"'Ya'yansa Sun Amince," An Nada Wanda Zai Zama Khalifan Sheikh Dahiru Bauchi

"'Ya'yansa Sun Amince," An Nada Wanda Zai Zama Khalifan Sheikh Dahiru Bauchi

  • 'Ya'yan marigayi Sheikh Dahiru Usman Bauchi sun cimma matsaya kan wanda ya dace ya zama Khalifan mahaifinsu a kowane bangare
  • 'Daya daga cikin 'ya'yan marigayin ya bayyana cewa sun yi wa babban yayansu, Sayyid Ibrahim Sheikh Dahiru Bauchi mubaya'a
  • Wannan dai na zuwa ne bayan Allah ya karbi ran babban malamin kuma jigo a darikar Tijjaniyya, Sheikh Dahiru Bauchi a makon jiya

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Bauchi, Nigeria - Rahotanni sun nuna cewa 'ya'yan marigayi Sheikh Dahiru Usman Bauchi sun yarda sun zabi wanda zai zama Khalifan mahaifinsu.

Hakan dai na zuwa ne bayan babban malamin addinin musulunci kuma jigo a darikar Tijjaniyya, Sheikh Dahiru Bauchi ya rasu a ranar Alhamis da ta gabata.

Sayyid Ibrahim.
Sayyid Ibrahim tare da mahaifinsu, Sheikh Dahiru Usman Bauchi Hoto: Sayyid Ibrahim Sheikh Dahiru Bauchi
Source: Facebook

Wane ne ya zama Khalifan Dahiru Bauchi?

Jaridar TRT Hausa ta tattaro cewa 'ya'yan marigayin sun amince Sayyid Ibrahim Sheikh Dahiru Usman Bauchi ya zama Khalifan mahaifinsu kuma jagoransu.

Kara karanta wannan

Tsohon sanata daga Zamfara ya amince Amurka ta kawo farmaki Najeriya

Daya daga cikin 'ya'yan marigayi , Aminu Sheikh Dahiru Bauchi ne ya tabbatar da hakan, ya ce dukansu sun amince da babban yayansu, Sayyid Ibrahim.

Ya bayyana cewa duka 'ya'yan Dahiru Bauchi su 82 sun amince kuma sun yi mubaya'a ga babban yayansu, Sayyid Ibrahim a matsayin khalifan mahaifinsu a kowane mataki na jagoranci.

Haka zalika Aminu ya ce sun amince Sayyid Ibrahim ya zama jagora a cikin iyalan marigayi Sheikh Dahiru Bauchi.

Sarki Sanusi II ya kai ziyarar ta'aziyya

Sheikh Aminu, wanda yan daya daga fitattun 'ya'yan marigayi Dahiru Bauchi ya bayyana haka ne yayin da yake jawabin maraba lokacin da Sarkin Kano na 16, Khalifa Muhammadu Sanusi II ya kai musu ziyarar ta'aziyya.

Sarki Sanusi II, wanda bai samu halartar jana'izar Sheikh Dahiru Bauchi ba, ya ziyarci iyalansa domin yi masu ta'aziyyar wannan babban rashi a ranar Laraba da ta gabata, a Bauchi.

Basaraken ya bayyana cewa lokacin da malamin ya rasu ba ya Najeriya, kuma hakan ne ya sa bai samu damar halartar jana'izarsa ba.

Kara karanta wannan

Matakin da za a dauka idan aka kama jami'in dan sanda yana gadin babban mutum

Sanusi II ya ce Sheikh Dahiru ya bar tarihin tausayi, zaman lafiya, koyi da kyawawan halaye da koyar da Musulunci cikin hikima da natsuwa.

'Ya 'yan Sheikh Dahiru Bauchi sun yi mubaya'a

Da yake jawabin lokacin da Sarkin Kano ya je ta'aziyya, Sheikh Aminu ya bayyana cewa Sayyid Ibrahim ne zai zama Khalifan mahaifinsu, Sheikh Dahiru Bauchi a kowane mataki.

"Gaba dayan mu ('ya'yan Sheikh Dahiru Bauchi) mun goyi baya kuma mun yi mubaya'a ga babban yayanmu, Khalifa Sheikh Ibrahim Sheikh Dahiru Usman Bauchi. Babu mutum daya a cikinmu da ya ce bai yarda ba."

- In ji Aminu Dahiru Usman Bauchi.

Dahiru Bauchi da dansa, Sayyid Ibrahim.
Sheikh Dahiru Usman Bauchi tare da dansa, Sayyid Ibrahim Hoto: Sayyid Ibrahim Dahiru Bauchi
Source: Facebook

Wani dan Tijjaniyya a Katsina, Sani Ahmad ya shaida wa Legit Hausa cewa dama Sayyid Ibrahim ne ya dace ya zama Khalifan marigayin duba da cewa shi ne babban dansa a yanzu.

Sani ya yaba wa iyalan Sheikh Dahiru Bauchi bisa yadda suka hada kansu suka yi wa Sayyid Ibrahim mubaya'a ba tare da wani ya balle ba, ya yi fatan Allah Ya taimaki Khalifa.

"Sayyid Ibrahim shi ne ya cancanta da zama Khalifan Shehi, saboda dama shi ne babbansu, kuma mun yi farin cikin yadda 'ya'yan malam suka hada kansu, muna fatan Allah ya kara hada kansu," in ji shi.

Kara karanta wannan

Shaidar da malaman Musulunci a Najeriya suka yi wa marigayi Sheikh Dahiru Bauchi

Wasiyyoyi 9 daga Dahiru Bauchi

A baya, kun ji cewa Sheikh Dahiru Usman Bauchi ya bar wasiyyoyi da dama ga iyalansa da daukacin al'ummar musulmi, har da wadanda ba 'yan Tijjaniyya ba.

'Dan marigayin, Dr. Abubakar Surumbai Sheikh Ɗahiru Bauchi ya tattaro wasiyyoyi tara da malamin Musuluncin ya yi kafin ya koma ga Allah SWT.

Dr. Surumbai ya ce rashin Sheikh Dahiru Bauchi ya shafi Musulmai da Kirista, domin kowa da irin amfani da gudummuwar da ya ba shi musamman wajen hadin kasa.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262