NAHCON Ta Fitar Sababbin Ka'idoji game da Hajjin Shekarar 2026

NAHCON Ta Fitar Sababbin Ka'idoji game da Hajjin Shekarar 2026

  • Hukumar NAHCON ta umarci kamfanonin jirage da su fara bai wa mahajjata tikitin tafiya tun kafin lokacin tashin su domin rage matsaloli
  • Sababbin dokokin da hukumar aikin Hajji ta kasa ta samar sun tanadi hukunci mai tsanani ga duk mahajjacin da ya rasa jirginsa wajen tafiya
  • NAHCON ta bukaci bin sharuddan kiwon lafiya na Saudiyya, ciki har da cututtuka tara da za su iya hana mahajjaci tafiya zuwa aikin Hajji

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT, Abuja – Hukumar alhazai ta kasa, NAHCON, ta sanar da jerin sababbin ka’idoji da matakai da za su jagoranci aikin Hajjin 2026, musamman kan tikitin jirage, tsare-tsaren tafiya da kuma sharuddan kiwon lafiya.

An bayyana sabon tsari ne a cikin wata sanarwa da aka fitar ranar 4, Disamba, 2025, bayan wani taro da aka gudanar da shugabannin alhazai na jihohi da manyan kamfanonin jiragen sama.

Kara karanta wannan

Sheikh Gumi Ahmad ya ce ya daina shiga daji tattaunawa da 'yan bindiga

Shugaban hukumar NAHCON na kasa
Shugaban hukumar NAHCON, Farfesa Abdullahi Usman. Hoto: Jibwis Nigeria|Getty Image
Source: Facebook

Sanarwar da hukumar ta fitar a X, wacce Fatima Sanda Usara ta rattaba wa hannu ta ce NAHCON ta umurci dukkan kamfanonin da za su dauki mahajjata a 2026 da su fara fitar da tikiti maniyyatan.

Sababbin ka'idoji kan tikiti da tafiya Hajji

Hukumar ta bayyana cewa daga Hajjin 2026, duk mahajjacin da ya rasa jirginsa zai fuskanci hukunci mai tsanani, domin tikitin tafiya zai kasance a hade da katin Nusuk na mahajjacin wanda aka tanada a cikin motarsa tun kafin zuwansa Saudiyya.

Saboda haka, jinkiri ko rashin halarta na nufin “mutum bai hallara filin jirgi ba” tare da daura masa nauyin biyan kudin kujerar da ba a yi amfani da ita ba.

NAHCON ta ce bayan fitowar biza, babu wani mahajjaci da zai sake canza rukuni. Rukunin zai kasance na mutum 45, kuma za su tafi tare, su zauna tare a otel ɗaya a Makka, Madina da Masha’ir, sannan su dawo tare zuwa Najeriya bayan kammala ibada.

Kara karanta wannan

Karancin abinci: Manoma 14,000 sun samu tallafin N4bn a jihar Bauchi

Sababbin ka'idoji kan tashi zuwa Saudi

A cikin sanarwar, NAHCON ta ce ma’aikatar Hajji da Umrah ta Saudiyya ta samar da sabon kati da dole ne kowane mahajjaci ya samu kafin tashi.

Takardar za ta ƙunshi cikakken bayani kan jirgi, jiharsa, lokacin tashin jirgi, adadin mahajjata da cikakken jadawalin sauka a can.

Hukumar ta umurci jihohi da su gaggauta turawa NAHCON kudin kujerun da aka tara domin guje wa rasa karin kujeru na Hajjin 2026.

Mahajjata na bakin aiki a Saudiyya
Yadda wasu masu ibada ke gabatar da aikin Hajji. Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

Batun lafiya da cututtuka yayin zuwa Hajji

NAHCON ta jaddada cewa dole ne jihohi su yi aiki tare da asibitocin da aka tantance domin fitar da takardar lafiyar mahajjata gwargwadon sababbin ka’idojin Saudiyya.

Punch ta rahoto cewa hukumar ta ce Saudiyya ta ce duk mahajjacin da ke fama da daya daga cikin manyan cututtuka tara ba zai je kasar ba, sannan zai biya duk kudin da aka kashe idan aka dawo da shi.

Cututtukan sun hada da gazawar manyan sassan jiki – zuciya, hanta, koda da huhu; masu fama da ciwon daji da ke karbar magungunan; matsalolin kwakwalwa da na jijiyoyi da ke rage fahimta; tsufa mai tare ciwon mantuwa da kuma ciki.

Kara karanta wannan

An fara sabon takun saka tsakanin gwamna Fubara da yaran Wike a majalisar Rivers

Hukumar NAHCON ta ce kamfanonin jirage da aka amince da su sun hada da Air Peace, Fly Nas, Max Air da Umza Air.

Masu Umra 45 sun rasu a birnin Madina

A wani rahoton, mun kawo muku labari cewa kasar Saudiyya ta sanar da rasuwar wasu mutane da suka tafi Umara daga Indiya.

Gwamnatin Saudiyya ta bayyana cewa mutanen sun gamu da hadarin tankar mai ne a kusa da garin Madina.

Shugabannin kasar Indiya sun yi magana game da hadarin, inda suka ce suna magana da hukumomin Saudiyya kan lamarin.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng