Abubuwan da 'Yan Najeriya ke Fatan Samu daga Sabon Ministan Tsaro, Janar Musa
- Wani sanannen lauya mazaunin Abuja, Pelumi Olajengbesi ya yi tsokaci kan nadin Janar Christopher Musa a matsayin Ministan Tsaron Najeriya
- Ya ce 'yan Najeriya na fatan ganin sauye-sauye a dabarun yaki da ta'addanci, wadanda za su dawo da zaman lafiya karkashin sabon ministan
- Shugaba Tinubu ya nada Janar Musa, wanda ya fito daga jihar Kaduna a matsayin Ministan Tsaro bayan Badaru Abubakar ya yi murabus
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Abuja, Nigeria - 'Yan Najeriya na ci gaba da tofa albarkacin bakunansu kan sabon ministan tsaron da Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya nada, Janar Christopher Musa.
Janar Musa (mai ritaya) wanda bai dade da sauka daga matsayin babban hafsan tsaro ba, zai maye gurbin tsohon ministan tsaro da ya yi murabus, Badaru Abubakar.

Source: Facebook
Lauya ya yaba da nadin Janar Musa

Kara karanta wannan
A karshe, majalisa ta amince da nadin Janar Christopher Musa a matsayin ministan tsaro
The Cable ta ruwaito cewa Pelumi Olajengbesi, lauya mai zama a Abuja, ya yaba da nadin Christopher Musa a matsayin Ministan Tsaron Najeriya.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
A ranar Talata da ta gabata ne Shugaba Bola Tinubu ya mika sunan Musa ga Majalisar Dattawa domin tantance shi ya zama sabon Ministan Tsaro.
Da yake martani kan nadin a wata sanarwa da ya fitar yau Laraba, Olajengbesi ya ce babu abin da yan Najeriya ke san gani daga Janar Musa face sauyi a dabarun yaki da ta'addanci.
Ya ce jama'a na fatan sabon ministan zai yi amfani da kwarewarsa wajen kawo canje-canje a dabarun yaki da ta'addanci, yana mai kira ga Janar Musa da kada ya ba mutane kunya.
Abubuwan da jama'a ke fata daga ministan
Ya ce yadda jama’a suka yi maraba da nadin Musa cikin wata guda bayan an cire shi daga matsayin CDS, ya nuna cewa ’yan Najeriya na son kwararru da masu iya aiki su rike manyan mukaman kasa.
Olajengbesi ya bayyana Janar Musa a matsayin daya daga cikin fitattun hafsoshin soja marasa tabo a Najeriya, kamar yadda Punch ta rahoto.
“Janar Musa ya nuna bajinta matuka a matsayin kwamandan Operation Hadin Kai da ke yakar Boko Haram da ISWAP. Haka ’yan Najeriya sun ga ci gaba a yaki da ta’addanci lokacin da yake CDS.”
"Irin wannan gwarzon soja ya dace ya jagoranci dabarun tsaron kasa. Ina fatan Janar Musa, wanda ake sa ran abubuwa da dama daga gare shi, kada ya ba ’yan Najeriya kunya.
"Mutane na sa ran ganin canje-canje masu karfi a dabarun yaki da ’yan ta’adda. Mutane na son ganin sakamako, ba uzuri ba.”
- In ji Pelumi Olajengbesi.

Source: Twitter
Tinubu ya gana da hafsoshin tsaro a Abuja
A wani rahoton, kun ji cewa shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu ya gana da manyan hafsoshin tsaron Najeriya a fadarsa da ke birnin tarayya Abuja.
Hafsoshin sun isa fadar shugaban kasar ne da misalin ƙarfe 4:30 na yamma, inda suka sanya labule da Shugaba Tinubu ba tare da an bar ’yan jarida sun halarta ba.
Bayan taron, babban hafsan tsaro, (CDS) Janar Oluyede ya ce tattaunawar ta kasance mai zurfi inda shugaban kasar ya bada sababbin dabaru da tsauraran umarni wajen kawar da barazanar tsaro.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng
