Jigon APC Ya Fadawa Majalisa Mutum 1 da Ya Kamata a Cire a Jerin Sababbin Jakadu
- Wani babban jigon jam'iyyar APC, Denge Onoh ya sake jaddada adawa da nadin Reno Omokri a matsayin jakadan Najeriya
- Onoh, tsohon mai magana da yawun Shugaba Bola Tinubu, ya bukaci majalisar dattawa da ta yi watsi da nadin Omokri
- Ya gargadi majalisar cewa nadin Omokri zai zama barazana ga martabar Najeriya, yayin da ya gabatar da dalilansa
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Abuja - Denge Onoh, tsohon dan majalisar jihar Enugu ya yi kira ga majalisar dattawa da ta soke nadin Reno Omokri a matsayin sabon jakadan Najeriya.
Onoh, wanda tsohon mai magana da yawun Shugaba Bola Tinubu ne a yankin Kudu maso Gabas ya yi rokon ne a wata sanarwa da ya fitar a Abuja.

Source: Twitter
Jigon APC ya fito da matsalolin Reno Omokri
Tsohon dan majalisar, ya ce wannan bukatar da ya gabatar, ba wai bukata ce ta kashin kansa ba, illa dai bukatar kare mutuncin Najeriya, in ji rahoton Vanguard.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
A cewar Onoh, Omokri ya shafe shekaru yana yada wasu kalaman da suka kai ga zargin cewa Shugaba Tinubu “dan kwaya ne” kuma "dillalin miyagun kwayoyi ne.”
Ya ce Omokri ya yi amfani da sunaye daban-daban, ya wallafa littattafai, rubuce-rubuce a jaridun gida da waje, da sakonnin sada zumunta wajen shafawa Tinubu bakin fenti.
Jigon na APC ya ce ko kadan bai kamata a bar mutum kamar Omokri ya zama shi ne wakilin Najeriya a wata kasa ba, "domin hakan zai zubar da martabar Najeriya."
'Kuskuren nada Omokri jakada' - Jigon APC
Onoh ya yi bayanin cewa takardar Letters of Credence da za a ba jakada na kunshe da kalmomin da ke nuna shugaban kasa na da cikakken amincewa ga wanda aka nada.
Ya ce idan Omokri ya karbi irin wannan takarda daga hannun mutumin da ya zarga da aikata miyagun laifuffuka, to hakan zai ba kasashen duniya damar cewa Najeriya ta tabbatar da zancensa.
Onoh ya ce kasashen waje za su yi amfani da bayanan da Omokri ya riga ya yada su wajen nuna cewa gwamnatin Najeriya ta amince da zarginsa.
Ya ce hakan zai iya jawo wa ’yan Najeriya karin matsaloli, ciki har da karin tsangwama, karancin amincewa, matsalolin biza, da tozarci.
Jigon na APC ya kara da cewa hakan zai dagula alakokin diflomasiyya, ya kuma bata huldar leken asiri tsakanin Najeriya da kasashen waje.

Source: Twitter
An nemi majalisa ta soke nadin Omokri
Denge Onoh ya ce Majalisar Dattawa, wadda ke da alhakin kare martabar kasa da dakile kuskuren bangaren zartarwa, dole ta tsaya tsayin daka kan wannan batu.
Ya kuma jaddada cewa Najeriya na bukatar jakadu masu kima da mutunci, ba wadanda za su rage darajar kasar daga tashin farko ba.
A karshe Onoh ya yi kira da cewa majalisar ta yi watsi da nadin Omokri domin kare mutuncin kasa da martabar shugabancin Najeriya.
Omokri ya ce Tinubu ya cancanci tazarce
A wani labari, mun ruwaito cewa, Reno Omokri ya ce zabukan cike gurbi sun nuna amincewar ’yan Najeriya da shugabancin Bola Tinubu da APC.
Tsohon hadimin shugaban kasar ya gabatar da wasu dalilai 20 da ya ce za su sanya 'yan Najeriya su sake zabar Tinubu a 2027.
Dalilan da Reno Omokri ya kawo sun haɗa da daidaita tattalin arziki, sabon mafi ƙarancin albashi, kari a GDP, ingantaccen tsaro, da dai sauransu.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng


