Gwamna Radda Ya Yabi Sulhu da 'Yan Bindiga, Ya Fadi Amfanin da Aka Samu a Katsina
- Gwamnan Katsina, Dikko Umaru Radda na ci gaba da ziyarar ran gadi a kananan hukumomi 34 da ake da su a jihar
- Dikko Radda ya yaba kan zaman lafiyan da aka samu sakamakon sulhun da aka kulla da 'yan bindiga duk da ba da gwamnatinsa aka yi ba
- Gwamnan ya bayyana cewa sulhun ya jawo an samu raguwar hare-hare a yankunan da ke fama da matsalar rashin tsaro
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
Jihar Katsina - Gwamnan jihar Katsina, Dikko Umaru Radda, ya yi magana kan batun sulhun da wasu al'ummomi suka kulla da 'yan bindiga.
Gwamna Radda ya yabawa al’ummomin da suke fama da matsalar tsaro saboda kulla yarjejeniyar zaman lafiya da ‘yan bindiga a yankunansu.

Source: Facebook
Jaridar The Guardian ta ce Gwmana Radda ya bayyana hakan ne a ranar Juma’a yayin ziyararsa a kananan hukumomin Batsari da Danmusa, a ci gaba da zagayen da yake yi a fadin jihar.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Gwamna Radda ya shiga daji
Gwamnan ya ce yarjejeniyar da al’ummomin suka kulla da ‘yan bindiga ta fara haifar da sakamako mai kyau, musamman a yankunan da suka fi fuskantar matsalar rashin tsaro.
A matsayin hujja, gwamnan ya bi hanyar da ta ratsa dajin Danburum, wani daji da aka jima ana tsoron shiga saboda rashin tsaro.
Wannan daji ya kasance maboyar ‘yan bindiga tsawon shekaru, inda daruruwan mutane suka rasa rayukansu.
Sai dai, kokarin gwamnatin jihar da al’umma ta sa tsaro ya fara dawowa a dajin, harkokin noma da wasu ayyukan yau da kullum kuma na sake farfadowa.
A yayin zagayen, motocin gwamnan sun tsaya a tsakiyar dajin, wasu daga cikin mutanen cikin tawagarsa suka sauka suka yi tafiya a kafa cikin daji, suka tattaro wasu ‘ya’yan itatuwa suka ci.
Wata majiya cikin tawagar ta ce daga baya an ba gwamnan da wasu manyan baki daga cikin ‘ya’yan itatuwan.

Kara karanta wannan
Ba wasa: Matakin da Gwamna Abba zai dauka don dakile hare haren 'yan bindiga a Kano
Me Radda ya ce kan rashin tsaro?
Gwamnan ya ce duk da cewa jihar ba ta kai ga samun cikakken tsaro ba, yarjejeniyar zaman lafiyar ta haifar da gagarumin sauki a yankunan da ke fama da matsalar, jaridar The Punch ta dauko labarin.
“Muna godiya ga Allah cewa wannan yarjejeniyar zaman lafiya da al’ummomi suka shirya tana haifar da sakamako mai kyau sosai."
"A ‘yan kwanakin nan ban samu rahoton kai hari ko daya daga hukumomin tsaro ba kamar yadda na saba samu.”
- Gwamna Dikko Umaru Radda

Source: Facebook
Gwamna Radda ya kara da cewa hukumar gwamnati da ke daukar nauyin kula da jinya da sauran kudaden magani na mutanen da harin ‘yan bindiga ya rutsa da su ta sanar da shi cewa a watan Nuwamba ba ta kashe ko Naira miliyan 2 ba.
Ya bayyana cewa a baya, hukumar tana kashe fiye da Naira miliyan 40 a kowane wata wajen kula da wadanda suka jikkata.
Haka kuma tallafin da ake ba wadanda aka ceto daga garkuwa da kuma iyalan mutanen da aka kashe ya ragu sosai saboda rage yawan hare-hare.
'Yan bindiga sun sako mutanen da suka sace
A wani labarin kuma, kun ji cewa 'yan bindiga sun sako wasu mutanen da suka yi garkuwa da su a Katsina bayan kulla yarjejeniyar sulhu.
'Yan bindigan sun sako mutane 45 wadanda aka mika su ga hukumomi a karamar hukumar Bakori ta jihar Katsina.
An dai sako mutanen ne ta hannun daya daga cikin manyan jagororin 'yan bindiga, Alhaji Isiya Kwashen Garwa, a wani kauye da ke kan iyaka tsakanin Faskari da Bakori.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Asali: Legit.ng

