Malaman Majami'u Sun Taru a Abuja, Sun Fito da Gaskiya kan Zargin Kisan Kiristoci a Najeriya
- Tawagar wasu malaman majami'u sun kira taron manema labarai na musamman a Abuja yau Juma'a, 5 ga watan Disamba, 2025
- Hakan na zuwa ne gabanin taron tsaro na yankin Arewa maso Yamma, wanda za a gudanar a ranakun 17 da 18 ga watan Disamba
- Malaman sun yi magana kan abubuwa da dama ciki har da zargin yiwa kiritoci kisan kare dangi da nadin sabon ministan tsaro
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Abuja, Nigeria - Malaman majami'un kiristoci a Najeriya sun kira taro na musamman a Abuja kan zargin kisan 'yan uwansu da Amurka ke yi wa kasar nan.
Idan ba ku manta ba Shugaban Amurka, Donald Trump ya sanya Najeriya a jerin kasashen da ake tauye hakkin addini saboda zargin ana yi wa kiristoci kisan kare dangi.

Source: Twitter
Shin ana kashe kiristoci a Najeriya?
Daily Trust ta ruwaito cewa wasu jagororin majami'u na kirista sun karyata wannan zargi a taron manema labarai da suka gudanar yau Juma'a a Abuja.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Sun yi watsi da ikirarin cewa gwamnati na daukar nauyin kisan kiyashi ga Kiristoci a Najeriya.
Da yake magana da manema labarai kafin taron tsaro na Arewa maso Yamma da za a yi ranakun 17 zuwa 18 ga Disamba, 2024, shugaban tawagar, Bishof Timothy Cheren, ya ce babu wata hujja da ke nuna cewa gwamnati na da hannu a kisan Kiristoci.
“Babu wani kisan kiyashi da ake wa Kiristoci da gwamnati ke daukar nauyi. Amma muna ganin akwai wasu miyagu da ke tayar da tarzoma,” in ji shi.
Sun yaba wa Shugaba Tinubu
Bishof Cheren ya yaba wa kokarin Shugaba Bola Ahmed Tinubu wajen yaki da ta’addanci da ’yan bindiga, yana mai cewa ya zama wajibi ’yan Najeriya su mara wa gwamnati baya.

Kara karanta wannan
Hadimin Tinubu ya yi martani mai zafi kan kiran Amurka ta hana dokar shari'a a Najeriya
Ya ce Najeriya na fama da rikice-rikicen tsaro masu sarkakiya, amma hadin kan gwamnati da ’yan kasa ne kadai zai kawo karshen matsalolin.
Tawagar bishof-bishof din sun gargadi malaman addini da su guji kalaman tunzura jama'a ko koyarwa da ka iya tayar da rikici, in ji rahoton Vanguard.
“Zaman lafiya ba yana nufin babu adalci ba ne. Dole gwamnati ta hukunta duk wanda ya yi kiran hana zaman lafiya,” in ji Cheren.

Source: Twitter
Malaman majami'u sun yaba da nadin Musa
Sun kuma yi maraba da nadin Janar C.G. Musa a matsayin Ministan Tsaro, suna cewa hakan babban ci gaba ne wajen karfafa tsarin tsaro na kasa.
Haka kuma sun bukaci gwamnatin tarayya ta yi amfani da gargadin da Amurka ta yi kwanan nan a matsayin wata dama ta kara hadin kai wajen yaki da ta’addanci.
Sanata Marafa ya goyi bayan Trump
A wani rahoton, kun ji cewa tsohon sanatan Zamfara ta Tsakiya, Sanata Kabiru Marafa ya bayyana ra'ayinsa kan barazanar shugaban Amurka, Donald Trump ta kawo farmaki Najeriya.
Sanata Marafa ya bayyana cewa yana goyon bayan barazanar da Trump ya yi ta kawo dauki Najeriya domin yakar 'yan ta'adda.
A cewar Marafa, barazanar Shugaba Trump ta matsa wa gwamnatin Najeriya lamba wajen daukar matakan gaggawa kan matsalar tsaro da ke addabar kasar.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Asali: Legit.ng

