Da Gaske an Kama Wike a Faransa? Ministan Ya Fadi Halin da Yake Ciki
- Ministan Abuja, Nyesom Wike ya ce fitowar kakakin Majalisar Rivers da ’yan majalisa PDP zuwa APC na nuna karfin rikicinta
- Tsohon gwamnan ya bayyana cewa yana nan a PDP, yana mai kira ga shugabannin jam’iyyar su gaggauta magance rikicin
- Ya kuma yi karin haske kan rade-radin kama shi a Faransa, yana mai cewa duk ƙagaggun labarai ne da ba gaskiya ba
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Abuja - Ministan Babban Birnin Tarayya, Nyesom Wike, ya yi magana game da ficewar kakakin majalisar dokokin Jihar Rivers.
Kakakin majalisar da wasu mambobi 15 sun bar PDP zuwa APC wanda ya samo asali daga tsananin rikicin da ya raba jam’iyyar gida biyu.

Source: Twitter
Nyesom Wike ya fadi matsayarsa a PDP
Nyesom Wike ya bayyana haka ne bayan duba ayyukan gyaran hanyoyi a Abuja, a yau Juma'a 5 ga watan Disambar shekarar 2025, cewar Vanguard.
Wike ya ce ’yan majalisar sun yi aiki ne bisa tanadin kundin tsarin mulki saboda halin da PDP ke ciki.
Da aka tambaye shi kan lamarin, Wike ya ce kowa na da damar zuwa inda ya ga dama, domin jam’iyyar ta rabu gida biyu, sai dai ya bayyana cewa shi kuwa bai bar PDP ba, yana nan daram.
Ya ce daga yan majalisa 27, kimanin 16 ko 17 ne suka bar jam’iyyar, sauran kusan 10 kuwa za su ci gaba da aiki tare da shi.
Ministan ya bukaci shugabancin PDP su gaggauta warware rikicin da ke ruguza jam’iyyar, yana mai cewa rashin gyara matsalar zai ci gaba da janyo asara.
A cewarsa:
“Wadanda suka tafi sun yi abin da suke ganin daidai ne, amma mu da muka zauna a jam’iyyar, za mu ci gaba da aiki tare.”

Source: Facebook
Martanin Wike kan rade-radin kama shi
Kan jita-jitar cewa an kama shi a Faransa, Wike ya yi watsi da batun, yana mai cewa duk karya ce ta siyasa.
Ya tunatar da cewa an taba yayata cewa ya yi rashin lafiya kuma an kai shi kasashen waje, sannan yanzu kuma ake cewa an kama shi.
Ya ce irin wadannan maganganu ba za su karkatar da hankalinsa daga aikinsa ba, domin shi abin da ya dame shi, shi ne ganin ya cika amanar da shugaban kasa ya dora masa.
Wike ya jaddada cewa sakamakon aikinsa da kuma gamsuwar shugaban kasa shi ne abu mafi muhimmanci gare shi.
Ya ce lokaci zai nuna wa masu suka cewa aikinsa ne zai yi tasiri, domin daga baya mutane za su daina sauraron labaran karya da ake yadawa domin batanci.
Wike ya kori sakataren ilimi a Abuja
Kun ji cewa Ministan Abuja, Nyesom Wike, ya fusata game da fitar da wata sanarwa a birnin da ya shafi rufe makarantu saboda rashin bin ka'ida.
Hakan ya jawo dakatar da sakataren ilimi, Danlami Hayyo saboda rahoton kulle makarantu ba tare da izinin ministan Abuja ba.
Hukumar FCTA a wancan lokaci ta karyata sanarwar cewa za a rufe makarantu a ranar 28 ga Nuwambar 2025, ta ce ba a taba yanke irin wannan hukunci ba.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

