Rashin Tsaro: NLC na Shirin Zazzafar Zanga Zanga a Dukkan Jihohin Najeriya
- Kungiyar kwadago ta NLC ta ce ba za ta sake zama shiru ba yayin da kungiyoyin ta’addanci ke ci gaba da barazana a fadin Najeriya
- Shugaban NLC, Joe Ajaero, ya ce za su ayyana ranar zaman makoki tare da shirya zanga-zanga a fadin kasa bisa yadda rashin tsaro ke ta’azzara
- Femi Falana ya gargadi gwamnati kan yin hattara da kiran neman sojojin ketare su shigo Najeriya, yana mai cewa hakan barazana ne ga kasa
CHECK OUT: How to Start Earning with Copywriting in Just 7 Days – Even if You’re a Complete Beginner
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
FCT, Abuja - Kungiyar Kwadago ta NLC, ta yi gargadin cewa ba za ta ci gaba da zuba ido ’yan ta’adda da masu garkuwa da mutane na kara bazuwa a sassan kasar nan ba.
Kungiyar 'yan kwadagon ta ce ta shirya ayyana ranar zaman makoki da kuma tunkarar tituna domin zanga-zangar kasa baki daya domin nuna adawa da halin da ake ciki.

Source: Facebook
Vanguard ta rahoto cewa shugaban NLC, Joe Ajaero ne ya bayyana hakan a wajen bude taron majalisar zartarwar kungiyar da aka gudanar a birnin Lagos.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
NLC za ta yi zaman makoki da zanga-zanga
Joe Ajaero ya bayyana cewa lamarin tsaro ya kai wani matsayi mai tsanani, inda rayukan malamai, dalibai da ma’aikata ke cikin hatsari a ko’ina fadin kasar.
Business Day ta rahoto ya ce ba za su sake yarda da wannan hali ba, musamman ganin yadda hare-hare da garkuwa da mutane ke karuwa.
Shugaban NLC ya yi korafin cewa akwai alamun gazawa ko kuma wani abu da bai yi daidai ba a tsarin tsaron kasar, musamman ganin yadda aka janye jami’an tsaro kafin sace daliban da aka yi a kwanan nan.
Ajaero ya bayyana cewa wannan batu na bukatar cikakken bincike domin gano ko akwai sabawa doka ko rashin gaskiya a lamarin.
Ya kara da cewa kungiyar za ta shirya zaman makoki da zanga-zanga a kasa baki daya a kwanaki masu zuwa domin adawa da rashin tsaro.
Ficewar wakilan NLC daga jam’iyyar LP
A yayin taron, Ajaero ya kuma sanar da cewa kungiyar ta janye wakilanta daga jam’iyyar LP. Ya ce wakilan ba su wakiltar kungiyar yadda ya kamata.
Wannan mataki, a cewar Ajaero, na nufin NLC ba za ta ci gaba da lamunta da wakilai da ba sa bibiyar manufofin kungiyar da bukatun ma’aikata ba.

Source: Twitter
Joe Ajaero ya ce lokaci ya yi da za a tsaftace wakilci domin kare muradun jama’a masu fama da tsadar rayuwa da rashin tsaro.
Gargadin Femi Falana kan tsaron kasa
Fitaccen lauya kuma mai kare hakkin dan Adam, Femi Falana (SAN), ya yi gargadi a wajen taron, yana mai cewa Najeriya na cikin “babban hadari” saboda karuwar hare-hare, garkuwa da mutane da tashe-tashen hankali.
Ya ce kiran da wasu ke yi na neman sojojin ketare yana da hatsari, yana mai cewa hakan barazana ce ga Najeriya da mutuncin kasar.
Falana ya yi Allah-wadai da wasu kalaman shugaban Amurka, Donald Trump, yana mai cewa dole ne gwamnati ta dauki mataki cikin gaggawa domin kare ’yan Najeriya.
Gumi ya yi addu'a kan 'yan ta'adda
A wani labarin, kun ji cewa Sheikh Ahmad Abubakar Mahmud Gumi ya yi bakar addu'a a kan masu taimakon 'yan ta'adda.
Malamin Musuluncin ya roki Allah ya tona asirin wadanda suka kirkiro ta'addanci a Najeriya ku ke tallafawa masu kai hari a kasar.
Biyo bayan addu'ar Sheikh Ahmad Gumi, jama'a da dama sun yi martani amma ya cigaba da bukatar su ce 'Amin' kawai.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng


