Janar Musa: Tinubu Ya Dauki Mataki na Gaba bayan Majalisa Ta Amince da Nadin Ministan Tsaro
- Ta tabbata Janar Christopher Gwabin Musa (mai ritaya) wanda yake haifaffen jihar Sokoto, ya zama sabon Ministan tsaron Najeriya
- Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya rantsar da Christopher Musa a matsayin sabon Ministan tsaro a fadarsa da ke Aso Rock Villa a birnin tarayya Abuja
- Rantsar da shi a sabon mukamin na sa na zuwa ne bayan majalisar dattawa ta tantance shi tare da amincewa da shi a matsayin Ministan Tsaro
CHECK OUT: How to Start Earning with Copywriting in Just 7 Days – Even if You’re a Complete Beginner
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
FCT, Abuja - Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya rantsar da sabon Ministan tsaron Najeriya bayan amincewar majalisar dattawa.
Shugaba Tinubu ya rantsar da Janar Christopher Gwabin Musa (mai ritaya) a matsayin sabon Ministan Tsaro na Najeriya a yau.

Source: Twitter
Hadimin shugaban kasa, Bayo Onanuga ya ce an yi rantsuwar ne a fadar shugaban kasa da ke Abuja, ranar Alhamis, 4 ga watan Disamban 2025, a wani rubutu da ya yi a shafinsa na X.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Tinubu ya nada Janar Christopher Ministan tsaro
Idan ba a manta ba, shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya zabi Janar Christopher Gwabin Musa (mai ritaya) a matsayin Ministan tsaro a ranar Talata, 2 ga watan Disamban 2025.
Shugaban kasar ya aika da wasika zuwa ga majalisar dattawa domin tantancewa da amincewa da Janar Christopher Musa a matsayin Ministan tsaro.
Nadin dai da Shugaba Tinubu ya yi masa na zuwa ne kasa da wata biyu bayan ya sauke shi daga mukamin babban hafsan hafsoshin tsaro (CDS), a wani garambawul da ya yi a fannin tsaro.
Majalisa ta tantance Janar Christopher Musa
Aranar Laraba, 3 ga watan Disamban 2025, majalisar dattawa ta tabbatar da nadin Janar Christopher Musa bayan wani dogon zaman tantancewa da ya ɗauki kusan awanni biyar.
A lokacin tantancewar, tsohon babban hafsan hafsoshin tsaro (CDS) ɗin ya fuskanci tambayoyi masu tsanani kan matsalolin tsaro da suka faru kwanan nan.

Kara karanta wannan
Tinubu ya tura sako na musamman ga Majalisa bayan tabbatar da nadin ministan tsaro
Cikin matsalolin da suka faru har da janye sojoji daga makarantar Government Comprehensive Girls Secondary School (GGCSS) Maga, jihar Kebbi, kafin sace ‘yan mata a ranar 17 ga Nuwamban 2025.
Ya shaida wa ‘yan majalisar cewa zai gaggauta kafa kwamitin bincike game da janye dakarun sojojin da zarar ya kama aiki.
Haka kuma ya yi alkawarin binciken kisan da 'yan ta'addan ISWAP suka yi wa Birgediya Janar Musa Uba, a jihar Borno, tare da wasu hare-hare da suka shafi manyan jami'an soja.

Source: Facebook
Nadin Musa ya biyo bayan murabus din tsohon Ministan tsaro, Mohammed Badaru, wanda aka ce ya ajiye aiki ne bisa dalilan lafiya.
Mohammed Badaru Abubakar dai ya rike mukamin tun daga shekarar 2023 bayan nadin da Shugaba Tinubu ya yi masa.
Shugaba Tinubu ya tura sako ga majalisa
A wani labarin kuma, kun ji cewa shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu, ya aika da muhimmin sako ga majalisar dattawan Najeriya.
Tinubu ya aika da sakon yaba ga majalisar dattawa bayan ta kammala aikinta kan sabon Ministan Tsaron Najeriya, Janar Christopher Gwabin Musa (mai ritaya).
Shugaban kasar ya bayyana godiyarsa ga majalisar dattawan saboda gudunmawar da ta bayar wajen hanzarta tabbatar da Janar Christopher Musa (mai ritaya) a matsayin sabon Ministan tsaro.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng
