'Ba Rasuwa Sheikh Dahiru Bauchi Ya Yi ba,' Dan Shi Ya Fadi Me Ya Faru
- Nazir Dahiru Bauchi ya ce mahaifinsu, Sheikh Dahiru Bauchi, ya bai rasu ba komawa ya yi daga wannan rayuwa zuwa wata
- 'Dan malamin ya ce Sheikh Dahiru Bauchi na da karamomi da dama, ciki har da haddatar yara cikin kankanin lokaci
- Baya ga haka, Nazir ya fadi wasu abubuwa game da mahaifinsu, ciki har da fadin cewa malamin yana raba aljanna ga jama'a
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Jihar Bauchi – Daya daga cikin ’ya’yan fitaccen malamin Tijjaniyya, Sheikh Dahiru Usman Bauchi, wato Nazir Dahiru Bauchi, ya bayyana cewa ba za a ce mahaifinsu ya rasu ba.
Ya bayyana cewa lla dai ruhinsa ne ya koma ga Ubangiji yayin da jikinsa zai koma cikin ƙasa, kamar yadda Allah SWT ya halicci dan Adam daga ƙasa.

Source: Facebook
Nazir ya bayyana hakan ne yayin da yake bayani kan yadda ake fahimtar batun rayuwa ta duniya da wadda ke biyowa bayan mutuwa a wani bidiyo da ya wallafa a Facebook.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ya ce akwai wadanda suke rayuwa ba tare da mutane suna ganinsu ba, kamar aljanu, haka ma ana iya ganin waliyyai gwargwadon ƙarfin imani.
Nazir ya ce Dahiru Bauchi bai rasu ba
Nazir Dahiru Bauchi ya yi karin bayani cewa ruhin mahaifinsu ya koma zuwa ga Ubangiji, kuma idan Allah ya so, zai iya dawo da mutum jikinsa a zahiri, a gan shi a yi magana da shi ba ta mafarki ba, gwargwadon ƙarfin imanin mutum.
Ya ce wannan lamari na daga cikin ikon Allah wanda ba ya yiwuwa sai ga wadanda Allah ya kara musu fahimta da ƙarfin zuciya.
'Dan malamin ya kara da cewa akwai mutane da dama da ke ganin malamai ko waliyyai a zahiri ko a mafarki, gwargwadon matsayin su na imani.

Kara karanta wannan
'Suna da manyan makamai,' Sheikh Gumi ya ce ana taimakon 'yan ta'adda daga ketare
Aminiya ta wallafa a Facebook cewa ya ce mahaifinsu, Sheikh Dahiru Usman Bauchi ba rasuwa ya yi ba, ya kaura ne, ya koma wata rayuwa kawai.
Karamomin Sheikh Dahiru Usman Bauchi
Nazir ya bayyana cewa Sheikh Dahiru Usman Bauchi na da karamomi masu yawa tun kafin rasuwarsa. Daga cikin su, ya ce akwai iya haddatar da yara Kur'ani a cikin kankanin lokaci.
Ya kara da cewa Sheikh Ibrahim Inyass ne ya ba wa Sheikh Dahiru wannan karama ta karatun Al-Kur'ani mai girma.
Game da yanayin rayuwa kuma, ya ce rayuwar mahaifinsu ta kasance cike da tsoron Allah da yin ayyukan alheri.
Duk da cewa a ƙarshen rayuwarsa ya rage magana sosai, Nazir ya ce mahaifinsu kullum yana cikin zikiri da karatun Alƙur’ani.
Shehi na raba Aljanna inji Nazir Dahiru Bauchi
Nazir Dahiru Bauchi ya ce ba a magana a kan mutuwar irinsu Sheikh Dahiru Bauchi, domin a cewarsa su mutane ne da Allah ya ba su matsayi na musamman cikin al’umma.
Ya ce suna koyar da yadda za a tsira, suna kuma raba aljanna irin yadda Annabi Muhammad (SAW) ke raba aljanna ga mabiyansa.

Source: Facebook
A cewar Nazir Dahiru Bauchi, waliyyan Allah suna raba aljanna ne ta hanyar koya wa mutane addinin da Annabawa suka koyar.
Yadda Dahiru Bauchi ya yi wa Sanusi II addu'a
A wani labarin, mun rahoto muku cewa Khalifa Muhammadu Sanusi II ya ziyarci gidan Sheikh Dahiru Usman Bauchi domin ta'aziyya.
Mai martaba Sanusi II ya ce daga cikin dalilan da suka sanya ya dawo sarauta bayan sauke shi akwai addu'ar malamin.
Ya kara da cewa zai cigaba da kulla alaka da iyalan marigayin kamar yadda ya yi da iyaye da kakaninsa a shekarun baya.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

