Rikici a Raɗin Suna Ya Yi Ajalin Matashi a Wani Bauchi

Rikici a Raɗin Suna Ya Yi Ajalin Matashi a Wani Bauchi

  • Wani matashi mai shekaru 20, Haruna Haruna, ya rasu bayan rikici ya ɓarke a wajen bikin suna a Jihar Bauchi
  • Rikicin ya samo asali ne daga sabani da ya shiga tsakanin wasu matasa da suka halarci taron raɗin sunan
  • Da farko matashin ya suma bayan rikici ya yi zafi, kafin a garzaya da shi zuwa wurin kwararru inda aka ce ya rasu

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Bauchi – Wani matashi ɗan shekara 20 mai suna Haruna Haruna ya mutu bayan wata arangama ta ɓarke a lokacin bikin radin suna a jihar Bauchi.

Rahotanni sun bayyana cewa wannan mummunan lamari ya faru n a ƙauyen Kwata da ke ƙarƙashin Karamar Hukumar Warji a Jihar Bauchi.

Kara karanta wannan

'Suna da manyan makamai,' Sheikh Gumi ya ce ana taimakon 'yan ta'adda daga ketare

Matashi ya rasu bayan hatsaniya a Bauchi
Sufeton yan sandan Najeriya, Kayode Egbetokun Hoto: Nigeria Police Force
Source: Facebook

Jaridar Punch ta wallafa cewa lamarin ya faru ne a ranar Talata, lokacin da aka fara samun ƴan takaddama tsakanin wasu matasa da ke wajen taron.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Rikici ya ɓarke tsakanin matasa a Bauchi

Jaridar Aminiya ta wallafa cewa sabanin da ya fara da gardama ya rikide zuwa rikici, lamarin da ya sanya Haruna faɗuwa ƙasa ba kuma bai farfaɗo ba.

Wasu majiyoyi da suka tabbatar da faruwar lamarin sun bayyana cewa rikicin ya yi muni sosai, ya kuma zo da ƙarar kwana.

A cewarsa:

“Wani matashi ɗan shekara 20, Haruna Haruna na ƙauyen Kwata a Karamar Hukumar Warji ta Jihar Bauchi, ya rasu bayan rikicin tashin hankali da ya ɓarke a wajen bikin suna ranar 2 ga Disamba, 2025.”

Majiyar ta ce rikicin ya fara ne daga ƙaramin sabani da ba a yi tsammanin zai kai ga tashin hankali ba, amma ya a girmama.

Kara karanta wannan

Karancin abinci: Manoma 14,000 sun samu tallafin N4bn a jihar Bauchi

An yi kokarin ceto matashi a Bauchi

Majiyar ta ƙara da cewa lamarin ya ƙara muni kafin ka ce kwabo, kuma ana cikin hatsaniya sai Haruna ya fadi har ƙasa.

Yan sanda ba su bayar da bayani kan rikici a Bauchi ba
Taswirar jihar Bauchi, inda matashi ya rasu a taron suna Hoto: Legit.ng
Source: Original

Bayan rikicin ya lafa, aka garzaya da Haruna zuwa Asibitin Warji domin a ceto rayuwarsa. Sai dai duk da ƙoƙarin da likitoci suka yi, matashin ya rasu.

An tuntubi kakakin rundunar ‘yan sandan Jihar Bauchi, DSP Ahmed Wakili, domin ya yi karin bayani kan lamarin.

Ya bayyana cewa yana cikin wani taro, kuma zai bayar da cikakken bayani daga bisani amma har yanzu bai ce komai ba a kan rikicin ko rasa rai ba.

Rikici ya ɓarke a jihar Bauchi

A baya, mun ruwaito akalla mutum ɗaya ya rasa ransa bayan rikici ya ɓarke tsakanin manoma da makiyaya a ƙauyen Bursali da ke cikin Karamar Hukumar Zaki a Jihar Bauchi.

Rahotanni sun nuna cewa an kama mutane shida da ake zargin suna da hannu a cikin lamarin da ya bar jama'a a cikin zaman dar-dar da rashin tabbas a watan Nuwambar da ta wuce.

Kara karanta wannan

Bello Matawalle ya samu kariya ana tsaka da kiran Tinubu ya kore shi

Masani sun tabbatar da cewa wasu makiyaya Fulani masu yawo daga Jihar Jigawa ne suka shigo cikin gonakin mutanen yankin, lamarin da ya tada hankalin jama’a da hayaniya.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano. aisha.ahmad@corp.legit.ng