Cikakken Jerin Sunayen Jakadu 62 da Tinubu Ya Nada da Jihohin da Suka Fito a Najeriya
Abuja, Nigeria - Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya tura sunayen mutanen da ya kara nadawa a matsayin jakadun Najeriya ga Majalisar Dattawa.
CHECK OUT: How to Start Earning with Copywriting in Just 7 Days – Even if You’re a Complete Beginner
Bayan sunayen mutum uku na farko da mutane 32 na rukuni na biyu, Tinubu ya kara yawan jakadun zuwa 62.

Source: Twitter
Jaridar Daily Trust ta ruwaito wadanda aka nada sun kunshi cikakkun jakadu masu gogewa a harkokin jakadanci da kuma sababbin shiga.
Tinubu ya nada Ibas da Dambazau
Daga cikin jakadun akwai Ibok-Ete Ekwe Ibas, tsohon Shugaban Rundunar Sojin Ruwa kuma tsohon shugaban riko na Jihar Ribas da tsohon hafsan sojin kasa kuma tsohon ministan cikin gida, Laftanar Janar Abdulrahman Dambazau (rtd.).
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
A wasikar da shugaban Majalisar Dattawa, Godswill Akpabio ya karanta, Tinubu ya ce ya yi wannan nadi ne dogaro da sashe na 171(1), (2)(c), da (4) na Kundin Tsarin Mulki, in ji Punch.
Majalisar Dattawa, ƙarƙashin shugaban ta Senator Godswill Akpabio, ta tura sunayen zuwa Kwamitin Harkokin Kasashen Waje domin su yi aiki a kansu su dawo da rahoto cikin mako guda.
Sunayen cikakkun jakadu masu gogewa 34
Jakadu 34 masu gogewa da Tinubu ya nada sun hada da:
1. Ambasada Mwaobiola Ezeuwo Chukwuemeka (Abia)
2. Maimuna Ibrahim (Adamawa)
3. Enpeji Monica Okochukwu (Anambra)
4. Ambasada Mohammed Mahmoud Lele (Bauchi)
5. Endoni Sindup 5B (Bayelsa)
6. Ambasada Ahmed Mohammed Monguno (Borno)
7. Jen Adams Ni Okun Michael (Kuros Riba)
8. Ambasada Clark Omeru Alexandra (Delta
9. Chima J. Leoma Davies (Ebonyi)
10. Oduma Yvonne Ehinose (Edo)
11. Wasa Shogun Ige (Edo)
12. Ambasada Adeyemi Adebayo Emmanuel (Ekiti)
13. Ambasada Onaga Ogechukwu Kingsley (Enugu)
14. Ambasada Magaji Umar (Jigawa)
15. Ambasada Mohammed Saidu Dahiru (Kaduna)
16. Ambasada Abdul Salam Abus Zayat (Kano)
17. Ambasada Shehu (Katsina)
18. Ambasada Aminu Nasiru (Katsina)
19. Ambasada Abubakar Musa Musa (Kebbi)
20. Ambasada Haidara Mohammed Idris (Kebbi)
21. Ambasada Bako Adamu Umar (Kogi)
22. Ambasada Sulu Gambari (Kwara)
23. Ambasada Romata Mohammed Omobolanle (Legas)
24. Ambasada Shaga John Shama (Nasarawa)
25. Salau Hamza Mohammed (Neja)
26. Ambasada Ibrahim Dan Lamy (Neja)
27. Adjola Ibrahim Mopolola (Ogun)
28. Ruben Abimbola Samuel (Ondo)
29. Ambasada Akonde Wahab Adekola (Osun)
30. Ambasada Ariwani Adedokun Esther (Oyo)
31. Ambasada Gedagi Joseph John (Filato)
32. Ambasada Luther Obomode Ayokatata (Ribas)
33. Danladi Yakubu Yaku (Taraba)
34. Bidu Dogondagi (Zamfara)
Sunayen sababbin jakadu
Rukuni na biyu ya kunshi mutanen da ba su taba aikin jakadanci ba. Ga su kamar haka:
35. Sanata Grace Bent (Adamawa)
36. Sanata Ita Enang (Akwa Ibom
37. Nkechi Linda Okocha (Anambra)
38. Farfesa Mahmud Yakubu (Bauchi)
39. Philip K. Ikurusi (Bayelsa)
40. Paul Olga Adiku (Benuwai)
41. Vice Admiral Ibok-Ette Ibas (rtd.) (Kuros Riba)
42. Hon. Abbasi Brahma (Edo)
43. Erelu Angela Adebayo (Ekiti)
44. Barista Olumilua Oluwayemika (Ekiti)
45. Rt. Hon. Ogwanyi Ifeanyi (Enugu)
46. Chioma Ohakim (Imo)
47. Lt-Gen. Abdulrahman Dambazau (rtd.) (Kano)
48. Tasiu Musa Maigari (Katsina)
49. Abubakar Sanusi Aliu (Kogi)
50. Femi Pedro (Legas)
51. Barista Mohammed Obanduma Aliu (Nasarawa)
52. Sanata Jimoh Ibrahim (Ondo)
53. Joseph Yusuf Shara’aji (Ondo)
54. Femi Fani-Kayode (Ogun)
55. Fatima Florence Ajimobi (Oyo)
56. Lola Akande (Oyo)
57. N. Gambo (Filato)
58. Farfesa Nora Ladi Daduut (Filato)
59. Onweze Chukwudi (Ribas)
60. Dr. Kulu Haruna Abubakar (Sakkwato)
61. Rt. Hon. Jerry Samuel Manwe (Taraba)
62. Adamu Garba Tarba-Nagri (Yobe).

Source: Facebook
Majalisa ta fara tantance jakadu 3 na farko
A wani rahoton, kun ji cewa kwamitin harkokin kasashen waje na majalisar dattawa ya fara tantance jakadu uku da Shugaba Bola Tinubu ya aiko don tabbatarwa.
Tantancewar ta gudana ne a ranar Laraba a Abuja, inda Kayode Are daga Ogun, Aminu Dalhatu daga Jigawa da Ayodele Oke daga Oyo suka bayyana gaban kwamitin.
Wannan jerin sunaye guda uku dai shi ne farkon rukuni na jakadu da Tinubu ya aika nwa majalisa bayan tsawon sama da shekaru biyu ba tare da nadin jakadu ba.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng


