Shettima, Manyan Kasa Sun Dura Jigawa Bikin Cikar Sarkin Gumel Shekara 45 a Mulki

Shettima, Manyan Kasa Sun Dura Jigawa Bikin Cikar Sarkin Gumel Shekara 45 a Mulki

  • Mataimakin shugaban ƙasa, Sanata Kashim Shettima ya ce gwamnati za ta ci gaba da kare martabar sarakunan gargajiya da matsayinsu a al’umma
  • Ya jaddada cewa kujerun siyasa na da wa’adin ƙarewa amma sarautun gargajiya na dawwama kuma suna kusa da talakawa fiye da kowane matsayi
  • Shettima ya taya mai martaba Sarkin Gumel murnar cika shekara 45 a kan karaga tare da yabon rawar da Sultan tke akawa wajen haɗa kan ’yan kasa

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Gumel, Jigawa – Mataimakin shugaban ƙasa, Sanata Kashim Shettima ya tabbatar da cewa gwamnatin shugaba Bola Tinubu za ta riƙa kare martabar sarakunan gargajiya da kuma tabbatar da dorewarsu.

Shettima ya bayyana haka ne a bikin cika shekaru 45 na mulkin Sarkin Gumel, Mai Martaba Alhaji Ahmed Mohammed Sani II, da kuma kaddamar da sabon masallacin Juma’a a karamar hukumar.

Kara karanta wannan

Bello Matawalle ya samu kariya ana tsaka da kiran Tinubu ya kore shi

Shettima a fadar Sarkin Gumel
Shettima, Sultan, a fadar Sarkin Gumel. Hoto: Kashim Shettima
Source: Facebook

Hadimi a fadar shugaban kasa, Stanley Nkwocha ya wallafa a X cewa Shettima ya ce sarakunan gargajiya sune mafi kusa da al’umma, suna tsare tarihi, al’ada da zaman lafiya.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Shettima: “Dole ne mu girmama sarakuna”

Mataimakin shugaban ƙasar ya jaddada cewa mulkin siyasa yana da wa’adin ƙarewa, sarautun gargajiya na ci gaba da gudana ko bayan gwamnati ta sauya.

Shettima ya ce:

“Mulkin siyasa yana ƙarewa bayan shekara takwas, amma masarautu suna nan daram. Saboda haka dole mu girmama su, mu kula da su, kuma mu kare wannan gadon namu.”

Ya taya Sarkin Gumel murnar zagayowar shekaru 45 a kan karaga, yana addu’ar Allah ya tsawaita zamaninsa har ma ya shaida zagayowar shekaru 50 da 100 cikin koshin lafiya.

Ya bayyana tarihin masarautar Gumel tun daga kafuwarta a 1750 ta hannun Danjuma, yana mai cewa Sarkin yanzu shi ne na 13.

Kara karanta wannan

An barke da farin ciki a Gaza yayin da Falasdinawa 54 suka daura aure

Ya kuma tuna cewa mai martaba, Alhaji Ahmed Mohammed Sani II, ya yi aikin gwamnati a matsayin kwamishina a zamanin Abubakar Rimi kafin hawansa sarauta.

Shettima ya yaba wa Sultan kan hadin kai

Shettima ya yi tsokaci kan rawar da Sarkin Musulmi, Alhaji Muhammad Sa’ad Abubakar III, ke takawa wajen haɓaka zaman lafiya da haɗa kan ’yan Najeriya.

Ya ce:

“Mai Alfarma Sultan shugaba ne da ya cancanci a yi koyi da shi. Shi alamar haɗin kanmu ne, kullum yana yawo ƙasar nan domin hada kai. Allah ya ƙara masa lafiya da tsawon rai.”

A nasa jawabin, Gwamna Namadi ya gode wa Shettima bisa halartar wannan gagarumin taro, yana mai cewa hakan alamar goyon bayan gwamnati ne ga Gumel da al’ummar jihar.

Yadda aka yi sallah a sabon masallacin Gumel
Shettima, Sarkin Musulmi, gwamna Namadi a Masallacin Gumel. Hoto: Kashim Shettima
Source: Facebook

Shi ma Sultan ya yi kira ga ’yan Najeriya da su ƙara zama ɗaya, su yi hakuri da juna, su girmama bambance-bambancen addini da al’ada domin ci gaban ƙasa.

Manyan baki da suka hallara Gumel

Bikin ya samu halartar manyan jami’an gwamnati da fitattun mutane ciki har da Sanata Ibrahim Hassan Hadeija, Ministan Noma, Abubakar Kyari, Farouk Adamu Aliyu, Mataimakin Gwamnan Jigawa, Aminu Usman Gumel.

Kara karanta wannan

Gwamna Abba Kabir ya ziyarci wuraren da aka yi artabu da 'yan bindiga a Kano

Haka kuma akwai sarakuna daga Machina, Dutse, Hadejia, da sauran manyan baki daga majalisar zartarwa ta jihar da ’yan majalisar tarayya.

Shettima ya je jana'izar Dahiru Bauchi

A wani labarin, mun kawo muku cewa mataimakin shugaban kasa, Sanata Kashim Shettima ya halarci jana'izar Sheikh Dahiru Usman Bauchi.

Sanata Kashim Shettima ya bayyana cewa ya wakilci shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu ne a wajen sallar jana'izar.

Gwamnoni da dama ciki har da Abba Kabir Yusuf na Kano, Inuwa Yahaya na Gombe, da Umaru Bago na Neja sun hallara.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng