Albishir da Ministan Tsaro Ya Fara Yi ga ’Yan Najeriya bayan Shiga Ofis a Abuja

Albishir da Ministan Tsaro Ya Fara Yi ga ’Yan Najeriya bayan Shiga Ofis a Abuja

  • Sabon Ministan Tsaro, Christopher Musa ya yi magana jim kadan bayan shiga ofis a birnin tarayya wato Abuja
  • Janar Musa mai ritaya ya ce lokacin zubar da jinin wadanda ba su ji ba, ba su gani ba a Najeriya ya wuce a yanzu
  • Ministan ya sha alwashi inganta jin daɗin sojoji da iyalansu, yana mai cewa dole ne a ba masu sadaukarwa kulawa

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Abuja - Sabon Ministan Tsaro, Janar Christopher Musa mai ritaya, ya fara aiki bayan karbar rantsuwa daga Bola Tinubu.

Musa ya bayyana cewa lokacin zubar da jinin yan Najeriya ya zo ƙarshe inda ya yi alkawarin aiki tukutu kan tsaro.

Ministan tsaro ya dauki alkawari kan ta'addanci
Ministan tsaro, Christopher Musa. Hoto: HQ Nigerian Army.
Source: Facebook

Minista ya sha alwashi kan tsaro

Musa ya yi wannan jawabi ne a ranar Juma’a 5 ga watan Disambar 2025 yayin karɓar ragamar ofis a hedikwatar ma’aikatar tsaro da ke Abuja, cewar Vanguard.

Kara karanta wannan

Sulhu da 'Yan bindiga: Sheikh Gumi ya yi wa ministan tsaro, Janar Musa martani

Tsohon hafsan tsaro ya ce yana dawowa ne da cikakken goyon bayan Shugaba Bola Tinubu da kuma amanar da ’yan Najeriya suka ba shi.

A cewarsa, canji ba ya zuwa da maganganu kawai, sai dai ta hanyar aiki da jajircewa daga kowane ɗan ƙasa.

Ya jaddada cewa ’yan Najeriya suna da hakkin rayuwa ba tare da tsoro ba, yara su koma makaranta, manoma su koma gonakinsu ba tare da fargaba ba.

Musa ya ce kulawa da walwalar sojoji da iyalansu na da matuƙar muhimmanci, domin wanda yake sadaukar da rayuwarsa ga ƙasa ya cancanci girmamawa da kulawa ta musamman.

Ya bayyana ginshiƙai uku da zai gina ma’aikatar tsaro a kai ingantacciyar aiki, haɗin kai tsakanin rundunoni, da dogon hangen nesa. mai faɗi.

Ya kuma ce fasahar zamani, bayanai da harkar leƙen asiri za su zama tubalin sabuwar hanya da ake bi wajen kare ƙasa, tare da haɗa kai da abokan hulɗa na waje.

Kara karanta wannan

'Ina cikin aminci a Najeriya': Tsohon Firayim ministan Birtaniya kan tsaro

Ministan tsaro ya kama rantsuwa a Abuja
Ministan tsaro, Christopher Musa da Bola Tinubu. Hoto: Bayo Onanuga.
Source: Facebook

Gargadin da Janar Musa ya yi ga dakaru

Janar CG Musa mai ritaya ya gargadi jami’ai cewa ba za a yarda da rashin ladabi, cin hanci ko jinkirin aiki ba.

Ya ce idan aka yi kuskure, dole ne a gyara nan da nan ba tare da ɓoye komai ba, kamar yadda Daily Post ta ruwaito.

Tsohon sojan bayyana kwarin guiwar ma’aikatar da ke kawo gagarumin sauyi a harkar tsaro, yana mai kira ga duk ma’aikatan ma’aikatar sojoji da farar hula, su ba da gudummawa ba tare da jiran umarni ba.

Ya jinjinawa mahimmancin ma’aikatan, yana mai cewa su ne ginshikin tsari da tarihin ma’aikatar, saboda haka yana buƙatar jajircewarsu wajen fassara manufofin tsaro zuwa aiyuka da kasafin kuɗi masu inganci.

Musa ya yi kira ga ’yan Najeriya da su kasance masu haɗin kai da jajircewa wajen magance ƙalubalen tsaro, yana mai cewa aikin da ke gaba babba ne.

Kara karanta wannan

Ba wasa: Janar Christopher Musa ya sha sabon alwashi bayan zama Ministan tsaro

Minista ya magantu bayan shan rantsuwa

A baya, kun ji cewa shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya rantsar da Janar Christopher Musa (mai ritaya) a matsayin sabon Ministan tsaro.

Janar Christopher Musa zai kama aiki a matsayin Ministan tsaro bayan murabus din Mohammed Badaru Abubakar.

Sabon Ministan tsaron kasar ya alwashin cewa zai yi duk mai yiwuwa domin ganin cewa tsaro ya samu a Najeriya.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.