Sarki Sanusi II Ya Fadi Dalilin Rashin zuwa Jana'izar Sheikh Dahiru Bauchi
- Tsohon gwamnan Kogi, Yahaya Bello da Sarki Muhammadu Sanusi II sun ziyarci gidan Sheikh Sheikh Dahiru Usman Bauchi domin ta'aziyya
- Sarki Sanusi II ya kira Musulmi su koyi dabi’un marigayin, ya kuma bayyana dalilin rashin halartarsa jana’iza saboda wasu dalilai da ya fada
- An gudanar da addu’o’i na kwanaki uku a Bauchi inda manyan malamai, jami’an gwamnati da iyalai suka hallara domin tunawa da marigayin
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Jihar Bauchi – Fitattun shugabanni da manyan jiga-jigan kasa sun je gidan marigayi Sheikh Dahiru Usman Bauchi, malamin addinin Musulunci da ya rasu.
Wannan ya bayyana ne a lokacin addu’o’in kwanaki uku da aka gudanar a Bauchi domin tunawa da malamin bayan rasuwarsa.

Source: Facebook
A wani bidiyo da fadar mai martaba Muhammdu Sanusi ta wallafa a X, Sarkin ya bayyana dalilan da suka saka bai samu halartar jana'iza ba.

Kara karanta wannan
Allahu Akhbar: An yi jana'izar Sheikh Dahiru Bauchi, an birne gawarsa a masallaci
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Tsohon gwamnan jihar Kogi, Yahaya Bello, ya ce Sheikh Dahiru Bauchi mutum ne da rayuwarsa ta kare kan bautar Allah da hidima ga al’umma.
Sanusi II ya fadi dalilin rashin zuwa jana’iza
Sarki Khalifa Muhammadu Sanusi II ya yi magana yana mai ba da uzuri kan rashin halartar jana'izar Sheikh Dahiru Usman Bauchi:
“Na fara da bayar da uzuri saboda ban kasance a Najeriya ba lokacin da jana’izar ta gudana. Na dawo kasar nan ne ranar Litinin.”
Sarkin ya ziyarci jihar Bauchi tare da manyan ’yan Tijjaniyya da suka taka masa baya, kuma ya bayyana cewa ya turo hakimai su halarci sallar jana’iza duk da cewa bai kasance a cikin kasar ba.
Sanusi II ya ce Sheikh Dahiru ya bar tarihin tausayi, zaman lafiya, koyi da kyawawan halaye da koyar da Musulunci cikin hikima da natsuwa.
Yahaya Bello ya je gidan Sheikh Dahiru Bauchi
Yahaya Bello ya bayyana Sheikh Dahiru a matsayin malami mai gaskiya da tsoron Allah, mai kaunar zaman lafiya da tausayi ga kowa.
Ya ce koyarwar marigayin ta kasance wajen jaddada zaman tare, jinkai ga marasa galihu da bin ka’idar addini cikin soyayya da hakuri.
Yahaya Bello ya tuna cewa Sheikh Dahiru ya kasance yana yi wa jihar Kogi addu’o’i na musamman a duk lokacin da ya je ziyara, yana mai rokon zaman lafiya, zaman tare da ci gaban kasa.

Source: Facebook
Arise News ta rahoto ya ce ya ce rasuwarsa babban gibi ne ga al’ummar Musulmi da Najeriya baki ɗaya saboda irin rawar da ya taka wajen wanzar da zaman lafiya da fahimtar juna.
Taron addu’ar ya samu halartar Yahaya Bello tare da Sanata Abubakar Ohere, Abubakar Rajab, Isah Omade wanda ya kasance tsohon mataimakin shugaban ma’aikatan fadar gwamnatin Kogi, Sheikh Abdulkudus da sauran mutane masu daraja.
Dahiru Bauchi ya hana a masa Maulidi
A wani labarin, mun kawo muku cewa Sheikh Dahiru Usman Bauchi ya hana mutane su masa Maulidi bayan rasuwarsa.
Malamin ya bayyana haka ne a cikin wata wasiyya da ya yi tun kafin rasuwarsa, inda ya ce yana cikin mabiya Tijjaniyya.
Sheikh Dahiru Bauchi ya kara da cewa ba kowa za a rika yi wa Maulidi ba, domin idan aka yi haka abin zai yi yawa.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

