Gwamnatin Gombe Ta Samu Ƙarin N2.8bn a Asusunta bayan Korar 'Ma'aikatan Bogi'

Gwamnatin Gombe Ta Samu Ƙarin N2.8bn a Asusunta bayan Korar 'Ma'aikatan Bogi'

  • Gwamnan Gombe, Muhammad Inuwa Yahaya, ya ce gwamnati ta yi nasarar rairaye wasu ma'aikata da aka tabbatar na bogi ne a jihar
  • Ya bayyana cewa wannan aiki da gwamnati ta yi ya bayar da daman alkilta sama da N2bn da ake asara ta hanyar ma'aikatan
  • Ya kara da cewa an yi wannan kora ne a fannin lafiya, kuma an gina da gyara cibiyoyin lafiya na farko 114 a ƙananan hukumomi da dama a Gombe

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa. Jihar Gombe – Gwamnan jihar Gombe, Muhammad Inuwa Yahaya, ya bayyana cewa gwamnatin sa ta samu N2.8bn ta hanyar cire ma’aikatan bogi 500 daga tsarin lafiya a jihar.

Gwamna Inuwa Yahaya ya ce hakan ya bayar da dama wajen amfani da kuɗin a inda ya dace tare da inganta harkar lafiya a Gombe.

Kara karanta wannan

Gwamnatin Abba ta shaidawa Tinubu lamarin rashin tsaro a jihar Kano

Gwamnatin Gombe ta gano ma'aikatan bogi
Gwamnan Jihar Gombe, Inuwa Yahaya Hoto: Ismaila Uba Misilli
Source: Facebook

The Cable ta wallafa cewa Gwamnan ya ce an gina ko gyara cibiyoyin lafiya a matakin farko guda 114 a duk fadin jihar.

Ana inganta harkar lafiya a Gombe

Gwamnan ya ce a yanzu haka, kowace karamar hukuma na da nata asibiti a matakn farko, sannan an samar da inshorar lafiya ga sama da mutane 300,000.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Gwamna Inuwa Yahaya ya fadi hakan ne yayin da yake ba da faɗin nasarorin gyaran kananan asibitocin da sauran ayyuka a bangaren lafiya a jihar.

Gwamna Inuwa Yahaya ya ce:

“A shekarar 2019, lokacin da na zama gwamna, jihar na fama da gibin kasafin kudi. Tsarukan gwamnati sun rushe, asibitoci na ta rushewa, makarantu sun lalace, kuma kudi kadan ne ake da shi don aiki a lokacin."
"Tsarin lafiyar mu na samun 3.5% kacal daga kasafin jihar. Ma’aikata kaɗan ne kuma sau da yawa ba su nan."

Gwamnan Gombe ta ce an samu canji

Kara karanta wannan

Jirgin fadar Shugaban kasa ya yi kwantai bayan dogon lokaci a kasuwa

Inuwa Yahaya ya bayyana cewa daya daga cikin kalubale mafi girma shi ne gabatar da tsarin bin diddigin ma’aikata ta amfani da tsarin zamani na 'biometric.'

Gwamnati ta ce an kori ma'aikatan bogi a Gombe
Muhammad Inuwa Yahaya, Gwamnan Gombe Hoto: Ismaila Uba Misilli
Source: Facebook

Ya ce:

“A takarda, asibitocin mu suna da ma’aikata. Amma a aikace, na shiga wasu asibitocin sha-ka-tafi, na ga ma’aikata kaɗan na kula da marasa lafiya da yawa fiye da yadda ya kamata."
"Mun gano ma’aikatan bogi 500, kuma ta wannan hanyar muka ceto N2.8bn, sannan muka sake amfani da kudin wajen horo, daukar ma’aikata, da fadada ayyuka.”

Gwamnan ya kara da cewa yanzu suna amfani da fasaha wajen inganta tsarin lafiya, kula da ayyuka da ma’aikata, da kuma tsara amfani da kudin waje ta yadda ya dace.

Gwamnatin jihar Gombe ta yi kora

A baya, mun wallafa cewa Gwamnan jihar Gombe, Muhammadu Inuwa Yahaya, CON, ya amince da sallamar shugaban hukumar ilimin bai daya ta jihar Babaji Babadidi.

Sanarwar ta fito ne daga babban daraktan yada labaran gwamnan, Ismaila Uba Misilli, ya ce an ɗauki matakin ne bisa sahalewar dokar hukumar SUBEB ta jihar Gombe.

Kara karanta wannan

Kano: Gwamnati ta yi bayani kan dokar hana acaba, an yi sassauci a wasu yankuna

Gwamnan ya kuma amince da naɗin Farfesa Esrom Toro Jonathan wanda ya shahara wajen bincike da gudanarwa a fannin ilimi a matsayin sabon shugaban SUBEB.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano. aisha.ahmad@corp.legit.ng