Badaru Ya Ƙaryata Jita Jitar da Ake Yaɗawa game da Murabus daga Kujerarsa

Badaru Ya Ƙaryata Jita Jitar da Ake Yaɗawa game da Murabus daga Kujerarsa

  • Tsohon Ministan Tsaro a Najeriya, Mohammed Badaru Abubakar ya yi karin haske game da yada jita-jita bayan ya yi murabus
  • Badaru ya karyata rahoton bogi da ya ce ya yi murabus ne saboda bai son hare-haren Amurka da gwamnatin Bola Tinubu kan yan bindiga
  • Ya bayyana labarin a matsayin sharri da ƙoƙarin bata masa suna tare da haddasa sabani tsakaninsa da Shugaba Tinubu da gwamnatin tarayya

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Abuja - Tsohon ministan tsaro da ya yi murabus, Alhaji Mohammed Badaru Abubakar ya magantu bayan ajiye mukaminsa a makon nan.

Badaru Abubakar ya soki masu yadda jita-jita kan dalilin ajiye aikinsa inda ya bukaci al'umma su yi hankali da irin wadannan labaran karya.

Badaru ya soki masu yada karya kan murabus dinsa
Tsohon ministan tsaro, Mohammed Badaru Abubakar. Hoto: Mohammed Badaru.
Source: Twitter

Murabus: Badaru ya soki masu yada karya

Kara karanta wannan

Abubuwan da 'yan Najeriya ke fatan samu daga sabon ministan tsaro, Janar Musa

Legit Hausa ta samu wannan bayani ne daga shafinsa na Facebook wanda ya wallafa a yau Laraba 3 ga watan Disambar 2025.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Tsohon ministan ya ce abin takaici ne yadda mutane ke yada karya ba tare da tantacewa ba ko sanin gaskiyar lamarin.

Ya ce:

"Na samu wani rubutu da ke yawo a intanet yana ikirarin cewa na ce na yi murabus saboda ba na son ganin ana kai hare-hare kan ‘yanuwanmu ba.
"Ina bayyana haka a fili cewa wannan labari karya ne da tsagwaron sharri, domin ba daga gare ni ko wani wakili na ya fito ba kwata-kwata.
"Manufar wadanda suka kirkiri wannan labari ita ce su bata sunana, su tada fitina tsakanina da Shugaba Bola Ahmad Tinubu tare da kawo rudani."
Badaru ya yi karin haske kan dalilin murabus dinsa
Tsohon ministan tsaro, Mohammed Badaru Abubakar. Hoto: Defence Headquarters Nigeria.
Source: Facebook

Badaru ya fadi dalilin murabus dinsa

Badaru ya ce tuni ya sanar da shugaban kasa, Bola Tinubu game da dalilin murabus dinsa wanda ya amince ba tare da bata lokaci ba.

Tsohon gwamnan Jigawan ya sake jaddada goyon bayansa ga gwamnatin Tinubu domin samun nasarori ta kowane bangare.

Kara karanta wannan

An taso Nuhu Ribadu a gaba, an bukaci Tinubu ya sauya shi da tsohon soja

"Na sanar da gaskiyar dalilin murabus dina ga Shugaban Kasa tun farko, kuma an bayyana hakan ta kafofin sada zumunta da jaridu cikin cikakken bayani.
"Ina sake tabbatar da goyon baya ga Shugaban Kasa, jam’iyyar APC da al’ummar Nigeria wajen wanzar da zaman lafiya, tsaro da ci gaban kasar nan baki daya."

Har ila yau, Badaru ya tabbatar da cewa har yanzu yana nan daram a jam'iyyar APC kuma zai ci gaba da ba ta goyon baya don tabbatar da samun nasararta.

Ya kara da cewa:

"Haka kuma ina nan daram cikin shirye-shiryen ciyar da jam’iyyarmu gaba, musamman yayin da ake fuskantar zaben shekara ta 2027 domin samun nasara mai dorewa."

Ana zargin Matawalle zai iya rasa kujerarsa

An ji cewa ana zargin cewa karamin ministan tsaro, Bello Matawalle zai iya bin sahun tsohon minista, Mohammad Badaru Abubakar.

An ce akwai yiwuwar cewa Shugaba Bola Tinubu zai sake korar wasu manyan jami’an tsaro bisa bin shawarar tsaro da Amurka ta ba shi.

Wasu na ganin cewa rahotanni daga shugaban kasa sun ce Amurka ta nemi a sake tsarin tsaro gaba ɗaya domin kawo karshen masu tayar da ƙayar baya.

Kara karanta wannan

An gano wanda zai iya maye gurbin Badaru a matsayin ministan tsaro

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.