Farashin Kayan Abinci Ya Sake Ruguzowa ana Shirin Bankwana da 2025
- Farashin abinci ya fara raguwa a jihohi da dama yayin da ake dab da shiga bukukuwan Kirsimeti da sabuwar shekarar 2026
- Kudin wasu kayayyaki ya ragu sosai, amma a wasu wuraren hauhawar farashin jigilar kaya da ƙalubalen tsaro ya zama matsala
- A wannan rahoton, mun kawo muku bayanai game da farashin kayan abinci daga kasuwanni daban-daban a jihohin Najeriya
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
FCT, Abuja - A yayin da al’ummar ƙasar nan ke shirin shiga bukukuwan ƙarshen shekara, farashin kayan abinci da suka haɗa da shinkafa, gero, wake, doya da garin kwaki ya fara sauka a kasuwanni da dama.
Saukar farashin ya zo ne bayan watanni da dama da al’umma ke fama da tsadar kaya sakamakon cire tallafin man fetur da rashin tsaro a yankunan da ake noma.

Source: Getty Images
Rahoton Leadership ya nuna cewa kasuwannin Relief da World Bank a jihar Imo sun fara sauke farashin kayayyaki sosai, wanda ya sa jama’a ke samun sauƙin sayayya a wannan lokaci.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Haka zalika jihohi irin su Legas, Delta, Bayelsa, Sokoto, Neja, Yobe da Gombe sun nuna wani yanayi na saukar farashi, sai dai kowane wuri da nasa ƙalubalen.
Saukar farashi a jihar Imo
A jihar Imo, farashin buhun shinkafa mai nauyin kilo 50 ya sauka daga N75,000 zuwa N60,000. Garin kwaki ya sauka daga N7,600 zuwa N5,000.
Rahotanni sun nuna cewa doyar da ake sayarwa a kan N2,500 ta koma N1,900, haka nan wake ya sauka daga N34,000 zuwa N30,000.
Farashi ya sauka a Sokoto da Neja
A kasuwannin Binji, Bodinga da Gada da ke Sokoto, shinkafar ketare na tsakanin N55,000–N57,000, yayin da farshin shinkafar gida ya koma N92,000.
A jihar Neja kuma, ambaliya, hare-haren ‘yan bindiga da rashin tallafin gwamnati sun yi wa noma illa, lamarin da ya sa ba a sami saukar farashi sosai ba.
Yadda farashi ya ke a Yobe da Gombe
Rahotanni sun nuna cewa a jihar Yobe, saukar farashin ya shafi amfanin gona sosai, musamman saboda ana lokacin girbi.
A jihar Gombe, farashin masara, gero, shinkafa da wake ba su tashi ba. Babangida Bello da ke sayar da kayan masarufi a babbar kasuwar Gombe ya shaidawa Legit Hausa cewa:
"A gaskiya an samu sauki sosai a bana. An samu sauki a farashin taliya, manja, man gyada da sauran kayan masarufi.
"Sai dai kamar Indomie ne dai ba ta sauka ba a halin yanzu."
Saukar farashi a Legas, Delta da Bayelsa
A Mushin da Daleko a jihar Legas, farashin shinkafa ya yi kasa sosai, inda buhu yanzu yake a N54,000 daga N75,000 da aka rika sayarwa watanni baya.
A Asaba a jihar Delta, yawancin kayayyaki sun yi kasa, amma masu saye da sayarwa sun koka da ƙarancin kuɗin da ke hannun jama’a.
Tumatur ya koma N4,000 daga N5,000, shinkafa tana tsakanin N60,000 zuwa N65,000, wake kuma N50,000 bayan ya kai N90,000 a da.

Source: Facebook
A Yenagoa na Bayelsa, farashin shinkafa, wake da garin kwaki ya dan ragu, amma doya, manja, kifi da nama sun tsaya cak saboda matsalolin hanyoyi da tsadar jigilar kaya daga Arewa zuwa Kudu.
Farashin abinci ya yi kasa a Benue
A wani labarin, mun kawo muku cewa wasu 'yan kasuwa sun karya farashin kayan abinci a sassan a jihar Benue.
Sai dai lamarin ya bakanta ran wasu manoma, suna cewa saukar farashin na barazana ga harkokinsu a Najeriya.
Masana tattalin arziki sun gargadi gwamnatin Najeriya da cewa karyewar farashin kayan abinci zai yi illa ga noma.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Asali: Legit.ng


