Sanusi II Ya Fadi Tasirin Addu'ar Dahiru Bauchi wajen Maido Shi Sarautar Kano

Sanusi II Ya Fadi Tasirin Addu'ar Dahiru Bauchi wajen Maido Shi Sarautar Kano

  • Sarki Muhammadu Sanusi II ya ziyarci gidan Sheikh Dahiru Usman Bauchi domin yin ta’aziyya bayan rasuwar fitaccen malamin
  • Sanusi II ya bayyana tsawon alaƙarsa da Sheikh Dahiru Bauchi tun daga kakanni, yana mai cewa malamin yana yawan masa addu’o’i
  • Ya ce addu’ar Sheikh Dahiru Bauchi ta kasance ginshiƙi wajen dawo da shi kan mulkin Kano da Gwamna Abba Kabir Yusuf ya yi

Jihar Bauchi — A jiya Laraba, Sarki Muhammadu Sanusi II ya ziyarci gidan marigayi Sheikh Dahiru Usman Bauchi domin mika ta’aziyya ga iyalan fitaccen malamin da ya rasu.

A bayanan da ya yi, Muhammadu Sanusi II ya bayyana cewa alaƙarsa da marigayin ta samo asali tun kakanni, kuma ta kasance cike da girmamawa da soyayya.

Sanusi II da Sheikh Dahiru Bauchi
Sarki Muhammadu Sanusi II da Sheikh Dahiru Usman Bauchi. Hoto: Masarautar Kano|Sayyid Ibrahim Sheikh Dahiru Usman Bauchi
Source: Facebook

Legit Hausa ta tattaro bayanan da Muhammadu Sanusi II ya yi ne a cikin wani bidiyo da fadarsa ta wallafa a shafin X.

Addu’ar Sheikh Dahiru Bauchi ga Sanusi II

Kara karanta wannan

Sarki Sanusi II ya fadi dalilin rashin zuwa jana'izar Sheikh Dahiru Bauchi

Sanusi II ya bayyana cewa yana yawan tuntubar Sheikh Dahiru a lokuta daban-daban, inda ya ce mai sunan Chiroma ne ke hada su a waya domin su gaisa.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sarkin ya ce duk lokacin da ya kira mai sunan Chiroma, malamin yana karbar wayarsa tare da yi masa addu’a cikin karamci da kauna.

Ya kuma tuna cewa lokacin da Abdullahi Umar Ganduje ya sauke shi daga sarauta, Sheikh Dahiru ya karanta masa ayar ta 87 a Suratul Qasas, alamar da ke nuna cewa zai dawo.

Ya ce daga baya addu’o’in Sheikh Dahiru Bauchi sun kasance cikin dalilan da suka taimaka wajen dawo da shi kan sarautar Kano da Gwamna Abba Kabir Yusuf ya tabbatar.

Alaƙar Sanusi II da Sheikh Dahiru Bauchi

Sanusi II ya jaddada cewa dangantakarsu da Sheikh Dahiru Bauchi ta yi tsawo sosai, tun daga lokacin kakansa Muhammadu Sanusi I.

Khalifan ya ce ya sha haduwa da marigayin a Azare, lokacin da suke ziyartar kakansa, inda ya ga irin girmamawar da suke ma juna.

Ya kara da cewa alaƙar Sheikh Dahiru Bauchi da iyalansu ta kasance mai karfi, saboda malamin ya yi hulɗa da kakansa, mahaifinsa har zuwa ga shi kansa. Ya ce saboda wannan tarihi mai tsawo, ya kuduri aniyar ci gaba da kulla alaka da iyalan malamin.

Kara karanta wannan

Sheikh Dahiru Bauchi ya taka wa masu Maulidi burki a wasiyyar da ya bari

"Wajen Dahiru Bauchi na yi tarbiyyar Tijjaniya' - Sanusi II

Sanusi II ya bayyana cewa ya samu tarbiyyar Darikar Tijjaniyya ta hannun Sheikh Dahiru Usman Bauchi, kuma yana da matukar godiya ga Allah kan hakan.

A wajen ne kuma Sanusi II ya yi bayanin yadda ya karbi darikar daga wajen kakansa.

Sanusi II a gidan Sheikh Dahiru Usman Bauchi
Lokacin da Sanusi II ya je gidan Sheikh Dahiru Bauchi. Hoto: Masarautar Kano
Source: Facebook

A lokacin ziyarar, Sarki Sanusi II ya je tare da manyan malaman Darikar Tijjaniyya daga Kano, ciki har da ‘yan majalisar shura na darikar.

Sanusi II ya yabi rayuwar Sheikh Dahiru Bauchi, yana mai cewa shekaru da Allah ya ba shi na karantar da al’umma alama ce ta rayuwa mai albarka.

Sanusi II bai je jana'izar Dahiru Bauchi ba

A wani labarin, kun ji cewa mai martaba Muhammadu Sanusi II ya mika uzuri kan rashin zuwa jana'izar marigayi Sheikh Dahiru Usman Bauchi.

Sarkin ya bayyana cewa bai samu zuwa jana'izar ba ne saboda ba ya Najeriya a lokacin da babban malamin ya rasu.

Sai dai duk da haka, ya ce ya tura wakilan da suka hada da hakimai domin halartar jana'izar a madadin masarautar shi.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng