Ministan Abuja Ya Fatattaki Shugaban Hukumar FCT IRS, Ya Fadi Wanda Zai Maye Gurbinsa
- Nyesom Wike ya tunbuke Michael Ango daga kujerar mukaddashin shugaban hukumar FCT-IRS nan take saboda wani dalili da ba a bayyana ba
- A wata sanarwa da hadimin Ministan harkokin Abuja ya fitar, Wike ya umarci babban jami'in hukumar ya karbi ragamar jagoranci daga hannun Ango
- Hukumar FCT-IRS na da matukar muhimmanci a harkar gudanarwa na Abuja saboda ita ce ke da alhakin tattara duk wasu kudaden shiga
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Abuja, Nigeria - Ministan Harkokin Babban Birnin Tarayya Abuja, Nyesom Ezenwo Wike ya yi gyara a hukumar tattara harajin FCT watau (FCT-IRS).
Wike, tsohon gwamnan jihar Ribas ya tsige shugaban rikon kwarya na Hukumar Tara Haraji ta FCT (FCT-IRS), Michael Ango, daga mukaminsa nan take.

Source: Twitter
Vanguard ta tattaro cewa an bayyana korar ne a yau Juma'a, 5 ga watan Disamba, 2025 a cikin wata takaitacciyar sanarwa da mai taimaka wa ministan kan harkokin yada labarai da kafafen sada zumunta, Lere Olayinka, ya fitar a Abuja.
Babban jami’in FCT-IRS ya karɓi mulki
A cewar sanarwar, Wike ya umarci jami’i mafi girma a FCT-IRS da ya gaggauta karɓar jagoranci domin ci gaba da gudanar da ayyukan wannan muhimmiyar hukumar ta tattara kudaden shiga a Abuja.
A rahoton da Daily Trust ta kawo, sanarwar ta ce:
“Ministan Babban Birnin Tarayya (FCT), Mista Nyesom Wike, ya tsige Shugaban Hukumar Tara Haraji ta Abuja (FCT-IRS) na rikon kwarya, Mr. Michael Ango, nan take.
"An kuma umarci jami’i mafi girma a hukumar da ya karɓi ragamar gudanar da FCT-IRS daga hannun Ango ba tare da wani bata lokaci ba.”
Me yasa Nyesom Wike ya kori Ango?
Sai dai sanarwar ba ta bayyana dalilin Wike na daukar matakin ba, lamarin da ya sa aka fara tantama da tambayoyi kan dalilin tsige Mista Ango daga kan mukaminsa cikin gaggawa.
Hukumar FCT-IRS dai tana da matukar hummanci a harkokin gudanarwa na birnin Abuja domin ita ce ke da alhakin tantance haraji, tara kudaden shiga
Haka zalika hukumar ce ke rubuta dun wani rahoton kudaden da ake biya ga gwamnatin Abuja, mama daga na haraji da sauran makamanansu.

Source: Facebook
Hukumar FCT-IRS na taka muhimmiyar rawa wajen samun kudaden da ake amfani da su a gudanar da al’amuran Babban Birnin Tarayya, kamar yadda Leadership ta rahoto.
Wike zai kwace filayen manya a Abuja
A wani rahoton, kun ji cewa hukumar gudunarwar birnin tarayya, Abuja ta fitar da sunayen mutane da hukumomi masu gidaje 1,095 da aka soke takardun mallakarsu.
Ta bayyana cewa za a fara aiwatar da matakan kwace filayen.bayan karewar wa’adin kwanaki 14 da aka ba wa masu kadarorin, wanda ya cika a ranar 25 ga Nuwamba, 2025.
Hukumar ta ce daga cikin jerin, kadarori 835 sun gaza biyan harajin da aka dora a kan gidaje ko filayensu, yayin da 260 suka gaza biyan kudin sabawa ka’ida da kuma kudin sauya amfani da ƙasa.
Asali: Legit.ng

