Majalisa Ta Tantance Oke, Are da Dalhatu, Abu 1 Ya Rage Su Zama Jakadun Najeriya

Majalisa Ta Tantance Oke, Are da Dalhatu, Abu 1 Ya Rage Su Zama Jakadun Najeriya

  • Kwamitin harkokin kasashen waje na majalisar dattawa ya fara tantance jakadu uku da Shugaba Bola Tinubu ya aiko don tabbatarwa
  • Kayode Are, Aminu Dalhatu da Ayodele Oke sun bayyana gaban kwamitin majalisa, inda aka gudanar da tantancewar a bayan fage
  • Yanzu dai mutanen uku na zaman jiran tsammani yayin da kwamitin zai gabatar da rahotonsa don duba yiyuwar amincewa da nadinsu

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Abuja - Kwamitin Harkokin Ƙasashen Waje na Majalisar Dattawa ya fara tantance jakadu uku da Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya aika masu domin tabbatarwa.

Tantancewar ta gudana ne a ranar Laraba a Abuja, inda Kayode Are daga Ogun, Aminu Dalhatu daga Jigawa da Ayodele Oke daga Oyo suka bayyana gaban kwamitin.

Majalisar dattawa ta fara tantance sababbin jakadun da Tinubu ya aika mata.
Shugaban majalisar dattawa, Sanata Godswill Akpabio ya shiga zauren majalisa don fara zama. Hoto: @NGRSenate
Source: Twitter

Majalisa ta tantance jakadu 3 da Tinubu ya nada

Kara karanta wannan

Tinubu ya ci gaba da nade nade, ya sake zabo jakadun da za su wakilci Najeriya

Wannan jerin sunaye guda uku dai shi ne farkon rukuni na jakadu da Tinubu ya aika nwa majalisa bayan tsawon sama da shekaru biyu ba tare da nadin jakadu ba, in ji rahoton Punch.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Zaman tantancewar ya kasance ne a bayan fage, wanda ya bai wa kwamitin damar tattauna wasu muhimman bayanai na sirri tare da kowane daga cikin mutanen uku.

Bayan tattaunawar, kwamitin ya bayyana cewa ya kammala tantance jakadu uku da shugaban kasar ya fara aike mata.

Shugaban kwamitin, Sanata Abubakar Sani Bello, ya bayyana cewa Ayodele Oke ya amsa tambayoyi kan tuhume-tuhumen da aka taɓa yi masa tun yana jagorantar hukumar NIA, kuma ya wanke kansa a gaban kwamitin.

Tarihin ayyukan jakadu 3 da aka tantance

Kayode Are ya taɓa jagorantar hukumar tsaro ta farin kaya (SSS) daga 1999 zuwa 2007, sannan ya zama mai ba shugaban kasa shawara kan harkokin tsaro a 2010.

Har ila yau, Kayode Are ya samu digiri da mafi kololon maki (First Class) a fannin ilmin halayyar 'dan adam daga Jami'ar Ibadan a 1980, kamar yadda Legit Hausa ta rahoto.

Aminu Dalhatu kuwa ya taɓa zama jakadan Najeriya a ƙasar Koriya ta Kudu a lokacin mulkin tsohon Shugaba Muhammadu Buhari.

Kara karanta wannan

An fara sabon takun saka tsakanin gwamna Fubara da yaran Wike a majalisar Rivers

Ayodele Oke shi ma gogaggen jami’in diflomasiyya ne wanda ya yi aiki a matsayin Darakta Janar na NIA, sannan daga baya ya wakilci Najeriya a ofishin Majalisar Commonwealth ta kasashen rainon Birtaniya a Landan.

Shugaba Tinubu dai ya roki majalisar dattawa da ta gaggauta amincewa da nadin jakadun Najeriya.
Shugaba Bola Tinubu ya na magana gaban zauren hadin gwiwa na majalisar tarayya. Hoto: @officialABAT
Source: Twitter

Ana jiran rahoton kwamitin majalisa

A lokacin da Sanata Akpabio yayin karanta wasikar Shugaba Tinubu, ya ce sunayen jakadu uku na farko ne kawai, kuma sauran jakadu za su biyo baya.

A cewarsa, wannan mataki na shugaban ƙasa ya kawo ƙarshen gibin shugabanci da ofisoshin jakadancin Najeriya suka yi tsawon lokaci ba tare da manyan jakadu ba.

Yanzu da aka tantance jakadu uku na farko, an ce za a jira kwamitin harkokin kasashen waje ya gabatar da rahotonsa a gaban zauren majalisa, in ji rahoton Channels TV.

Rahoton ya nuna cewa, majalisar za ta yi amfani da rahoton kwamitin ne domin duba yiwuwar tabbatar da nadin jakadu ko akasin hakan, nan ba da jimawa ba.

Tinubu ya tura karin jakadu ga majalisa

A wani labarin, Legit Hausa ta rahoto cewa, Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya turo karin sunayen sababbin jakadu 32 ga majalisar dattawa domin tantancewa.

Kara karanta wannan

Matan da Shugaba Tinubu ya zaba don zama jakadun Najeriya a kasashen waje

Daga cikin wadanda aka ga sunansu akwai tsofaffin gwamnoni, tsohon shugaban INEC, matan tsofaffin gwamnoni da manyan jami’an gwamnati.

A cikin wasiku biyu daban-daban da ya turo wa Shugaban Majalisar Dattawa, Godswill Akpabio, Tinubu ya nemi majalisar ta gaggauta tabbatar da sababun jakadun.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com