"Ya Tafi har Abada": Dangote Ya Yi Wa 'Yan Najeriya Sabon Albishiri
- Alhaji Aliko Dangote ya kai ziyara fadar shugaban kasa da ke Abuja inda suka tattauna da Mai girma Bola Ahmed Tinubu
- Hamshakin attajirin ya yi magana da 'yan jarida bayan kammala ganawarsu, inda ya tabo batun samar da man fetur a Najeriya
- Dangote ya nuna cewa matatar man da yake da ita a Legas ta magance matsalar da 'yan Najeriya suka dade suna fama da ita shekara da shekaru
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
FCT, Abuja - Hamshakin ɗan kasuwa kuma shugaban matatar Dangote, Aliko Dangote, ya yi magana kan samar da isashshen man fetur a Najeriya.
Aliko Dangote ya bayyana cewa zamanin dogayen layukan neman mai ya ƙare har abada a Najeriya.

Source: Getty Images
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Jaridar Daily Trust ta ce Dangote ya faɗi haka ne yayin da yake zantawa da manema labarai a Fadar Aso Rock bayan ganawa da shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, a ranar Juma’a.
Matatar Dangote na kai mai zuwa Turai
Dangote ya bayyana cewa a karo na farko, matatar mai ta Dangote tana samar da man fetur zuwa Turai da Amurka.
Ya kuma ce kuma sun rubuta wa Hukumar NMDPRA don sanar da ita cewa yanzu za su iya samar da lita miliyan 50 na man fetur kullum a Najeriya.
Dangote ya ce tattaunawarsa da shugaban kasa ta shafi tattalin arziki, yanayi da sauran muhimman bangarori, yana mai cewa irin wannan ganawa abu ne da suke yi lokaci zuwa lokaci.
Wane albishir Aliko Dangote ya yi?
"A Najeriya mun shafe shekaru tun 1972 muna fama da layukan neman mai. Amma kun san yanzu mun kawar da wadannan layuka. Ba sai an yi dogaro da shigo da mai daga waje ba.”
“A karo na farko, muna samar da mai ga Turai da Amurka. Mun rubuta wa NMDPRA mun kuma tabbatar musu cewa za mu iya samar da lita miliyan 50 a kullum.”

Kara karanta wannan
Tinubu ya tura sako na musamman ga Majalisa bayan tabbatar da nadin ministan tsaro
“Ku san yanzu babu wani dalilin da zai sa a sami layi. Ko da lokacin da muke gyaran matatar, babu layi. Don haka batun layukan mai ya zama tarihi ba zai sake faruwa ba, da izinin Allah.”
- Aliko Dangote
Dangote ya kuma ce kasahe makwabtan Najeriya ma ba za su kara fama da layi ba, rahoton jaridar TheCable ya tabbatar da labarin.
“Za su iya siya daga gare mu, amma ta hanyar hukuma. Zuwa watan Fabrairu, za mu iya samar da lita miliyan 15 zuwa 20 fiye da abin da Najeriya ke amfani da shi. Don haka dole ma mu fitar da ragowar.”
- Aliko Dangote

Source: Getty Images
Dangote zai fadada matatarsa
Game da tsare-tsaren da yake yi saboda gaba, Dangote ya ce:
“Daga 2028, za mu kai wannan matatar mu ta zama mafi girma a duniya. Za mu wuce Reliance, wadda ke da tace ganga miliyan 1.25 a kullum."
"Mu za mu kai ganga miliyan 1.4 a kullum. Mun riga mun kammala yarjejeniya, kuma gina karin sassan matatar zai fara kafin karshen Janairu.”
- Aliko Dangote
Dangote ya tabo batun mutuwar kamfanonin Arewa
A wani labarin kuma, kun ji cewa hamshakin attajiri, Aliko Dangote, ya yi tsokaci kan dalilin da ya sa kamfanonin Arewa suka ruguje.
Aliko Dangote ya danganta durkushewar masana’antun Arewa da tsawon shekaru na rikice-rikice kan manufofin gwamnati da rashin wutar lantarki mai inganci.
Fitaccen attajirin ya ce matsalar wutar lantarki ita ce ginshikin halakar da masana’antun da ake da su.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

