Matakin da za a Dauka idan Aka Kama Jami'in 'Dan Sanda Yana Gadin Babban Mutum

Matakin da za a Dauka idan Aka Kama Jami'in 'Dan Sanda Yana Gadin Babban Mutum

  • Rundunar 'yan sanda ta tabbatar da cewa duk jami’in da aka kama yana tsaron manyan mutane zai fuskanci hukunci mai tsanani
  • Babban sufetan 'yan sanda, IGP Kayode Egbetokun ya umarci kwamishinoni su kama duk jami'in da ya karya wannan sabuwar doka
  • Tun da fari, Shugaba Bola Tinubu ya bada umarnin janye 'yan sanda daga manyan mutane, inda aka ce su koma amfani da jami'an NSCDC

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Abuja - Rundunar 'yan sandan Najeriya ta fitar da gargaɗi mai karfi cewa duk jami’in da aka kama yana yi wa manyan mutane rakiya ko gadinsu zai fuskanci hukunci.

Rundunar ta ce gadi ko rakiyar manyan mutane yanzu ba aikin 'yan sanda ba ne, bisa sabon umarni da Sufeto Janar na ƴan sanda, Kayode Egbetokun, ya bayar.

Kara karanta wannan

Ta fasu: An fallasa shirin raba Atiku da duniya kafin zaben 2027

Rundunar 'yan sanda ta gargadi jami'anta kan gadin manyan mutane
Babban sufetan 'yan sandan Najeriya, IGP Kayode Egbetokun a ofishinsa yana aiki. Hoto: @PoliceNG
Source: Twitter

Za a fara daukar mataki kan 'yan sanda

Jami’in hulɗa da jama’a na rundunar, Benjamin Hundeyin, ne ya bayyana haka a ranar Talata yayin wata tattaunawa a shirin 'siyasa a yau' na Channels TV.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya tabbatar cewa an janye dukkan jami’an 'yan sanda da ke tsaron manyan mutane gaba ɗaya, kuma ana ci gaba da bincike tare da kama masu karya doka a faɗin ƙasar.

“Ana aiwatar da wannan umarni. Sufeta Janar ne ya bayar da umarnin cewa duk jami’in da aka gano yana tsaron manyan mutane a kama shi domin yana yin aikin da aka haramta yanzu.

Benjamin Hundeyin ya kara da cewa an umurci babban kwamishina mai kula da sashen tsaro na musamman (SPU) da ya sanya mutane a filin jirgin saman Abuja domin kama duk wani ɗan sanda da aka gani yana rakiyar babban mutum.

Haka kuma, kwamishinan ƴan sanda na Legas ya samu irin wannan umarni na zuwa filin jirgin saman Legas domin kama jami’an da suka saba doka.

Kara karanta wannan

Matafiya sun shiga tsaka mai wuya yayin da 'yan sanda suka fafata da 'yan bindiga

Wadanda ke karkashin tsaron 'yan sanda

Sai dai ya yi karin haske cewa akwai manyan jami’an gwamnati da doka ta tanadar musu kariya ta ƴan sanda, kuma za su ci gaba da samun wannan tsaro har sai an samu sabon umarni daga fadar shugaban kasa.

Kakakin rundunar ya bayyana cewa gwamnoni da alkalan kotu na daga cikin waɗanda har yanzu suke da kariyar jami’an ƴan sanda.

Sabon matakin dai ya biyo bayan umarnin Shugaba Bola Ahmed Tinubu wanda ya ce a janye ƴan sanda daga manyan mutane domin mayar da su kan muhimman ayyukan tsaro, musamman a yankunan karkara da ake fama da ƙarancin jami’an tsaro.

Rundunar 'yan sanda ta ce yanzu haramun ne 'yan sanda su rika gadin manyan mutane.
CSP Benjamin Hundeyin, sabon mai magana da yawun rundunar 'yan sandan Najeriya. Hoto: @BenHundeyin
Source: Twitter

Janye 'yan sanda daga manyan mutane

A karkashin wannan sabon tsari, duk wani babban mutum da ke bukatar kariya mai ƙarfi ya nemi jami’ai daga hukumar NSCDC, ba daga ƴan sanda ba.

Mai magana da yawun shugaban kasa, Bayo Onanuga, ya ce wannan mataki na nufin mayar da ƴan sanda kan aikin su na hakika na kare rayuka da dukiyoyi.

Kara karanta wannan

Dubun masu garkuwa da mutane ta cika: An cafke hatsabiban 'yan bindiga a Zamfara

Wannan cigaba na zuwa ne a daidai lokacin da Shugaba Tinubu ya ayyana dokar ta-baci kan harkokin tsaro a faɗin Najeriya, sakamakon yawaitar garkuwa da mutane da hare-haren ta’addanci a sassa daban-daban.

A wani bangare na martanin gwamnati, an amince da daukar karin jami’an ƴan sanda 20,000 domin su zama 50,000, tare da karin yawan sojojin da za a dauka domin yaki da matsalolin tsaro.

'Yan sanda sun janye daga gadin manya

A wani labarin, mun ruwaito cewa, sashen SPU na rundunar 'yan sanda ya aika sako ga dukkannin jami'an da ke aikin gadin manyan mutane da wurare na musamman a fadin Najeriya.

Sashen ya ba jami'an 'yan sandan umarnin gaggawa na janye wa daga gadin duk wani babban mutum ko manyan wurare, bayan umarnin Shugaba Bola Tinubu.

Kwamandar SPU Base 16 da ke Legas, Neji Veronica ta ce matakin zai taimaka wajen tura jami'ai a yankunan karkara inda ofisoshin ’yan sanda ke fama da karancin jami'ai.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com