Wani Bam Ya Tarwatse da Mutane a Banki, An Samu Asarar Rayuka a Jihar Borno

Wani Bam Ya Tarwatse da Mutane a Banki, An Samu Asarar Rayuka a Jihar Borno

  • Rundunar ‘yan sanda ta tabbatar da cewa yara hudu sun mutu bayan fashewar wani bam da aka ce yaran sun dauko daga cikin bola
  • An rahoto cewa wani yaro dan shekara 12, Mustapha Tijja ya samu munanan raunuka kuma an kai shi asibitin FHI 360 NGO a Banki
  • Kwamishinan ‘yan sandan jihar Borno ya yi gargadi ga jama’a musamman yara da su guji wasa da abubuwan da ba su saba gani ba

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Borno - Rahotanni da muka samu na nuni da cewa wani abun fashewa da ake zargin bam ne ya tashi a karamar hukumar Bama, jihar Borno.

Yara hudu ne suka rasa rayukansu a fashewar bam din da ya afku a garin Banki, lamarin da ya jefa mutane a cikin tashin hankali.

Kara karanta wannan

Matashi 'dan shekara 17 ya lallaba ya kashe matar makwabcinsu cikin dare a Borno

Bam ya tarwatse da yara a jihar Borno, inda hudu suka mutu, daya ya jikkata.
Jami'in dan sanda da ke a sashen EOD ya na kokarin kwance wani bam da aka samu a gona a Borno. Hoto: @PoliceNG
Source: Twitter

Kakakin rundunar 'yan sandan jihar Borno, Nahum Daso, ya tabbatar da faruwar lamarin a sanarwar da ya raba wa manema labarai a ranar Juma'a, in ji rahoton Punch.

Bam ya tarwatse da yara a jihar Borno

Nahum Daso Kenneth ya sanar da cewa abin fashewar ya tarwatse ne a bayan tashar motar Banki da ke a gundumar Wajari.

A cewar sanarwar 'yan sanda, wadanda abin ya rutsa da su suna wasa da bam din ne, wanda ake zargin sun tsinto a bola, lokacin da ya tarwatse.

Sanarwar Nahum Daso ta ce:

"Rundunar 'yan sandan jihar Borno na sanar da al'umma faruwar wani mummunan lamari na tashin wani abun fashewa da ya faru a ranar 5 ga watan Disamba, 2025.
"Wannan abun fashewa ya tarwatse ne da misalin karfe 12:40 na rana a ]bayan tashar motar Banki da ke a gundumar Wajari, karamar hukumar Bama, jihar Borno.

Yadda yara suka tsinci bam, ya tarwatse

Kara karanta wannan

Shugaban kasa Bola Tinubu zai jagoranci babban taron jam'iyyar APC a Abuja

Kakakin rundunar 'yan sandan ya bayyana cewa wani mutumi, Babagana mohammed daga gundumar Wajari ne ya kai rahoton faruwar lamarin ga 'yan sanda da misalin karfe 3:00 na rana.

Bayan karbar rahoton, DPO na yankin Banki da tawagarsa, tare da hadin gwiwar sashen dakile tashin bama-bamai, suka gaggauta isa wurin da abin ya faru, in ji rahoton Premium Times.

Daso ya ci gaba da cewa wani yaro dan shekara 12, Mustapha Tijja ya samu munanan raunuka kuma an kai shi asibitin FHI 360 NGO da ke Banki, inda ake kula da lafiyarsa.

"Karin bincike ya nuna cewa yaron da ya ji rauni tare da abokansa hudu sun je bayan tashar motar ne suna wasa, inda wadanda suka rasu suke wasa da abin fashewar da suka tsinta a bola har ya tarwatse."

- Nahum Daso Kenneth.

'Yan sanda sun yi karin bayani game da bam din da ya tashi a jihar Borno.
Kwamishinan 'yan sandan Borno, Naziru Abdulmajid ya gargadi yara kan wasa da karafan da ba su saba gani ba. Hoto: @BornoPoliceNG
Source: Twitter

An fadi sunayen yaran da suka rasu

Wadanda suka rasu su ne Awana Mustapha, dan shekara 15; Malum Modu, dan shekara 14; Lawan Ibrahim dan shekara 12 da kuma Modu Abacha da shekara 12.

Kakakin rundunar 'yan sandan ya bayyana cewa zuwa yanzu an dawo da kwanciyar hankali a yankin, yayin da ake ci gaba da gudanar da bincike.

Kara karanta wannan

Kano: Gwamnati ta yi bayani kan dokar hana acaba, an yi sassauci a wasu yankuna

"Kwamishinan 'yan sanda, CP Naziru Abdulmajid, ya mika ta'aziyyarsa ga iyalan wadanda suka rasa raukansu, kuma ya gargadi mutane, musamman yara da su guji wasa da abun da basu saba gani ba."

- Nahum Daso Kenneth.

Bam ya tarwatse da 'yan firamare

A wani labarin, mun ruwaito cewa, dalibai bakwai sun jikkata, yayin da wani abin fashewa da ake zargin bam ne ya tashi da su a ranar 16 ga watan Satumba, 2025.

An ce abin fashewar (IED) ya tarwatse da yaran ne a makarantar firamare ta LEA, Ater Ayange a karamar hukumar Ukum, jihar Benue.

Fashewar ta auku ne misalin karfe 2:00 na rana, lokacin da yaran suka tarar da wani abu a cikin makaranta, suka fara wasa da shi ba tare da sanin cewa bam ba ne.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com