Akwai Matsala: Nnamdi Kanu Ya Fadi dalilin Neman Ɗauke Shi daga Gidan Yarin Sokoto

Akwai Matsala: Nnamdi Kanu Ya Fadi dalilin Neman Ɗauke Shi daga Gidan Yarin Sokoto

  • Shugaban kungiyar IPOB, Nnamdi Kanu ya tura roko na musamman ga kotu game da daure shi a gidan gyaran hali na Sokoto
  • Kanu ya roƙi kotu ta dauke shi daga gidan yari na Sokoto zuwa birnin Abuja saboda wasu dalilai da ka iya jawo matsala
  • A cewarsa, kasancewarsa bai tare da lauyan da ke kare shi da kuma rashin damar ganawa da iyali zai ba shi matsala

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Abuja - Shugaban kungiyar IPOB, Mazi Nnamdi Kanu ya roki kotu alfarma bayan kai shi wata magarkama a jihar Sokoto.

Kanu wanda aka yanke wa hukuncin daurin rai-da-rai, ya shigar da korafi yana neman a cire shi daga gidan yarin Sokoto.

Nnamdi Kanu ya roki dauke shi a Sokoto
Shugaban kungiyar IPOB, Nnamdi Kanu. Hoto: Omoyele Sowore.
Source: Twitter

Rokon da Nnamdi Kanu ya yi ga kotu

A cikin buƙatar da ya sanya hannu da kansa, Kanu ya ce zaman sa a Sokoto za ta hana shi yin ingantaccen shiri na daukaka ƙara, cewar Vanguard.

Kara karanta wannan

An taso Nuhu Ribadu a gaba, an bukaci Tinubu ya sauya shi da tsohon soja

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

An gabatar da buƙatar ne ta hannun ƙaninsa, Emmanuel Kanu, wanda ya bayyana cewa Nnamdi Kanu ba zai iya halartar kotu ba saboda yanayi.

Kanu ya ce bayan hukuncin ranar 20 ga Nuwambar 2025, kotu ta umurci a tura shi duk wani gyaran hali banda Kuje saboda dalilai na tsaro.

Ya bayyana cewa an kai shi Sokoto ranar 21 Nuwamba, kuma tazarar kilomita fiye da 700 daga Abuja na hana shi samun damar shirin daukaka ƙara.

Bukatar Nnamdi Kanu ga kotu bayan daure shi a Sokoto
Shugaban IPOB da aka kai gidan yarin Sokoto. Hoto: Emmanuel Kanu.
Source: Twitter

Dalilin neman dauke Kanu daga Sokoto

A cewarsa, yana son ya yi amfani da hakkinsa da kundin tsarin mulki ya ba shi wajen daukaka ƙara, amma hakan na bukatar zuwansa kotu.

Ya ƙara da cewa iyalansa, abokansa da masu ba shi shawara suna Abuja, don haka zama a Sokoto na iya hana shi samun wannan taimako.

Kanu ya ce wannan yanayi yana iya hana shi yin amfani da hakkinsa na daukaka ƙara, wanda ya saba da sashe na 36 na kundin tsarin mulki, cewar Daily Post.

Kara karanta wannan

Natasha ta yi barazana ga Sanata kan sakon WhatsApp, ta sha alwashin tona asiri

Saboda haka, ya roƙi kotu ta umurci gwamnatin tarayya da hukumar gidan yari su mayar da shi kusa da Abuja domin ya iya kare kansa yadda ya kamata.

A madadin haka, ya nemi a tura shi Suleja ko Keffi domin sun fi kusa da kotu, kuma hakan zai taimaka masa wajen aiwatar da shirin daukaka ƙara.

Abin da alkalin ya fada wa Emmanuel Kanu

Bayan karanto korafin, alkalin kotu Mai Shari'a, James Omotosho ya ƙi sauraron Emmanuel, yana mai cewa ba lauya ba ne, don haka ba shi da hurumin gabatar da buƙata.

Alkalin ya ce dole ne Kanu ya samu lauya ko yin amfani da taimakon wasu lauyoyi domin doka ba ta amince da ɗan uwa ya wakilce shi ba.

Ya kuma gargadi jama’a game da bayanan da ka iya ruɗar da mutane, yana mai cewa Kanu ba lallai ya kasance a kotu domin a tattara bayanan ƙara ba.

Gwamna ya ziyarci Nnamdi Kanu a Sokoto

Mun ba labarin cewa Gwamnan Abia Alex Otti ya kai ziyarar farko ga Nnamdi Kanu a gidan gyaran hali da ke Sokoto.

Kara karanta wannan

'Ni ne mafi girman Kirista a gwamnati': Akpabio ya fadi yadda ya taso a kaskance

Babbar kotun tarayya a Najeriya ta yanke wa Nnamdi Kanu, shugaban haramtacciyar kungiyar 'yan ta'addan IPOB hukuncin a watan Nuwambar 2025.

Kotu ta tabbatar da kama shi da laifuffukan ta'addanci da suka hada da kitsa hari ga ofishin UN a Abuja da kashe jami'an tsaro.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.