASSOB, EPC, BHRI, BLC, BRF, BRO da kuma UBSE.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A cewar su, hukuncin da aka yanke wa Kanu ya ƙara haskaka matsalolin da suke ganin suna addabar siyasar Najeriya, musamman batun wariya da rashin adalci.

Shugaban MASSOB, Uchenna Madu, ne ya karanta matsayar gamayyar, inda ya jaddada cewa za su cigaba da fadi-tashi.

Matsayar kungiyoyin Biyafara kan Nnamdi Kanu

Kungiyoyin sun bayyana cewa hukuncin da kotu ta yanke kan Kanu ya gaza bin hanyar adalci da ya kamata a bi a irin wannan lamari.

The Sun ta rahoto sun ce:

“Mun yi watsi da hukuncin da aka yanke wa Mazi Nnamdi Kanu, kuma mun ƙaryata shi gaba ɗaya.”

Sun ce gwamnatin Najeriya ta karya alkawuran da ta ɗauka a gaban majalisar dinkin duniya da tarayyar Afirka na mutunta yancin al’umma.

A cewar gamayyar:

Kara karanta wannan

Farin jinin Matawalle ya fadada, 'yan Kudu sun roki Tinubu game da kujerarsa

“An karya yarjejeniyoyin kare hakkin dan Adam da Najeriya ta sanya hannu a kansu a gaban ƙungiyoyin duniya.”

Za a cigaba da neman kafa kasar Biyafara

Kungiyoyin sun ce duk da hukuncin da aka yanke wa Kanu, gwagwarmayar neman kafa Biyafara ba za ta tsaya ba.

Sun ce:

“Daurin rai-da-rai ba zai taba dakatar da gwagwarmayar neman ‘yancin kai ba.”

Haka kuma gamayyar ta yi kira ga dukkan kungiyoyin fafutukar siyasa na yankin Kudu maso Gabas da su ƙara haɗa kai, domin a cewarsu rikicin siyasar Najeriya ya sake tsananta.

Shugaban IPOB, Nnamdi Kanu
Shugaban 'yan ta'addan IPOB, Nnamdi Kanu a kotu. Hoto: Omoyele Sowore
Source: Twitter

Batun tsare Nnamdi Kanu a Sokoto

Gamayyar ta ce tsare Kanu a nesa kamar Sokoto ba zai rage musu kwarin guiwa ba wajen neman kafa kasar Biyafara.

A cewarsu:

“Tsare Mazi Nnamdi Kanu a Sokoto ba zai taɓa rage mana kuzari ba; maimakon haka ya ƙara mana ƙarfin gwiwa.”

Shugaban IPOB, Kanu ya rusa kuka a kotu

A wani labarin, mun rahoto muku cewa shugaban 'yan ta'addan Biyafara, Nnamdi Kanu ya rusa kuka a kotu.

Kara karanta wannan

Bayan an ceto daliban Kebbi, ƴan siyasa fiye da 1500 sun fice daga PDP zuwa APC

Legit Hausa ta gano cewa shugaban 'yan awaren ya rusa kuka ne bayan yanke masa hukunci a kotun tarayya.

Biyo bayan bayyanar bidiyon kukan da Kanu ya yi, mutane da dama sun yi martani, wasu na cewa ba a masa adalci ba.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng