Aliko Dangote Ya Fadi Dalilin Rugujewar Kamfanonin Arewa
- Atiku Abubakar da Aliko Dangote sun yi kira ga Arewa ta san inda ta dosa domin kauce wa durkushewa ta fuskar tsaro da tattalin arziki
- Dangote ya danganta rugujewar masana’antun Arewa da rikice-rikicen manufofin gwamnati da wasu abubuwan da suka shafi lantarki
- Atiku ya tunatar da tsarin da Sardauna ya kawo da ya shafi ilimi, noma da masana’antu tare da gargaɗin cewa ya kamata a koma gare su
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Kaduna – A wajen bikin cika shekaru 25 na kungiyar Arewa Consultative Forum (ACF), tsohon mataimakin shugaban ƙasa Atiku Abubakar da ɗan kasuwa Aliko Dangote sun aika da saƙonni masu nauyi ga shugabannin Arewa.
Bayanan da shahararrun mutanen suka yi game da Arewa sun shafi tabarbarewar tsaro, tattalin arziki da tsarin ilimi a Arewacin Najeriya.

Source: Getty Images
Vanguard ta rahoto cewa Atiku ya ce Arewa na fuskantar haɗari idan ba ta sake duba tsarin ci gabanta ba, yana mai cewa rashin tsari da gurguncewar ilimi na jefa yankin cikin mummunan yanayi.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Atiku ya nemi Arewa ta farka daga barci
Atiku ya ce Arewa ba za ta iya ci gaba da sakaci ba a lokacin da matsalolin tsaro, talauci da durkushewar ilimi suka yi wa yankin katutu.
Ya wallafa a Facebook cewa:
“Idan ba a farka ba Arewa za ta ci gaba da nutsewa cikin rashin tsaro.”
Ya yaba wa shugabannin ACF na baya kan jajircewar da suka yi, amma ya ce lokaci ya yi da za a daina dogaro da abin da ya wuce a koma ga nazari da dabarun cigaba.
Ya tuna yadda tun shiga gwamnati a 1999 suka kafa kwamitin sulhunta siyasa ƙarƙashin Sarkin Ilorin, Ibrahim Sulu-Gambari, wanda daga baya ya haifi ACF.

Source: Depositphotos
Atiku ya ce an kafa ACF ne domin haɗa kan Arewa da kuma farfaɗo da ci gaban da Sardauna ya yi nuni da shi tun 1961—ilimi, noma da masana’antu.
Atiku ya ce:
“Idan akwai wani lokaci da Arewa ke bukatar ta haɗa kai, to yanzu ne.”
Dangote ya fadi dalilan rugujewar kamfanonin Arewa
A nasa bangaren, Aliko Dangote ya danganta durkushewar masana’antun Arewa da tsawon shekaru na rikice-rikice kan manufofin gwamnati da rashin wutar lantarki mai inganci.
Ya bayyana cewa ya taɓa bai wa kamfanin Arthur Andersen binciken dalilin rugujewar manyan masana’antun Arewa, cikin su har da masana’antar yadi.
Dangote ya ce matsalar wutar lantarki ita ce ginshikin halakar da masana’antu, yana mai cewa:
“Idan ba wutar lantarki, babu cigaba.”
Shahararren ɗan kasuwar ya danganta yawaitar ’yan fashi, rashin aikin yi da lalacewar matasa da sakaci wajen gina masana’antu da samar da abubuwan more rayuwa a cikin matsalolin yankin.
Ya yi kira ga shugabannin Arewa su soma samar tsari mai ma’ana da zai haɗa neman ilimi, masana’antu da noma tare da shiri na dogon lokaci domin farfaɗo da yankin.
Dangote ya gargaɗi cewa:
“Idan ba a tashi tsaye ba, matsalolin da ke addabar Arewa za su shafi kowa, ko mai laifi ko marar laifi.”
Dangote ya ki sayen matatun NNPCL
A wani labarin, mun kawo muku cewa attajirin Najeriya, Alhaji Aliko Dangote ya ce ba zai saye matatun NNPCL ba.
'Dan kasuwar ya bayyana haka ne yayin da ake masa tambayoyi game da fadada matatarsa a jihar Legas.
An nemi ya saye matatun man Najeriya na kamfanin NNPCL ya yi aiki da su maimakon fadada matatarsa amma ya ce a'a.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng


