Bwala: 'Yadda Mahaifiyar Tinubu Ta Taka Rawa a Nadin Manyan Mukaman Gwamnati'
- Shugaba Bola Tinubu ya bayyana cewa darasin da ya dauka daga mahaifiyarsa ne ke taka rawa a nade naden mukaman da yake yi
- Daniel Bwala, mai ba shugaban kasa shawara ne ya bayyana hakan yayin da yake martani ga masu sukar jakadun da Tinubu ya nada
- A cewar Bwala, 75% na wadanda ke tare da Tinubu yanzu tsofaffin abokan hamayyarsa ne, saboda shi Tinubu ba ya kin mutane
CHECK OUT: How to Start Earning with Copywriting in Just 7 Days – Even if You’re a Complete Beginner
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Abuja - Daniel Bwala, mai ba shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu shawara kan harkokin yada manufofi, ya bayyana wasu dabarun Tinubu na nadin manyan mukamai.
Bwala ya ce koyarwar mahaifiyar Tinubu ce ke taka muhimmiyar rawa a yadda shugaban ke zaɓen mutanen da zai dora a mukaman gwamnati, ciki har da waɗanda suka taɓa adawa da shi.

Kara karanta wannan
Hadimin Tinubu ya yi martani mai zafi kan kiran Amurka ta hana dokar shari'a a Najeriya

Source: Twitter
Hadimin shugaban kasar ya yi wannan bayani ne a wata hira da aka yi da shi a wani shirin Arise TV a ranar Alhamis, 4 ga watan Disamba, 2025.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Kalaman Bwala dai suna zuwa ne a matsayin martani kan tambayoyin da suka taso game da sunayen wasu jakadu da Tinubu ya nada, alhalin sun taɓa sukarsa a baya.
“Mahaifiyata ta koya min son mutane” — Tinubu
A cewar Bwala, Tinubu ya sha faɗa masa cewa mahaifiyarsa, wadda shugabar ƙungiyar ‘yan kasuwa mata ce a lokacin rayuwarta, ta koya masa cewa shugaba ba ya zama makiyin jama'arsa saboda kuskuren da suka yi.
Bwala ya ruwaito Tinubu yana cewa:
“Idan za ka dinga fushi da mutane saboda sun bata maka rai, wata rana za ka wayi gari babu kowa da za ka jagoranta.
"Mahaifiyata ta yi mun horo a kan son mutane, kuma ka da in rika kin mutane saboda wani kuskure da suka yi muna a baya.”
Bwala ya ce wannan tarbiya da Tinubu ya samu ta nuna dalilin da ya sa shugaban kasar ke maraba da kowa, ciki har da masu hamayya, ko waɗanda suka yi adawa da shi a baya.
“Tsofaffin 'yan adawa ke tare da Tinubu” - Bwala
Daniel Bwala ya ce siyasa cike take da rashin jituwa, amma ana yinta ba da gaba ba, yana mai cewa, ita siyasa ba ta da abokin gaba ko masoyi na dindindin, in ji rahoton Tribune.
A saboda haka, Bwala ya ce shugaban kasa Tinubu yake ɗaukar mutanen da ba sa tare da shi a baya ya ba su mukami idan har ya ga cancantar su na yi wa ƙasa hidima, kamar yadda Legit Hausa ta rahoto a baya.
Hadimin shugaban kasar ya ce:
“Fiye da kashi 70 cikin 100 na mutanen da ke kusa da shi a yau sun taɓa yi masa adawa a wani lokaci a baya.”

Source: Twitter
Haduwar Bwala da Tinubu a karon farko
Daniel Bwala a kuma tuna tattaunawarsa ta farko da Tinubu a ranar 10 ga Janairun bara bayan ya dade yana guje masa saboda matsayinsa da ya dauka kan tikitin Musulmi–Musulmi.
A cewarsa, lokacin da ya shiga wajen Tinubu, ya fara neman yafiya. Sai Tinubu ya dakatar da shi yana mai cewa:
“Ba ka bukatar yin dogon bayani. Idan da ka saurare ni a wancan lokacin, to da ba ka da dalilin shiga wata fargaba kan kudurina.”
Tinubu ya tura jakadu 32 ga majalisa
Tun da fari, mun ruwaito cewa, Shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu ya turo sunayen sababbin jakadu 32 ga Majalisar dattawan Najeriya domin tantancewa.
Daga cikin wadanda aka ga sunansu akwai tsofaffin gwamnoni, tsohon shugaban INEC, matan tsofaffin gwamnoni da manyan jami’an gwamnati.
Wannan na zuwa ne kwanaki kadan bayan Tinubu ya tura sunayen mutum uku da yake son turawa kasashen waje a matsayin jakadun da ake kira 'non-career' a Turance.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Asali: Legit.ng

