'Suna da Manyan Makamai,' Sheikh Gumi Ya Ce ana Taimakon 'Yan ta'adda daga Ketare

'Suna da Manyan Makamai,' Sheikh Gumi Ya Ce ana Taimakon 'Yan ta'adda daga Ketare

  • Sheikh Ahmad Abubakar Gumi ya ce alamu na nuna cewa wasu ƙasashe masu ƙarfi na taimaka wa ’yan bindiga ta bayan fage
  • Ya yi nuni da cewa matsalar da ta ragu a Abuja–Kaduna da Birnin Gwari ta sake ɓullo wasu wurare, abin da ke nuna akwai lauje cikin nadi
  • Malamin ya ce kabilanci ya shiga matsalar tsaro, abin ya ce yana bukatar kulawa ta musamman daga gwamnatin tarayyar Najeriya

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Najeriya – Fitaccen malamin addinin Musulunci, Sheikh Ahmad Abubakar Gumi, ya sake tayar da muhawara kan rashin tsaro, inda ya yi zargin cewa wasu ƙasashen waje masu ƙarfi na da hannu a ta’addanci a Najeriya.

Gumi ya ce kafin wannan sabon tashin hankalin, alamu sun nuna cewa tsaro na inganta musamman a babban titin Abuja zuwa Kaduna.

Kara karanta wannan

Sheikh Gumi Ahmad ya ce ya daina shiga daji tattaunawa da 'yan bindiga

Sheikh Ahmad Abubakar Mahmud Gumi
Sheikh Gumi yana bayani yayin wani taro. Hoto: Salisu Webmaster
Source: Facebook

A wata tattaunawa da ya yi da BBC Hausa, malamin ya ce irin yadda hare-hare suka sake ƙaruwa ya nuna akwai wani abu a kasa.

Ta'addanci: Zargin Gumi ga kasashe waje

Da aka tambaye shi ko wace ƙasa ce ke taimaka wa ’yan bindiga, Sheikh Gumi bai ambaci wata ƙasa guda ba, sai dai ya ce alamu sun nuna akwai wasu ƙasashen da ke da hannu a rashin tsaron Najeriya.

A cewarsa, kayan aiki irin su manyan makamai da motocin da ake samu a hannun ’yan bindiga sun fi ƙarfin abin da za a iya shigowa da shi ba tare da taimakon ƙasashen waje ba.

Vanguard ta rahoto ya ce abin da ya fi tayar masa da hankali shi ne yadda ake samun manyan makamai da ’yan bindiga ke amfani da su, amma sojojin Najeriya ba su da makamantansu.

Wasu 'yan ta'adda a Najeriya
Wasu 'yan ta'adda dauke da manyan makamai. Hoto: Zagazola Makama
Source: UGC

Gumi ya yi kira ga gwamnatin Najeriya da ta ƙara zurfafa bincike, inganta leken asiri, da kuma sa ido kan duk wata alaƙa daga ƙasashen waje da za ta iya kawo cikas ga tsaro.

Kara karanta wannan

Sheikh Gumi ya yi zazzafar addu'a kan 'yan ta'adda da masu taimakonsu

Zargin kabilanci a rikicin tsaron Najeriya

Sheikh Ahmad Abubakar Gumi ya yi tsokaci kan yadda kabilanci ke ƙara ɓarna cikin rikicin tsaron da ya addabi Najeriya.

Ya ce ɓangarori daban-daban na zargin juna, Fulani na cewa wasu kabilu na kashe su, sauran kabilu kuma na cewa ana son kashe su.

Malamin ya ce ƙoƙarinsa shi ne ya fahimtar da ɓangarorin cewa ta’addanci ba shi da kabila, amma wasu na kallon irin wannan ƙoƙari a matsayin goyon bayan ’yan bindiga, lamarin da ya ce ba gaskiya ba ne.

Sheikh Gumi ya ce rikicin rashin tsaro na shafar kowa ba tare da bambancin addini ba, amma abin takaici shi ne yadda Amurka da wasu hukumomi ke mai da batun kisan Kiristoci wata hanya ta siyasantar da rikicin.

Gumi ya daina zuwa wajen 'yan bindiga

A wani labarin, kun ji cewa malamin addinin Musulunci, Sheikh Ahmad Abubakar Mahmud Gumi ya ce ya daina zuwa wajen 'yan bindiga.

Kara karanta wannan

Bello Matawalle ya samu kariya ana tsaka da kiran Tinubu ya kore shi

Malamin ya bayyana haka ne yayin da aka tambaye shi ko yaushe rabonsa da zuwa wajen 'yan bindiga a dazukan Najeriya.

A cewar Sheikh Gumi, tun a lokacin da gwamnatin Buhari ta ayyana su a matsayin 'yan ta'adda ya daina zuwa wa'azi wajen su.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng