Sanata Oshiomhole Ya Kai Maganar Opay da Moniepoint gaban Majalisar Dattawa

Sanata Oshiomhole Ya Kai Maganar Opay da Moniepoint gaban Majalisar Dattawa

  • Sanata Edo ta Arewa Adams Oshiomhole ya yi maganar cibiyoyin kudi irinsu Opay, Palmpay da Moniepoint a zauren Majalisar Dattawa
  • Oshiomhole ya bayyana yadda aka yi amfani da irin wadannan cibiyoyin hada-hadar kudi a lokacin da aka yi masa kutse a asusun banki
  • Ya bukaci Majalisar Dattawa ta yi dokar da za ta ba da damar sanya ido kan wadannan cibiyoyi, da kuma gano wadanda suka mallake su

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Abuja, Nigeria - Sanatan Edo ta Arewa, Adams Oshiomhole ya yi magana kan cibiyoyin hada-hadar kudi da ake amfani da su ta Intanet kamar Opay da Moniepoint a Majalisar Dattawa.

Kalaman Sanata Oshiomhole na zuwa ne a daidai lokacin da wasu ke zargin irin wadannan bankuna na intanet na sace masu kudi daga asusun ajiyarsu.

Kara karanta wannan

Sheikh Gumi Ahmad ya ce ya daina shiga daji tattaunawa da 'yan bindiga

Adams Oshiomhole.
Sanatan Edo ta Arewa, Adams Oshiomhole a zauren Majalisa Hoto: Adams Oshiomhole
Source: Facebook

Tsohon gwamnan na Edo ya yi kira ga majalisar dattawa da ta kara tsaurara kulawa kan cibiyoyin hada-hadar kudi da ke aiki ba tare da tsarin bankuna ba, cewar rahoton The Cable.

Oshiomhole ya ba da wannan shawara ne a ranar Alhamis yayin tattaunawa kan dokar cibiyoyin kudi da ake son gyarawa.

Dokar dai ita ce wacce za ta ba da damar tantancewa, rajista da kuma tsaurara sa-ido kan muhimman cibiyoyin kudi da ke da tasiri ga tsarin tattalin arzikin kasa.

Maganar da Oshiomhole ya yi kan Opay

Sanatan ya ce ya taba fuskantar kutse a asusun bankinsa, amma da ya bincika sai ya gano cewa 'yan damfarar sun yi amfani da Opay da Moniepoint wajen kokarin cutarsa.

Oshiomhole ya ce:

“Lokacin da aka yi min kutse, na gano cewa a Opay ca Moniepoit suka angiza kudaden, babu wani banki mai rijista da muka sani.
"Da na tambaya sai aka ce mini ba su da ofishi a Abuja, ba sa daukar ma’aikata, ba su da wani takamaiman wuri da suke hulda da jama'a."

Kara karanta wannan

'Ina cikin aminci a Najeriya': Tsohon Firayim ministan Birtaniya kan tsaro

Sanata Oshiomhole ya bada shawara

Sanata Oshiomhole ya ce irin wadannan cibiyoyi na kudi suna taka muhimmiyar rawa amma babu isasshen kulawa a kansu ko sanin wadanda suka mallake su.

Ya ce ya kamata majalisa ta tabbatar cewa an rufe duk wata kafa da za a iya amfani da ita wajen aikata laifuka, musamman ganin cewa jama’a da yawa suna amfani da Opay da sauran makamantansu.

Oshiomhole.
Tambarin kamfanin hada-hadar kudi na Opay da Sanata Adams Oshiomhole Hoto: Opay Nigeria, Adams Oshiomhole
Source: Facebook

A cewarsa, dokar majalisa tana da karfi fiye da ka’idojin da CBN ke fitarwa, don haka ya bukaci a goyi bayan kudurin tare da yin cikakken bincike kan masu mallakar irin wadannan cibiyoyin kudi.

A karshe, kudurin dokar, wanda sanata Tokunbo Abiru na Lagos ta Gabas ya dauki nauyinsa, ya tsallake karatu na biyu, kamar yadda Daily Post ta kawo.

Oshiomhole ya nemi a yi karin albashi

A wani rahoton, kun ji cewa tsohon gwamnan jihar Edo kuma Sanata a APC, Adams Oshiomhole ya koka kan yadda ma'aikatan Najeriya ke kara talaucewa.

Kara karanta wannan

Tinubu ya tura sako na musamman ga Majalisa bayan tabbatar da nadin ministan tsaro

Sanata Oshiomhole ya bukaci gwamnati ta karawa ma'aikata albashin da ya haura N70,000, ya bukaci duk jihar da za ta iya ta karawa ma'aikata kudi.

Ya bayyana cewa akwai lokacin da ya taba tilasata Bola Tinubu ya karawa ma'aikata kudi a kan mafi karancin albashi a lokacin da yake gwamnan Legas.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262