Janar Musa Ya Bude Sabon Babin Tsaro a Najeriya, Ya Soki Sulhu da 'Yan Bindiga
- Ministan Tsaro, Janar Christopher Musa, ya ce gwamnati ba za ta sake shiga tattaunawa da ‘yan ta’adda ko biyan fansa ba a lokacinsa
- Ya ce ya zama dole a inganta dokokin yaki da ta’addanci, musamman hanzarta shari’o’i da tsaurara hukunci ga masu yin garkuwa da mutane
- Sabon ministan ya bayyana haka ne yayin wani zaman majalisar datattawan Najeriya domin tantance shi bayan Bola Tinubu ya tura sunan shi
CHECK OUT: How to Start Earning with Copywriting in Just 7 Days – Even if You’re a Complete Beginner
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
FCT, Abuja - Yayin tantance Ministan tsaro, Janar Christopher Musa (Mai ritaya), ya bayyana cewa ba a bukatar kowace gwamnati ta shiga tattaunawa da masu garkuwa da mutane ko ‘yan ta’adda a fadin ƙasar nan.
Ya ce biyan kudi ga miyagun mutane yana ƙara musu ƙarfin da komawa kai hare-hare, wanda hakan ke barazana ga zaman lafiya.

Source: Twitter
Vanguard ta wallafa cewa Janar CG Musa ya ce yaki da ta’addanci ba zai taba yin tasiri ba muddin ba a gina wani babban kundin bayanan jama’a guda ɗaya da zai haɗa bayanan tsaro, bankuna da takardun shaidar zama ‘yan ƙasa ba.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Janar Musa ya ce babu sulhu da 'yan ta'adda
A jawabin da ya yi lokacin tantancewa a Abuja, Janar Musa ya bayyana karara cewa dole gwamnati ta kafa dokar hana biyan kudi ga ‘yan ta’adda ko sulhu da su.
Ya bayyana yadda biyan fansa ke zama hanyar da ‘yan ta’adda ke sake tara kudi, sayen makamai da shirya sababbin hare-hare.
Ya ce:
“Ba wani sulhu da duk wani mai laifi. Idan aka biya kudin fansa, ana ba su lokaci ne su sake shiryawa, sannan a ƙarshe su komo su kai farmaki.”
Sabon ministan ya kuma ce tsarin bankin Najeriya na iya gano hanyoyin da ake amfani da kudi wajen aikata laifuffuka idan aka yi amfani da shi yadda ya kamata.
Bukatar hada kai a yaki da 'yan ta'adda
Janar Musa ya ce karfin soji kawai ba zai iya kawo ƙarshen ta’addanci ba, domin aikin soja na ɗaukar kaso 25 zuwa 30 cikin 100 na yaki da ta’addanci.
Ya ce talauci, jahilci, rashin shugabanci mai inganci da gazawar kananan hukumomi na daga cikin manyan matsalolin da ke haifar da rikice-rikice.
Haka kuma ya soki jinkirin shari’o’in masu laifin ta’addanci a Najeriya, yana mai cewa daukar dogon lokaci kan rage kwarin gwiwar jami’an tsaro.

Source: Twitter
Janar Musa ya bukaci kafa kotuna na musamman da za su yi hanzarin sauraron shari’o’in ta’addanci da garkuwa da mutane.
A karshen jawabin nasa, ya ce tabbatar da tsaron manoma da farfado da noman abinci ya zama ginshiƙi na kwanciyar hankali a ƙasar nan.
Janar Musa ya ce dole a daina kashe jama'a
A wani labarin, mun kawo muku cewa sabon ministan tsaron Najeriya, Janar Christopher Musa ya ce dole su dauki matakan kare rayukan jama'a.
Rahotanni sun nuna cewa sabon ministan ya ce zai mayar da hankali wajen aiki tukuru domin 'yan Najeriya suna fatan ya samu nasara.
Ya kara da cewa rashin tsaro ya shafi kowa da kowa a kasar nan, saboda haka akwai bukatar hada kai wajen kawo karshen 'yan ta'adda.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng


