An Taso Nuhu Ribadu a Gaba, an Bukaci Tinubu Ya Sauya Shi da Tsohon Soja

An Taso Nuhu Ribadu a Gaba, an Bukaci Tinubu Ya Sauya Shi da Tsohon Soja

  • An taso Shugaba Bola Tinubu ya gaba da sauya mai ba shi shawara kan harkokin tsaro a Najeriya, Malam Nuhu Ribadu
  • Sanata Francis Fadahunsi ya bukaci Tinubu ya nada tsohon hafsan soja a matsayin NSA, yana cewa hakan ne kawai zai tabbatar tsaro
  • Fadahunsi ya yaba da nadin tsohon hafsan tsaro, Christopher Musa, kuma ya ce lokaci ya yi da ake bukatar ƙwararrun sojoji

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Abuja - Sanatan Osun ta Gabas, Francis Fadahunsi, ya roki Shugaba Bola Ahmed Tinubu da ya ci gaba da gyara tsarin tsaro.

Sanatan ya bukaci gyaran ne ta hanyar nada wani tsohon soja a matsayin mai ba da shawara kan tsaro na kasa (NSA).

An bukaci Tinubu ya kori Ribadu daga mukaminsa
Mai ba shugaban kasa shawara kan tsaro, Nuhu Ribadu da Shugaba Bola Tinubu. Hoto: Nuhu Ribadu, Asiwaju Bola Tinubu.
Source: Facebook

An roki Bola Tinubu ya sallami Nuhu Ribadu

Hakan na cikin wata sanarwa da Mai taimaka masa kan harkokin labarai, Sam Segun-Progress, ya fitar, cewar Punch.

Kara karanta wannan

An gano wanda zai iya maye gurbin Badaru a matsayin ministan tsaro

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Fadahunsi ya ce ya dace a mayar da NSA na yanzu, Mallam Nuhu Ribadu, zuwa wani bangare na gwamnati da zai fi dacewa da kwarewarsa.

Ya tunatar da cewa a baya ya yi kira da a yi gyara mai tasiri a rundunar tsaron Najeriya, yana mai jaddada cewa matsalar ita ce wadanda ke kan shugabanci ba sojoji ba ne.

A wata tattaunawa da aka yi da shi a majalisa, Fadahunsi ya ce:

“Ministan tsaro ba soja ba ne. karamin ministan ma duk ‘yan kasuwa ne. NSA shi ma tsohon dan sanda ne. Sojoji ba sa daukar umarni daga wadanda ba manyan hafsosin su ba.”
Bayan murabus din Badaru, ana neman sauke Ribadu
Mai ba shugaban kasa shawara kan harkokin tsaro, Malam Nuhu Ribadu. Hoto: Nuhu Ribadu.
Source: Facebook

Fargabar da sanata ke da shi kan tsaro

Sanatan ya ce idan Shugaban kasa bai sake duba tsarin tsaron da ke kewaye da shi ba, za a ci gaba da bata kudi ba tare da sakamako ba.

Yayin da yake mayar da martani kan murabus din tsohon ministan tsaro Mohammed Badaru da kuma nadin tsohon hafsan tsaro, Christopher Musa, Fadahunsi ya yaba da matakin, yana mai cewa abu ne mai kyau.

Kara karanta wannan

Babbar magana: Ministan tsaro, Mohammed Badaru Abubakar ya yi murabus

Sai dai ya kara da cewa dole ne Shugaban kasa ya kara kawo gyara ta hanyar sauya Ribadu domin inganta tsaro.

“A sauya Nuhu Ribadu da wani tsohon hafsan soja domin samun daidaito da ingantacciyar jagoranci a yaki da ‘yan bindiga da sauran miyagun laifuffuka.”

- Francis Fadahunsi

Ya ce wadanda ke rike da manyan mukaman tsaro sun yi iya kokarinsu, amma yanzu lokaci ne da ya dace a mika ragamar ga masu cikakken tarihi da kwarewa a fagen soja.

'Dan majalisar ya ce hakan zai ba su dama domin su jagoranci aiwatar da hangen nesan shugaban kasa wurin dakile miyagu a Najeriya, cewar Daily Post.

An roki Tinubu ya bar Matawalle a kujersa

A wani labarin, Kungiyar Northern Stakeholders Consultative Initiative, (NSCI) ta nuna damuwa kan kiraye-kiraye da ake yi cewa a kori Bello Matawalle.

Ta roki Shugaba Bola Tinubu ya ci gaba da rike Karamin ministan tsaron a kujerarsa bayan saukar Mohammed Badaru Abubakar daga mukaminsa.

Kungiyar ta ce Matawalle yana taka muhimmiyar rawa wajen tsare-tsare na tsaro a Arewa tare da samun goyon bayan al’umma domin kawo karshen yan ta'adda.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.