Tsugunne ba Ta Kare ba: Rikicin Natasha da Akpabio Ya Dawo Sabo

Tsugunne ba Ta Kare ba: Rikicin Natasha da Akpabio Ya Dawo Sabo

  • Za a fafata shari'a tsakanin shugaban majalisar dattawa, Godswill Akpabio da Sanata mai wakiltar Kogi ta Tsakiya, Natasha Akpoti-Uduaghan
  • Sanata Godswill Akpabio ya yanke shawarar shigar da kara gaban kotu kan zargin da Sanatar Kogi ta yi masa na yunkurin cin zarafinta
  • Natasha ta yi farin ciki kan karar da shugaban majalisar dattawan ya shigar da ita, inda ta nuna cewa hakan ya sanya ta samu wata babbar dama

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

FCT, Abuja - Shugaban majalisar dattawa, Godswill Akpabio, ya shigar da Sanata Natasha Akpoti-Uduaghan kara gaban kotu kan zargin bata suna.

Sanata Godswill Akpabio ya shigar da karar ne a gaban babbar kotun tarayya da ke birnin tarayya Abuja.

Akpabio ya shigar da Natasha kara gaban kotu
Shugaban majalisar dattawa, Godswill Akpabio da Sanata Natasha Akpoti-Uduaghan Hoto: Godswill Obot Akpabio, Natasha H Akpoti
Source: Facebook

Sanata Natasha Akpoti-Uduaghan, wacce ke wakiltar Kogi ta Tsakiya, ta tabbatar da shigar da karar ne a wani rubutu da ta yi a shafinta na Facebook a ranar Juma’a, 5 ga watan Disamban 2025.

Kara karanta wannan

Rashin tsaro: NLC na shirin zazzafar zanga zanga a dukkan jihohin Najeriya

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Natasha ta yi murna kan karar Akpabio

Ta bayyana cewa shigar da karar da Akpabio ya yi, zai ba ta damar tabbatar da zargin da ta yi a kansa.

Sanata Natasha ta bayyana farin cikinta cewa shugaban majalisar dattawa ya bi hanyar zuwa kotu, tana mai cewa a baya an hana ta damar gabatar da shaidun ta.

“A yau 5 ga watan Disamba 2025, na karɓi sabuwar karar bata suna inda ake neman Naira biliyan 200 da Sanata Godswill Akpabio ya shigar a kaina kan zargin cin zarafi.”
“Ina farin ciki cewa Akpabio ya dauki matakin zuwa kotu, domin kwamitin ɗa'a na majalisar dattawa ya ki sauraron korafina, bisa hujjar cewa matar Akpabio ta riga ta shigar da kara kan bata suna a kaina, don haka ba za su saurari lamarin da ke gaban kotu ba.”
"Hakan ya sa ba zan iya zuwa kotu ba saboda bisa dokokin majalisa, dole ne na gabatar da korafina a gaban kwamitin da'a (kwamitin da ya ba da shawarar dakatar da ni ba bisa ka'ida ba)."

Kara karanta wannan

Shari'ar Musulunci: MURIC ta kalubalanci Amurka, ta faɗi abin da Musulmi za su yi

“A ƙarshe, yanzu na samu damar tabbatar da yadda aka ci zarafina da kuma yadda kin amincewata ga bukatunsa ya jawo aka taso ni a gaba wajen zubar mini da mutunci."

- Sanata Natasha Akpoti-Uduaghan

Sanata Natasha za ta fafata da Akpabio a kotu
Sanata Natasha Akpoti-Uduaghan a zauren majalisa Hoto: Natasha H Akpoti
Source: Original

Yaushe za a fara shari'ar Natasha da Akpabio?

Sanatar ta wallafa kwafin umarnin alkalin kotun, U.P. Kekemeke, wanda ya bayar da izinin a mika mata takardun shari’ar.

An bayar da umarnin ne tun ranar 6 ga watan Nuwamba, kuma za a fara shari’ar ne a ranar, 21 ga watan Janairu, 2026.

Sanata Natasha ta yi ta'aziyya

A wani labarin kuma, kun ji cewa Sanata Natasha Akpoti-Uduaghan ta yi ta'aziyyar rasuwar tsohon sanata a tsohuwar jihar Kwara, Sanata Isa Abonyi Abaro.

Sanata Natasha ta tura sakon ta'aziyya ga al'ummar Kogi ta Tsakiya bisa rasuwar sanatan wanda ya wakilci mazabar Okene/Okehi a tsohuwar jihar Kwara.

Marigayin dai ya bayar da gudunmawa a kan dokoki da manufofin da suka shafi ci gaban mazabarsa da walwalar al’ummar yankin.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng