Sheikh Ahmad Gumi Ya Ce Ya Daina Shiga Daji Tattaunawa da 'Yan Bindiga
- Sheikh Ahmad Abubakar Gumi ya yi karin bayani game da tsanani da dawowar hare-hare a wasu yankunan Najeriya a kwanan nan
- Malamin ya ce a wasu wurare kamar hanyar Abuja–Kaduna da Birnin Gwari an samu kwanciyar hankali kafin matsalar ta sake ƙara kamari
- Ya bayyana dalilan da suka sanya shi daina shiga daji ya koyar da 'yan bindiga ko tattauna wa da su tun lokacin Muhammadu Buhari
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
FCT, Abuja – Fitaccen malamin addinin Musulunci, Sheikh Ahmad Abubakar Mahmud Gumi, ya bayyana damuwarsa game da halin da tsaron Najeriya ya sake shiga a kwanakin nan.
Sheikh Gumi ya ce duk da cewa an samu kwanciyar hankali na wani lokaci, musamman a hanyar Abuja zuwa Kaduna da yankin Birnin Gwari, abubuwa sun sake dagulewa a wasu yankuna.

Source: Facebook
Malamin ya yi wannan bayani ne a wata hira da BBC Hausa, inda ya yi nazari kan jerin hare-hare da suka sake tashi a sassa daban-daban na ƙasar.
A cewar malamin, akwai buƙatar gwamnati ta kara bincike tare da fahimtar ainihin tushen rikicin domin samar da mafita ga kasa baki daya.
Wuraren da tsaro ya samu a Najeriya
Sheikh Gumi ya yi nuni da cewa kafin yanzu an samun raguwar hare-hare sosai, inda ya kawo misalin hanyar Abuja–Kaduna wadda a da ta kasance tamkar tarko ga matafiya.
Ya ce a yau, kusan abin ya zama tarihi, domin an samu sassauci mai yawa kafin lamarin ya sake kamari a kwanan nan.
Haka kuma ya ce a yankin Birnin Gwari, an ga manoma suna komawa gonaki cikin kwanciyar hankali, wanda ya bambanta da shekarun baya da ba za a iya kusantar yankin ba saboda tsananin barazanar 'yan bindiga.
Malamin ya yi ikirarin cewa akwai yiwuwar rikicin ya wuce abin da ake gani a fili, yana mai cewa “akwai dalilin” da yake sa haddasa mutanen da suka zauna lafiya tare tsawon lokaci su rikide su zama barazana ga al’umma
Sheikh Gumi ya daina ganawa da 'yan bindiga
Sheikh Gumi ya bayyana cewa ya daina shiga dajin da 'yan bindiga ke buya tun lokacin da gwamnatin Najeriya ta ayyana su a matsayin ‘yan ta’adda.
Ya ce daga lokacin da aka dauki wannan matsaya, ya zama tilas ya ja da baya domin kada ya yi hulɗa a yanayi da zai fassara shi da tallafa wa ta’addanci.

Source: Facebook
Malamin ya bayyana cewa tun daga lokacin gwamnatin Muhammadu Buhari ya daina shiga daji, kuma tun daga wannan lokacin bai sake komawa ba.
Ya kara da cewa tun a lokacin yana shiga daji tare da 'yan jarida na Arewa da Kudancin Najeriya su dauki abin da ake tattaunawa.
Sheikh Gumi ya yi addu'a kan tsaro
A wani labarin, kun ji cewa malamin Musulunci, Sheikh Ahmad Abubakar Mahmud Gumi ya yi mummunar addu'a a kan tsaro.
Malamin ya roki Allah ya tona asirin duk masu hannu a ta'addanci da ake fama da shi a Najeriya tsawon shekaru.
Bayan maganar da Sheikh Ahmad Gumi ya yi, 'yan Najeriya sun yi martani wasu na goyon bayansa, wasu na sukar shi.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng


