Kano: Gwamnati Ta Yi Bayani kan Dokar Hana Acaba, An Yi Sassauci a Wasu Yankuna

Kano: Gwamnati Ta Yi Bayani kan Dokar Hana Acaba, An Yi Sassauci a Wasu Yankuna

  • Gwamnatin jihar Kano ta tabbatar da cewa dokar hana acaba ta 2013 tana nan daram, ba a soke ta ba domin tabbatar da tsaron rayuka
  • Kwamishinan shari'a na jihar, AbdulKarim Maude SAN, ne ya jaddada haramcin a yayin taro da manema labarai yayin da ake zaman fargaba kan batun
  • Ya ce babu wanda aka amince ya yi achaba a kwaryar birni, amma akwai wuraren da aka sassauta dokar bayan an cika wadansu sharudda

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Kano Gwamnatin Kano ta sake bayyana cewa dokar hana zirga-zirgar acaba, da aka samar a jihar domin ceton rayuka jama'a na nan daram.

Wannan bayanin ya fito ne daga bakin Kwamishinan Shari’a na jihar, AbdulKarim Maude SAN, yayin taron ’yan jarida da aka gudanar a Kano.

Kara karanta wannan

Ba wasa: Matakin da Gwamna Abba zai dauka don dakile hare haren 'yan bindiga a Kano

Gwamnatin Kano ta ce dokar hana achaba na nan daram
Kwamishinan yan sandan Kano, Abba Kabir Yusuf Hoto: Abdullahi Haruna Kiyawa/Abba Kabir Yusuf
Source: Facebook

A cikin wani sautin murya da Arewa Updates ta wallafa a Facebook, Maude SAN ya lissafa yankunan da doka ta hana ganin babura masu daukar fasinja.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

An haramta achaba a kwaryar birnin Kano

A cikin sakon, AbdulKarim Maude SAN ya ce haramcin ya fi karfi a cikin kwaryar birnin Kano, wato kananan hukumomin da suka hada da Kano Municipal, Gwale, Nassarawa, Tarauni, Ungogo ta Kudu da Fagge.

Kwamishinan ya nanata cewa dokar ba wai sabuwa ba ce, kuma za ta ci gaba da aiki domin kare tsaro da inganta tsarin sufuri a cikin manyan titunan Kano.

Ya ce gwamnatin jihar ba za ta yi wasa da wannan doka ba, kuma za a hukunta dukkanin wadanda aka kama da watsi da shi.

An yi sassaucin acaba a wasu sassan Kano

Sai dai Maude ya bayyana cewa akwai wasu kananan hukumomi a wajen tsakiyar birni da aka yi wa doka sassauci. Amma duk mai son yin achaba a wadannan wurare dole ne ya cika wadansu sharudda.

Kara karanta wannan

Barazanar 'yan bindiga: Gwamnatin jihar Kano ta yi magana kan 'yan acaba

Gwamnatin Kano ta ce akwai ana son kare rayukan jama'a
Gwamnan Kano, Injiniya Abba Kabir Yusuf Hoto: Abba Kabir Yusuf
Source: Facebook

A kalamansa:

“Sai ya yi rajista da mai unguwa, sai kuma ya yi rajista da karamar hukuma, sannan sai ya sake rajista da ofishin ’yan sanda na yankin.”

Ya jaddada cewa wannan tsari yana aiki tun daga 2013, kuma an tsara shi domin gWAMgWAM tsafta da ingantaccen tsari a harkar sufuri a Kano.

AbdulKarim Maude SAN, ya ce rajistar ba za a dauke dokar da wasa ba saboda tana taimaka wa gwamnati da jami’an tsaro wajen aikinsu.

AbdulKarim Maude SAN ya gargadi masu karya doka cewa hukuncin dokar ya tsaya: daurin watanni shida ko tarar N10,000 ko ma duka biyun.

Ya ce:

“Gwamnatin Kano na kira da babbar murya da a tabbatar an bi doka yadda ya kamata domin kare rayuka da dukiyoyin al’umma.”

Gwamnatin Kano ta magantu kan achaba

A baya, mun wallafa cewa gwamnatin Jihar Kano ƙarƙashin Abba Kabir Yusuf ta bayyana cewa tana bibiyar korafe-korafe daga jama’a game da yadda sana’ar achaba ke kokarin dawowa.

Kara karanta wannan

Gwamnatin Kogi ta sha alwashi bayan 'yan bindiga sun tattaro fasto da masu ibada a coci

A cikin sanarwar da Kwamishinan Yaɗa Labarai na jihar, Ibrahim Waiya ya fitar, ya ce gwamnati na da rahotanni masu tabbatar da cewa ’yan acaba sun fara bayyana a manyan tituna da unguwanni daban-daban na Kano.

Sanarwar ta ce har ma wasu kananan hukumomi da ke iyaka da Kano suna fuskantar irin wannan matsala, lamarin da ya kara tabbatar da bukatar daukar matakai na musamman domin tsaro.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano. aisha.ahmad@corp.legit.ng