Ba Wasa: Janar Christopher Musa Ya Sha Sabon Alwashi bayan Zama Ministan Tsaro

Ba Wasa: Janar Christopher Musa Ya Sha Sabon Alwashi bayan Zama Ministan Tsaro

  • Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya rantsar da Janar Christopher Musa (mai ritaya) a matsayin sabon Ministan tsaro
  • Janar Christopher Musa zai kama aiki a matsayin Ministan tsaro bayan murabus din Mohammed Badaru Abubakar
  • Sabon Ministan tsaron kasar ya alwashin cewa zai yi duk mai yiwuwa domin ganin cewa tsaro ya samu a Najeriya

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

FCT, Abuja - Sabon Ministan tsaron Najeriya, Janar Christopher Musa (ritaya), ya sha alwashin cewa zai kawo sauye-sauyen gaggawa a fannin tsaro.

Janar Christopher Musa ya tabbatar wa ‘yan Najeriya cewa rundunar sojoji karkashin jagorancinsa za ta ɗauki duk wani mataki da ya zama dole domin dawo da zaman lafiya.

Janar Christopher Musa ya zama Ministan tsaro
Janar Christopher Musa yayin rantsar da shi a matsayin Ministan tsaro Hoto: @aonanuga1956
Source: Twitter

Jaridar Leadership ta kawo rahoto cewa Janar Christopher Musa ya yi wannan jawabi ne a fadar shugaban kasa ranar Alhamis, 4 ga watan Disamban 2025.

Kara karanta wannan

Janar Musa: Tinubu ya dauki mataki na gaba bayan majalisa ta amince da nadin Ministan tsaro

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sabon Ministan ya bayyana hakan ne jim kaɗan bayan Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya rantsar da shi.

Shugaba Tinubu dai ya naɗa shi ranar Talata, kuma majalisar dattawa ta tabbatar da shi a ranar Laraba, bayan murabus din da tsohon Minista Mohammed Badaru ya yi kan dalilan lafiya.

Wane alwashi Janar Musa ya sha?

Sabon Ministan ya ce abin da ya fi muhimmanci yanzu shi ne karfafa haɗin kai tsakanin rundunonin tsaro da sauran hukumomi, yana mai jaddada cewa ba za a samu tsaro ba sai da haɗin kan dukkan ‘yan kasa, rahoton The Punch ya tabbatar da hakan.

“Abin da ya fi mini muhimmanci yanzu shi ne tabbatar da cewa ma’aikatar tsaro ta taka rawar da ta dace."
"Muna bukatar cikakken haɗin kai tsakanin rundunar sojoji, sauran hukumomin tsaro, da kuma ‘yan Najeriya gaba ɗaya. Tsaro amanar kowa ne."
“Zamu samar da haɗin kai, mu karfafa shi, kuma cikin kankanin lokaci, ‘yan Najeriya za su ga sakamako.”

Kara karanta wannan

Tinubu ya tura sako na musamman ga Majalisa bayan tabbatar da nadin ministan tsaro

- Janar Christopher Musa

Janar Musa ya godewa 'yan Najeriya

Janar Musa ya yi godiya ga irin goyon bayan da ‘yan Najeriya suka nuna masa tun bayan barinsa matsayin CDS, yana mai cewa wannan amincewar za ta kara masa kwarin gwiwa wajen yin abin da ya dace.

“’Yan Najeriya sun nuna mini kauna. Ina tabbatar musu cewa zan yi aiki, zan yi duk mai yiwuwa domin tabbatar da tsaron kasar nan.”

- Janar Christopher Musa

Janar Christopher Musa ya kama aiki a matsayin Ministan tsaro
Sabon Ministan tsaron Najeriya, Janar Christopher Musa (mai ritaya) Hoto: @HQNigerianArmy
Source: Facebook

Game da umarnin da Shugaba Tinubu ya ba shi, Janar Musa ya ce shugaban kasa ya jaddada wajabcin dawo da zaman lafiya da kwanciyar hankali a ko’ina cikin ƙasar.

“Shugaban kasa ya ce dole ne mu tabbatar cewa Najeriya ta zama kasa mai cikakken tsaro. Mutane su koma barci cikin kwanciyar hankali, su koma gonaki, a bude makarantu tare da wata tsangwama ba."

- Janar Christopher Musa

Tinubu ya gana da hafsoshin tsaro

A wani labarin kuma, kun ji cewa shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya gana da manyan hafsoshin tsaro.

Kara karanta wannan

Ministan tsaro, Janar Musa ya ware gwamnoni 6 da suka yi fice a kokarin samar da tsaro

Hafsoshin sun isa fadar shugaban kasa, inda suka sanya labule ba tare da an bar ’yan jarida sun halarci zaman ba.

Babban hafsan hafsoshi, Janar Olufemi Oluyede, shugaban rundunar sojojin kasa, Laftanar Janar W. Shaibu, shugaban rundunar sojojin sama, AVM Sunday Aneke, da shugaban sojojin ruwa, Vice Admiral I. Abbas, sun halarci taron.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng