Gwamnatin Najeriya Ta Yi Bayani game da 'Rabon' Motocin Yi wa Tinubu Kamfen

Gwamnatin Najeriya Ta Yi Bayani game da 'Rabon' Motocin Yi wa Tinubu Kamfen

  • Fadar shugaban kasa ta ƙaryata zargin cewa Shugaban Ƙasa Bola Tinubu na raba motocin kamfen na 2027
  • Rahotanni sun ce wata ƙungiya mai goyon baya ce ta kirkiri shirin, ba gwamnati ko shugaban kasa ba
  • Fadar ta lissafo wasu manyan abubuwan da gwamnatin Tinubu ta ce ta cimma cikin ƙasa da shekaru uku

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa. FCT Abuja – Fadar shugaban kasa ta musanta zargin da ke yawo cewa Shugaba Bola Ahmed Tinubu yana raba motocin kamfen domin zaben 2027.

Wannan na ƙunshe a cikin wata sanarwa da Cibiyar Yaɗa Labaran Shugaba Bola Ahmed Tinubu ta fitar a ranar Alhamis.

Fadar Shugaban Kasa ta karyata raba motocin kamfen
Shugaban Najeriya Najeriya Bola Ahmed Tinubu Hoto: Bayo Onanuga
Source: Facebook

A sanarwar da PBAT Media ta wallafa a shafin X, an bayyana cewa motsin da ake gani tare da motocin ba na gwamnatin tarayya ba ne.

Kara karanta wannan

'Da lauje cikin naɗi': Atiku ya yi mamaki da Tinubu ya naɗa tsohon shugaban INEC jakada

Gwamnati ta ƙaryata raba motocin kamfen

Sanarwar ta ƙara da cewa motocin da ake gani suna da alaka da wani shiri ne na ƙungiyar masoya shugaban kasa, ba wani aiki da ya shafi shugaban ƙasa kai tsaye ba.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sanarwar ta ce:

“Wannan abu da ake gani, wani shiri ne da wata ƙungiyar goyon baya mai suna 'Renewed Hope AmbassaThBolahhhhhsbkdors' ta fara."
"Ɗaya ce daga dubunnan ƙungiyoyi da suka nuna goyon bayansu ga shugaban kasa tun lokacin kamfen har zuwa yau ba tare da wani shisshigi daga Shugaban Ƙasa kansa ba.”

A cewar Fadar Shugaban Ƙasa, wannan ƙungiya na gudanar da shirye-shiryen tallafawa jama’a tun wasu shekaru da suka gabata.

Ta ce suna wannan shiri ne domin karfafa manufar Bola Tinubu da kuma nuna goyon bayansu ga sababbin tsare-tsaren shugaban kasa.

Cibiyar ta fahimci dalilin da ya sa jama’a suka yi martani kan motocin, amma ta ja kunne da kada su karkatar da batun zuwa siyasa.

Kara karanta wannan

Farin jinin Matawalle ya fadada, 'yan Kudu sun roki Tinubu game da kujerarsa

Fadar Shugaban kasa ta kambama aikin Tinubu

Sanarwar ta kuma jero wasu muhimman abubuwan da ta ce gwamnati ta samu cikin ƙasa da shekaru uku, amma ƴan adawa ba sa gani.

A cewar ta, tattalin arziki ya samu ci gaba da kashi 3.98 a cikin100 a baya-bayan nan, sannan hauhawar farashin kaya ya sauka zuwa 16%.

Fadar Shugaban Kasa ta ce aiki Tinubu ya saka a gaba
Shugaban Kasa Bola Ahmed Tinubu Hoto: Asiwaju Bola Ahmed Tinubu
Source: Facebook

Haka kuma ta ce sama da dalibai 700,000 ne suka ci gajiyar tsarin lamunin dalibai, sannan an zuba N30bn a shirin rancen da ake ba su.

Fadar ta ƙara da cewa ajiyar kuɗin waje yanzu ya kai Dala biliyan 46, daga Dala biliyan 34 da ta ce gwamnatin da ta gada ta bari.

An kuma ce an inganta tsarin fasfo, ana gudanar da manyan ayyukan gine-gine a faɗin ƙasar, tare da wasu sabbin cigaba a bangaren sufurin jiragen sama

Sanarwar ta ce:

“Shugaba Tinubu ya na da cikakken ƙuduri na gyara matsalolin da ke damun ƙasarmu, kuma babu wata ƙarya ko yaɗa jita-jita da za ta hana canjin da aka fara samu.”

Kara karanta wannan

Allah sarki: Mata, miji da 'ya'yansu duka sun kone yayin gobara a Katsina

Shugaba Tinubu ya godewa ƴan majalisa

A baya, kun ji labari Shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, ya aike da saƙon godiya da yabo ga Majalisar Dattawa bayan ta kammala tantancewar da ta yi wa sabon Ministan Tsaro.

Majalisar ta gudanar da zaman tantancewa Janar Christopher Musa mai ritaya ne a ranar Laraba, 3 ga Disamba, 2025, inda sanatoci suka kwashe sa’o’i suna masa tambayoyi.

Wannan ya biyo bayan nadin da Tinubu ya yi wa Janar Musa, tare da aike da sunansa ga Majalisar Dattawa domin tantancewa kamar yadda kundin tsarin mulkin ƙasa ya tanada.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano. aisha.ahmad@corp.legit.ng