'Dole a Daina Kashe Jama'a,' Christopher Musa Ya Yi Magana da Babbar Murya
- Janar Christopher Musa ya ce nauyin da ke kansa yana da girma saboda irin fatan da ’yan Najeriya suka nuna bayan nada sa ministan tsaro
- Ya gode wa shugaba Bola Ahmed Tinubu da ya nada shi, tare da gode wa ’yan kasa da suka nuna cikakken amincewa da ba shi mukamin
- Janar Musa ya ce dole ne a daina kisan bayin Allah a Najeriya, yana mai kira a hada kai wajen dakile miyagun da ke tada tarzoma a kasar nan
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
FCT, Abuja – Sabon ministan tsaro, Janar Christopher Musa (Mai ritaya), ya ce ba zai gaza ba a wannan sabon matsayi da aka ba shi, kasancewar ’yan Najeriya na da babban fata a kansa.

Kara karanta wannan
A karshe, majalisa ta amince da nadin Janar Christopher Musa a matsayin ministan tsaro
Ya bayyana haka ne a ranar Laraba yayin tantance sa a gaban majalisar dattawa bayan nada shi da shugaba Bola Ahmed Tinubu ya yi.

Source: Facebook
Daily Trust ta rahoto cewa Janar Musa ya ce martanin da ya gani daga jama’a bayan nada shi ya nuna girman nauyin da ya rataya a wuyansa, wanda ya sa ya kuduri aniyar yin aiki tukuru domin kare rayukan ’yan Najeriya.
A cikin bayanin da ya yi, ya ce haɗin kai ne ginshiƙin nasarar yaki da ta’addanci da sauran matsalolin tsaron Najeriya.
Janar Musa ya ce ba zai gaza ba
A jawabinsa, ya yi bayanai kan yadda ake buƙatar sabbin dabaru da jajircewa don dakile kashe-kashe da barna da ake fama da su a sassa daban-daban na kasar.
Trust Radio ya rahoto ya ce:
“Na san ba zan yarda na gaza ba wajen kare kasata. Duk abin da ya kamata mu yi, za mu yi shi da dukkan ƙarfi, kuma da taimakon Allah za mu yi nasara.”
Ya kara da cewa martanin da ya gani a dandalin sada zumunta bayan nadinsa ya tabbatar masa cewa ’yan Najeriya na son ganin an sami zaman lafiya.

Source: Facebook
Ya ce wannan ne ya kara masa kwarin gwiwa cewa akwai goyon bayan jama’a, kuma hakan na nufin dole ya tashi tsaye wajen tunkarar kalubalen tsaro.
Kira ga hadin kai da dakile kashe jama’a
Sabon ministan tsaro na kasa, Janar Musa ya nuna bacin ransa game da ci gaba da kashe jama’a da ake yi a wasu yankuna.
Ya ce:
“Ko da ana ta ce-ce-ku-ce kan batun kisan kiyashi ko ba kisan kiyashi ba, kowa na cikin wadanda abin ya shafa. Ana kashe kowa, ana hallaka rayuka babu bambancin addini.”
Ya ce miyagun da ke aikata wadannan laifuffuka ba su da tausayi kuma sun riga sun zama mugaye masu mugun hali, inda ya danganta su da amfani da miyagun kwayoyi da rashin sanin darajar dan Adam.
A cewar sa:
“Ba za mu lamunci a ci gaba da kashe ’yan Najeriya ba. Ba wani dalili da zai sa a kashe wani a cikin kasar nan. Abin da ya rage mana shi ne mu fuskance su kai tsaye mu dakatar da wannan ta’asa.”
Gwamnonin Arewa sun hada kai kan tsaro
A wani labarin, mun kawo muku cewa shugaban gwamnonin Arewa, Muhammadu Inuwa Yahaya ya ce sun hada kai don magance rashin tsaro.
Gwamna Inuwa Yahaya ya bayyana cewa za su dauki matakan bai daya domin hana yaduwar ta'addanci a fadin Arewacin kasar.
Ya kara da cewa za su dauki wasu matakai kan tsaro kafin shugaban kasa ya zartar da kafa 'yan sandan jihohi a fadin kasar a gaba.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

