'Ba Mu Yarda ba,' Majalisa Ta Rikice yayin da Ake Tantance Sabon Ministan Tsaro
- Rikici ya tashi a majalisar dattawa yayin da ake tantance tsohon hafsan tsaro, Christopher Musa a matsayin sabon ministan tsaro
- 'Yan majalisar dattawa sun tashi tsaye cikin fushi, lokacin da wani sanata ya nemi a bar Musa ya tafi ba tare da an yi masa tambayoyi ba
- A karshe, Sanata Godswill Akpabio ya yanke hukunci cewa dole ne Musa ya amsa tambayoyi, "ba wai don majalisa ba ta sonsa ba"
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Abuja - An samu hargitsi a zauren majalisar dattawa a ranar Laraba yayin da ake kokarin tantance sabon ministan tsaro, Christopher Musa.
An samu rikici tsakanin 'yan majalisar ne bayan wasu mambobi sun ki amincewa da bukatar a kyale Christopher Musa ya yi gaisuwa ya tafi kurum.

Source: Facebook
Rigima a majalisa yayin tantance sabon minista

Kara karanta wannan
Ministan tsaro, Janar Musa ya ware gwamnoni 6 da suka yi fice a kokarin samar da tsaro
Rahoton jaridar The Cable ya nuna cewa, wasu sanatoci sun dage cewa, ba za a kyale tsohon hafsan tsaron kasar ya tafi kurum ba, dole ya amsa tambayoyi.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
A yau Laraba ne majalisar dattawa ta sanya don tantance sabon ministan, kamar yadda Shugaba Bola Tinubu ya bukata.
Rigimar ta fara ne lokacin da Sanata Sani Musa, mai wakiltar Neja ta Gabas, ya bukaci majalisar ta amince Janar Musa ya yi gaisuwa ya tafi abin sa.
A cewar Sanata Musa, kowa ya riga da ya san Janar Musa ya kuma san irin ayyukan da ya yi, don haka babu haufi zai aiwatar da aikinsa yadda ake so.
Sanatan ya yi nuni da cewa, babu bukatar a yi wa Janar Musa tambayoyi, a kyale shi kawai ya tafi don tunkarar babban aikin da ke gabansa.
'Yan majalisa sun nuna fushinsu a fili
Sai dai, 'yan majalisa da dama sun nuna kin amincewarsu da wannan kudi na Sanata Musa, inda suka mike tsaye suna ihu, da nuna cewa dole sai Janar Christopher Musa ya amsa tambayoyinsu.

Kara karanta wannan
A karshe, majalisa ta amince da nadin Janar Christopher Musa a matsayin ministan tsaro
Garba Maidoki, sanata mai wakiltar Kebbi ta Kudu, ya nuna fushinsa a fili, kuma har ya je ga shugaban majalisar dattawan, ya na jaddada bukatar yi wa Janar Musa tambayoyi.
Shugaban majalisar Dattawa, Godswill Akpabio ya dakatar da rikicin, inda ya tunatar da 'yan majalisar cewa wannan tantancewar tana da matukar muhimmanci ga 'yan kasa.
Jaridar Punch ta rahoto cewa Sanata Akpabio, ya ce 'yan Najeriya sun zura idanu suna jiran wadanne matakai Janar Musa zai dauka, don kawo karshen matsalolin tsaron kasar.

Source: Facebook
'Trump ya kafa mana kahon zuka' - Akpabio
Sanata Akpabio ya shaidawa 'yan majalisar cewa:
"Al'ummar mazabunmu suna da bukatar ji daga bakinsa. Za mu yi masa tambayoyi ne saboda jama'ar da suka turo mu wakilci na son su yi masa tambayoyi su ma.
"Wannan ba lokaci ne da za mu ce ya yi gaisuwa ya kama gabansa ba. Hatta Donald Trump ya kafa mana kahon zuka yanzu.
"Yayin da kananan yara sama da 200 ke cikin daji hannun 'yan bindiga, dole a bar mutumin ne ya ba mutane kwarin guiwa. Ba wai ba ma sonsa ba ne."
Jim kadan bayan an dawo da kwanciyar hankali a majalisar, Sanata Akpabio ya ci gaba da jagorantar taron tantance tsohon babban hafsan tsaron kasar.
Majalisa ta amince da nadin Janar Musa
A wani labarin, mun ruwaito cewa, Majalisar dattawa ta amince da nadin Janar Christopher Musa a matsayin ministan tsaron Najeriya bayan tantance shi.
A yayin amsa tambayoyi, Janar Musa ya ce matsalolin tsaron Najeriya ba na sojojoji kadai ba ne, dole ana bukatar hadin kan kowane bangare.
Yayin da Sanata Godswill Akpabio ya yabawa Janar Musa, sabon ministan tsaron ya yi kira da a daina biyan kudin fansa ga 'yan bindiga don dakile karfinsu.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng
