'An Buga Rikici da Matawalle a Ma'aikatar Tsaro kafin Badaru Ya Ajiye Aiki'

'An Buga Rikici da Matawalle a Ma'aikatar Tsaro kafin Badaru Ya Ajiye Aiki'

  • Rahotanni sun bayyana cewa murabus ɗin tsohon ministan tsaro, Badaru Abubakar, ba dalilin rashin lafiya kaɗai ba ne, illa rigimar da aka dade ana yi
  • An ce rikicin ya shafi yadda ma’aikatar ke aiki, ciki har da dabarun watsa labarai da aiwatar da manufofin tsaro a tsakanin manyan jami’an ma’aikatar
  • Wasu majiyoyi sun ce matsin lamba kan sake tashe-tashen hankula da garkuwa da dalibai a Arewa ya ƙara haddasa matsin lambar da ta kai ga murabus ɗin

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT, Abuja - Tsohon Ministan tsaro, Badaru Abubakar, ya yi murabus daga mukaminsa bayan kusan shekaru biyu yana aiki a gwamnatin Najeriya.

A sanarwar farko an bayyana cewa ya yi murabus ne saboda matsalolin lafiya, kamar yadda hadimin shugaban ƙasa, Bayo Onanuga, ya sanar.

Kara karanta wannan

Albishir da ministan tsaro ya fara yi ga 'yan Najeriya bayan shiga ofis a Abuja

Bello Matawalle da Badaru Abubakar
Tsohon ministan tsaro, Badaru da Bello Matawalle. Hoto: Mati Ali|Bello Matawalle
Source: Twitter

Sai dai binciken Punch ya nuna cewa dalilin da ya fi rinjaye shi ne rikicin da ya daɗe tsakanin Badaru Abubakar da karamin ministan tsaro, Bello Matawalle, abin da aka rika ɓoye wa kafofin watsa labarai na tsawon watanni. .

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Badaru, wanda aka naɗa a ranar 21, Agusta, 2023 bayan kammala wa’adinsa na gwamnan jihar Jigawa, ya fara da tsarin sabunta kayan aikin soji da inganta leƙen asiri da yaki da ta’addanci kafin barin ma'aikatar tsaro.

Dalilin sauke Badaru daga ministan tsaro

Majiyoyi daga cikin ma’aikatar tsaro sun tabbatar da cewa rikicin Badaru da Matawalle ya yi tsanani, duk da cewa suna nuna jituwa a bainar jama’a.

Wata majiya ta ce dangantakar ta kasance “maras dadi” na tsawon lokacin da suka yi tare. A cewarta, rikicin ya shafi wasu ayyuka, musamman sashen watsa bayanai ga jama’a.

Majiyar ta ƙara cewa haɗa ministoci biyu da ke da irin wannan irin sabani a ma’aikata daya lamari ne da bai kamata ya faru ba tun farko, domin ya haifar da rashin daidaito a tafiyar ma’aikatar.

Kara karanta wannan

Rikici a raɗin suna ya yi ajalin matashi a wani Bauchi

A karkashin haka ne majiyar ta ce rikici tsakanin Bello Matawalle da Badaru ne ya kai ga babban Ministan tsaro ya rasa kujerarsa.

Matsin lambar tsaro da kiran a cire Badaru

A makonnin baya, hare-hare da garkuwa da mutane sun sake ƙaruwa a yankuna da dama, lamarin da ya sa 'yan siyasa da jama’a suka fara kallon ma’aikatar tsaro a matsayin marar tasiri.

Sace ɗalibai mata a Kebbi da wasu da dama a Neja ya ƙara jawo kira ga sauya manyan shugabannin tsaron Najeriya a kwanakin baya.

Tsohon ministan tsaro, Badaru Abubakar
Tsohon ministan tsaro, Badaru Abubakar yana jawabi. Hoto: Mati Ali
Source: Twitter

Wasu masana sun fara kira ga shugaba Tinubu da ya sauya ministan tsaro, suna cewa ma’aikatar ba ta samun sakamakon da ake bukata ba.

Tasirin siyasar Matawalle a jam'iyyar APC

Majiyoyi daga cikin ma’aikatar sun ce Matawalle na da ƙarfi a siyasa kuma yana da kusanci da fadar shugaban ƙasa, wanda hakan ya sa ya fi rinjaye a ma’aikatar.

Legit ta rahoto cewa wasu jagororin jam’iyyar APC ma sun ce suna kallon Matawalle a matsayin ginshiƙi ga babban zaben 2027 a yankin Arewa maso Yamma.

Kara karanta wannan

Ba wasa: Janar Christopher Musa ya sha sabon alwashi bayan zama Ministan tsaro

Fani-Kayode ya kare Bello Matawalle

A wani labarin, mun kawo muku cewa tsohon minista, Femi Fani-Kayode ya goyi bayan karamin ministan tsaro, Bello Matawalle.

Femi Fani-Kayode ya bayyana cewa Bello Matawalle yana aiki tukuru saboda haka babu dalilin neman a sauke shi.

A bayanan da ya yi, Fani-Kayode ya yi kira ga Matawalle ya cigaba da aiki kamar yadda ya saba, ya manta da mahassada.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng