Najeriya Ta Yi Babban Rashi, Tsohon Sanata a Arewa Ya Riga Mu Gidan Gaskiya

Najeriya Ta Yi Babban Rashi, Tsohon Sanata a Arewa Ya Riga Mu Gidan Gaskiya

  • An sanar da mutuwar tsohon Sanata a Najeriya wanda ya bayar da gudunmawa sosai ga al'ummarsa
  • Marigayi Sanata Isa Abonyi Obaro, da ya wakilci Okehi/Okene a tsohuwar jihar Kwara, ya rasu bayan jinya
  • Sanata Natasha da ta fito yanki daya da marigayin ta bayyana jimami game da rasuwar dattijon a Kogi

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Lokoja, Kogi - Najeriya ta yi babban rashin bayan sanar da rasuwar tsohon sanata da ya rike mukaman gwamnatin da dama a kasar.

Marigayi Sanata Isa Abonyi Obaro ya wakilci mazabar Okehi/Okene a tsohuwar Jihar Kwara a Jamhuriyya ta biyu.

Tsohon Sanata a Najeriya ya rasu
Sanata Natasha Akpoti da marigayi, Isa Abonyi Obaro. Hoto: Natasha H Akpoti.
Source: Facebook

Hakan an cikin wani rubutun mika sakon ta'aziyya da Sanata Natasha Akpoti ta yi a shafin Facebook.

Gudunmawar da marigayin ya ba al'ummarsa

Sanata Obaro ya yi wa jam’iyyar NPN hidima a matsayin dan majalisa mai wakiltar tsohuwar Kwara ta Kudu da yanzu ita ce Kogi ta Tsakiya.

Kara karanta wannan

Sarki Sanusi II ya fadi dalilin rashin zuwa jana'izar Sheikh Dahiru Bauchi

An san marigayin a matsayin gogaggen lauya, mai hada kan jama’a da kuma wakilin gaskiya ga al’ummar Ebira.

Kafin ya fara harkar siyasa, Obaro ya yi aiki a Ma’aikatar Tarayya daga 1958 zuwa 1960.

Sannan ya ba da gudunmawa a aikinsa na lauya a kamfanoni masu zaman kansu daga 1963 zuwa 1968, da kuma daga 1975 zuwa 1979.

Wasu mukamai da marigayin ya rike a Najeriya

Haka kuma, ya rike manyan mukamai a majalisar zartarwa ta jihar Kwara daga 1968 zuwa 1975, inda ya nuna jajircewa da kishin kasa wajen gudanar da ayyukan gwamnati da raya al’umma.

A lokacin da yake daga 1979 Majalisar Dattawa, Obaro ya kasance a Kwamitin Kasuwanci da Masana’antu.

Majiyoyin sun ce marigayin ya bayar da gudummawa a kan dokoki da manufofin da suka shafi ci gaban mazabarsa da walwalar al’ummar yankin.

An yi rashin tsohon Sanata a Kogi
Marigayi tsohon sanata a Najeriya, Isa Obaro Abonyi. Hoto: Natasha H Akpoti.
Source: Facebook

Sakon ta'aziyyar Sanata Natasha daga Kogi

Sanata Natasha da ke wakiltar Kogi ta Tsakiya ta yi jimamin rasuwar tsohon ministan wanda ya ba da gudunmawa ga al'umma.

Natasha ta tura sakon ta'aziyya ga al'ummar Kogi ta Tsakiya bisa rasuwar sanatan wanda ya wakilci mazabar Okene/Okehi a tsohuwar jihar Kwara.

Kara karanta wannan

Ba wasa: Matakin da Gwamna Abba zai dauka don dakile hare haren 'yan bindiga a Kano

A cikin rubutunta, Natasha ta ce:

“Rasuwar Sanata Isa Abonyi Obaro.
"Ina tare da jama’ar mazabar Kogi ta Tsakiya wajen yin jimamin rasuwar Sanata Obaro, wanda ya wakilci mazabar Okehi/Okene a tsohuwar Jihar Kwara a Jamhuriyya ta biyu.
"Allah ya jikansa ya yi masa rahama.”

Mutane da dama sun yi tsokaci kan ta'aziyyar Natasha inda suka taya ta jimami da kuma yi masa addu'o'i na musamman.

Shekaru 40 bayan Abonyi Obaro ya wakilici yankin ne Sanata Natasha Akpoti ta bi sahunsa, amma bayan an raba jihohi.

Tsohon sanatan Adamawa ya rasu

A baya, an ji cewa Najeriya ta yi babban rashi na tsohon gwamna kuma Sanata da ya yi mulkin soja a jihar Plateau.

Tsohon gwamnan soja na Plateau kuma Sanata da ya wakilci Adamawa ta Arewa, Kanal Muhammad Mana, ya rasu a Abuja.

Ɗan uwansa, Sarkin Fulani na Mubi, Abdurrahman B. Kwaccham, ya tabbatar da rasuwar, ya bayyana cewa marigayin ya bar mata da ’ya’ya.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.