Matashi 'Dan Shekara 17 Ya Lallaba Ya Kashe Matar Makwabcinsu cikin Dare a Borno

Matashi 'Dan Shekara 17 Ya Lallaba Ya Kashe Matar Makwabcinsu cikin Dare a Borno

  • 'Yan sanda sun kama wani yaro dan shekara 17 bisa zargin caka wa matar makwabcinsu wuka har lahira a Maiduguri
  • Mazauna yankin sun bayyana cewa yaron mai suna Amir ya shiga gida ya kashe matar bayan sace wayarta da na'urar yin caji
  • Jami'in hulda da jama'a na rundunar yan sandan Borno, ASP Nahum Kenneth Daso ya tabbatar da faruwar lamarin, ya ce ana kan bincike

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Borno, Nigeria - Ana zargi wani yaro dan shekara 17 da haihuwa mai suna Amir ya shiga har cikin gida, ya kashe matar makwabcinsu a jihar Borno.

Kara karanta wannan

Kano: Gwamnati ta yi bayani kan dokar hana acaba, an yi sassauci a wasu yankuna

Rahoto ya nuna cewa matashin ya aikata wannan danyen aiki da ake zargi a unguwar Layin Shagon Harun, Shuwarin II, cikin birnin Maiduguri a jhar Borno.

Jihar Borno.
Taswirar jihar Borno da ke Arewacin Najeriya Hoto: Legit.ng
Source: Original

Jaridar Daily Trust ta rahoto cewa lamarin ya faru ne misalin ƙarfe 10:45 na dare a ranar Talata da ta gabata, 2 ga watan Disamba, 2025.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

'Yan sanda sun kama matashin a Borno

Jami'in hulda da jama'a na rundunar ‘yan sandan jihar Borno, ASP Nahum Kenneth Daso, ya tabbatar da faruwar al’amarin, yana mai cewa an kama wanda ake zargi

Sai dai a cewar kakakin 'yan sanda, rundunar na ci gaba da kokarin tattara bayanai kan abin da ya faru.

Wani mazaunin yankin da ya bukaci a sakaya sunansa, ya ce matashin ya haura ta katangar gidan makwabcinsu ne bayan iyalin sun kwanta barci a daren ranar Talata.

Yadda Amir ya kashe matar a Maiduguri

“Tun da wuri wuri ya shiga ya boye a cikin gidan domin ya jira lokacin da ya dace. Ya yi amfani da wuka ya caka mata a kirjinta da wuyanta,” in ji shi.

Mutumin ya bayyana cewa wanda ake zargi ya gudu da wayar matar da ya kashe da kuma abin caji watau Power bank ɗinta bayan kisan.

Kara karanta wannan

Ta fasu: An fallasa shirin raba Atiku da duniya kafin zaben 2027

Ya kara da cewa:

“Mutane na ganin kamar yaron ya dade yana aikata kisan kai. Ya shiga da wuka ya caka wa matar a kirji da kuma jijiyoyin wuya.”
Jami'an yan sanda.
Jami'an rundunar 'yan sandan Najeriya a bakin aiki Hoto: PolicenNG
Source: Getty Images

A cewarsa, ‘yar uwar mijin marigayiyar ce ta gane wanda ya aikata laifin kana ta sanar da ‘yan sanda.

“Ta fada wa 'yan sanda cewa ta ji matar tana ihun neman agaji bayan yaron ya caka mata wuka.
"Nan take ta sanar dd makwabta don su kawo agaji lokacin da ta ga yaron ya dawo gidan ya wanke hannunsa da rigarsa domin kada a kama shi da hujja dumu-dumu.”

An ce jami’an 'yan sanda na tawagar Police Crack Squad ne suka kama shi da misalin 2:30 na rana a ranar Laraba, kamar yadda Daily Post ta rahoto.

An tsinci gawar budurwa a Bauchi

A wani rahoton, kun ji cewa an shiga rudani bayan gano gawar wata budurwa yar shekara 24, Fatima Salihu Mohammed a harabar Kwalejin Fasaha ta Bauchi.

Kara karanta wannan

Kwana ya kare: Babban jigon APC a Najeriya, Farfesa Abdulgafar ya kwanta dama

Kwamishinan ‘Yan Sanda na Jihar Bauchi, CP Sani-Omolori, ya bayar da.umarnin gudanar da bincike na musamman domin gano yadda lamarin ya faru.

Tun farko dai an gano gawar Fatima ne a cikin gonar da ke cikin harabar Kwalejin Fasaha ta Tarayya da ke Bauchi, ta hannun wani manomi.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262