Musulmai a Plateau Sun Mayar da Konannen Coci Masallaci? Kungiya Ta Yi Magana

Musulmai a Plateau Sun Mayar da Konannen Coci Masallaci? Kungiya Ta Yi Magana

  • Kungiyar al'umma a Mangu sun yi karin haske kan ikirarin Fasto Ezekiel Dachomo da ya ce an mayar da coci masallaci
  • Mangu Concerned Muslim Consultative Forum (MCMCF) ta karyata ikirarin Dachomo inda ya ce cocinsa aka kona
  • Kungiyar ta kalubalanci Faston ya gabatar da sunan cocin da lokacin da aka yi zargin canjin, ko kuma ya janye maganarsa

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Mangu, Plateau - Kungiyar Mangu Concerned Muslim Consultative Forum (MCMCF) ta yi magana bayan zargin Fasto da yin karya.

Kungiyar da ke karamar hukumar Mangu a jihar Plateau ta karyata ikirarin da aka danganta wa Rabaran Ezekiel Dachomo na mayar da cocinsa masallaci.

An kalubalanci Fasto kan zargin mayar da coci masallaci a Plateau
Rabaran Ezekiel Dachomo wanda ke zargin ana kisan Kiristoci. Hoto: Ezekiel Dachomo.
Source: Facebook

An soki Fasto kan zargin Musulmai

Rahoton Daily Trust ya ce Dachomo ya zargi cewa an ƙone wani cocinsa a yankin sannan aka mayar da shi masallaci.

Kara karanta wannan

Karancin abinci: Manoma 14,000 sun samu tallafin N4bn a jihar Bauchi

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Al’ummar yankin sun bayyana wannan ikirari a matsayin zargi marar tushe inda suka kalubalanci limamin ya fito da hujjoji domin tabbatar da maganarsa.

A cewar kungiyar, an ruwaito Fasto Dachomo a ranar 1 ga Disamba, 2025, a shafin Phoenix, yana cewa a hirar da ya yi da Channels TV an farmaki daya daga cikin cocinsa a Mangu sannan aka maida shi masallaci.

Musulmi sun dura kan Fasto a Plateau
Taswirar jihar Plateau da ta sha fama da rikice-rikicen addini. Hoto: Legit.
Source: Original

Abin da kungiyar Musulmi ta ce

Amma shugaban kungiyar, Sheik Suleiman Haruna, da sakataren ta, MA Lawal, sun ce babu wata hujja da ke tabbatar da wannan ikirari.

A wata sanarwa da suka fitar a Jos, kungiyar ta ce:

“Wannan zargi an yi ne don nuna Musulmi a matsayin masu ƙwace kadarorin Kirista, tayar da kiyayya, da kuma lalata kokarin zaman lafiya a yankin.”

Kungiyar ta ce ta yi fatali da wannan labari baki ɗaya, tana kuma neman limamin ya gabatar da shaidu ko kuma ya fito cikin jama’a ya janye maganar.

Kara karanta wannan

Shari'ar Musulunci: MURIC ta kalubalanci Amurka, ta faɗi abin da Musulmi za su yi

Sanarwar ta ce:

“Dole Rabaran Dachomo ya kawo sunan cocin da yake zargi, inda yake a Mangu, da kuma lokacin da ake zargin an mayar da shi masallaci.”

Kungiyar ta kara jaddada cewa Musulmi sun kasance masu ladabi da bin doka a lokacin rikice-rikicen da suka faru, inda suka tsare kadarorin Kirista, ciki har da cocin da ke Sabon Kasuwa, wanda ba a taba shi ba duk da rashin jami’an tsaro.

Kungiyar ta ce:

“A gefe guda kuma, masallatai da dama da aka lalata a lokacin rikicin ciki har da wadanda ke Mangu an dawo da wajen zubar da shara da najasa.”

MCMCF ta yi gargadin cewa ba za ta kara yarda wani ya bata sunan al’ummar Musulmi a Mangu ba, tana kuma bukatar Fasto Dachomo ya bayar da hujja ko ya fito ya janye maganarsa tare da ba da hakuri.

Sanarwar ta kara da cewa:

“Zaman lafiya ya kamata ya fi tasiri kan tayar da hankali. Rashin gabatar da hujja a dandalin da aka yada zargin zai tabbatar da cewa maganar ba ta da tushe.”

Kara karanta wannan

Kasa ta rikice: 'Yan bindiga sun yi garkuwa da kusa a APC

Fasto ya nemi a cire Kashim Shettima

An ji cewa Faston da ke da'awar kisan Kiristoci a Najeriya, Ezekiel Dachomo ya ce samun shugaban kasa da mataimakinsa duka Musulmai danniyar siyasa ce.

Ezekiel Dachomo ya zargi gwamnati da aiwatar da abin da ya kira tsarin siyasar Musulunci da nufin mayar da 'yan kasar nan Musulmai baki dayansu.

Ya yi kira ga Kiristoci su farka daga abin da ya kira barcin da suke yi, su kuma ki amincewa da kokarin da gwamantin Najeriya ke yi a kansu.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.