"Sun Aikata Zunubi," Hukumar NJC Ta Dakatar da Manyan Jami'an Gwamnati 2 a Kano
- Hukumar NJC ta dauki mataki mai tsauri kan wasu jami'an gwamnatin Kano da ke aiki a bangaren shari'a bayan gudanar da bincike
- NJC ta dakatar da wasu manyan jami'an kotu biyu ciki har da babban rajistara tare da tsaida albashinsu sai an gama bincike
- Hukumar ta ce ba za ta lamunci rashin ladabi da bin doka a harkokin shari'a ba saboda muhimmancin aikin ga al'umma
CHECK OUT: How to Start Earning with Copywriting in Just 7 Days – Even if You’re a Complete Beginner
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Kano, Nigeria - Hukumar Kula da Harkokin Shari’a ta Jihar Kano (JSC) ta ɗauki matakai masu tsauri kan wasu jami’an kotu bayan kammala binciken da Kwamitin Ƙorafe-Ƙorafen Jama’a (JPCC) ya gudanar.
Hakan dai na kunshe ne a wata sanarwa da mai magana da yawun hukumar, Baba Jibo Ibrahim, ya fitar a ranar Laraba.

Source: Facebook
JSC ta ce matakan sun biyo bayan kwashe shekarun an karya ka’idoji a cikin ma’aikatan bangaren shari’a, kamar yadda Leadership ta ruwaito.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
JSC ta gargadi alkalin kotun shari’a
Hukumar ta gargadi Umar Bala Musa, alkalin babbar kotun shari'ar musulunci da ke Dambatta bisa gaza fitar da rubutaccen bayanin zaman kotu cikin kwanaki bakwai da doka ta tanada.
JSC ta umarce shi da ya koma bin doka da ladubban aikin shari’a kamar yadda ya kamata domin yi wa al'umma adalci.
An dakatar da rijistara a jihar Kano
Bayan haka, hukumar ta dakatar da Saifuddeen Mukhtar Abdullahi, babban rijistara sashen kula da harkokin kotunan Kano
Ta dauki wannan mataki ne kan zarge-zargen almubazzaranci da kuɗin ƙungiyar haɗin gwiwa, s hannu na bogi da bayar da rahotannin kuɗi masu karo da juna.
Hukumar JSC ta kuma amince da shawarar kwamitin JPCC cewa a miƙa Saifudden ga ‘yan sanda, tare da dakatar da shi ba tare da albashi ba har zuwa ƙarshen bincike.
NJC ta dakatar da jami'in kotun shari'a
Hakanan an dakatar da Kamal Ado, wani babban jami'i a kotun shari'a ta Kurna bisa zarge-zargen da suka hada da shari’ar da yake fuskanta a kotun tarayya kan miyagun ƙwayoyi.
Sauran laififfukan da ake zargin ya aikata sun hada da kai hari ga jami’an bincike, lalata motar gwamnatin Kano, sakin wanda ake zargi ba bisa ka’ida ba da katsalandan a shari'a.
Hukumar NJC ta bayyana cewa an dakatar da shi ba tare da albashi ba saboda tsanani da nauyin laifuffukan da ake zargin ya aikata, cewar rahoton Punch.

Source: Twitter
An taso gwamnatin Kano kan kasafin 2025
A wani labarin, mun kawo cewa musayar yawu mai zafi ta barke tsakanin hadimin Ganduje kuma tsohon kwamishinan yada labari, Muhammad Garba da gwamnatin Kano.
Ya ce gwammatin NNPP mai ci ta cika mutane da surutu amma rahoton ayyukan kasafin kudi ya nuna gazawarta daga Janairu zuwa Satumba, 2025.
Kwamishinan Albarkatun Ruwa na Kano, Umar Haruna Muhammad Doguwa, ya mayar da martani, yana mai cewa zargin Garba siyasa ce kawai amma ba shi da hujja.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

