Majalisa Ta Gaji da Jira, Ta Taso Tinubu a Gaba kan Masu Ɗaukar Nauyin Ta'addanci

Majalisa Ta Gaji da Jira, Ta Taso Tinubu a Gaba kan Masu Ɗaukar Nauyin Ta'addanci

  • Majalisar wakilai ta tura bukata ta musamman ga gwamnatin Bola Tinubu game da ta'addanci a Najeriya domin kawo tsaro a kasar
  • An bukaci gwamnati ta bayyana sunayen wadanda ke daukar nauyin ta’addanci da garkuwa da mutane a fadin kasar
  • ’Yan majalisar sun jaddada bukatar kafa kotu ta musamman don shari’un ta’addanci, fashi da makami da garkuwa da mutane

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Abuja - Majalisar wakilai ta bukaci gwamnatin tarayya ta bayyana sunayen masu daukar nauyin ta’addanci da garkuwa da mutane a Najeriya.

Hakan ya biyo bayan tattaunawar tsaro da aka gudanar a makon da ya gabata a majalisar domin kawo karshen rashin tsaro.

Majalisa ta bukaci bayyana sunayen masu daukar nauyin ta'addanci
Majalisar Wakilai da Bola Tinubu . Hoto: House of Representatives.
Source: Twitter

’Yan majalisar sun nuna damuwa kan karuwar hare-hare da garkuwa da yara a sassa daban-daban, cewar rahoton TheCable.

Sulhu: Abin da fadar shugaban kasa ta ce

Kara karanta wannan

Ba wasa: Matakin da Gwamna Abba zai dauka don dakile hare haren 'yan bindiga a Kano

Wannan na zuwa ne a daidai lokacin da fadar shugaban kasa ta yi magana game da sulhu da yan ta'adda a Najeriya.

Fadar Shugaban Kasa ta bayyana matsayarta a kan sulhu da 'yan ta'adda ko shiga wata yarjejeniya domin ceto wadanda aka yi garkuwa da su.

Hadimin shugaban kasa a kan sadarwa, Daniel Bwala, ya bayyana akwai lokacin da gwamnatin tarayya ta taba hawa teburin tattaunawa da 'yan ta'adda.

Bwala ya ce Shugaba Tinubu ya kawo manufar babu sassauci kan tattaunawa domin wannan na iya zama hanyar tallafawa ta’addanci.

Majalisa ta yunkuro kan kawo karshen ta'addanci
Mambobin majalisar tarayya yayin zamansu a Abuja. Hoto: House of Representatives.
Source: Facebook

Ta'addanci: Abin da majalisar tarayya ke bukata

Mambobin sun ce dole a tsaurara matakai da bayyanawa jama’a gaskiya game da abin da ke faruwa a kasar duba da ƙaruwar ta'addanci.

Rahoton ya ce dole a bayyana sunayen masu daukar nauyin ta’addanci, a hukunta su, kuma shari’u su kasance a bainar jama’a cikin sauri da gaskiya.

Majalisar ta kuma bukaci kafa wata kotu ta musamman da za ta kula da shari’un ta’addanci, garkuwa da mutane da fataucin makamai a fadin kasar.

Kara karanta wannan

Gwamnati za ta kwace filayen Ganduje, Patience Jonathan da wasu manya a Najeriya

’Yan majalisar sun dage cewa hukunci kan haramtattun makamai ya zama mai karfi kuma ana tabbatar da bin doka wajen hukunta masu laifi ba tare da jinkiri ba.

Haka kuma, sun bukaci kafa kwamitin gaskiya da sulhu domin magance rikice-rikice na addini, kabilanci da matsalolin kungiyoyin masu tsatssauran ra'ayi a kasar.

Dukkan shawarwarin tsaro fiye da 40 da aka tattauna za a tura su majalisar dattawa don amincewa, sannan su isa ga shugaban kasa da hukumomi domin aiwatarwa.

Majalisa ta magantu kan yan sandan jiha

Mun ba ku labarin cewa Majalisar Tarayyar Najeriya za ta kada kuri’a kan kafa ’yan sandan jihohi da ba wa kananan hukumomi ‘yancin kai.

Ana duba batun kujerun mata na musamman da kirkirar sababbin jihohi a kokarin yi wa kundin tsarin mulki garambawul domin inganta mulki a Najeriya.

Akwai kudurin ’yan takara marasa jam’iyya ta yadda mutum zai tsaya ba a karkashin kowa ba wajen samun kujera yayin da zaben shekarar 2027 ke karatowa.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.