Yan Arewa Sun Roki Tinubu game da Kujerar Matawalle, Sun Fadi Tasirin Ministan
- Kungiyar Northern Stakeholders Consultative Initiative, (NSCI) ta yi magana bayan jin jita-jitar cewa za a kori Bello Matawalle
- Ta bukaci Bola Bola Tinubu ya ci gaba da rike Matawalle a kujerarsa bayan saukar Mohammed Badaru Abubakar daga mukaminsa
- NSCI ta ce Matawalle yana taka muhimmiyar rawa wajen tsare-tsare na tsaro a Arewa tare da samun goyon bayan al’umma
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Abuja - Kungiyar Northern Stakeholders Consultative Initiative (NSCI) ta roki alfarma wurin shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu.
Kungiyar ta bukaci Mai girma Bola Tinubu da ya ci gaba da rike karamin ministan tsaro, Mohammed Bello Matawalle a mukaminsa.

Source: Twitter
Kungiya ta jaddada tasirin Matawalle a gwamnati
Hakan na cikin wata sanarwa da mai magana da yawun kungiyar, Yerima Shettima ya sanya wa hannu, cewar Tribune.

Kara karanta wannan
Wata sabuwa: IPI ta sa kafar wando daya da sufetan yan sanda da gwamnoni 2 a Najeriya
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
NSCI ta ce wajibi ne a sake jaddada muhimmancin Matawalle ga gwamnatin Tinubu, musamman wajen karfafa tsaro da tabbatar da zaman lafiya a Arewa.
Kungiyar ta kara da cewa Matawalle ya kasance ginshiki a aiwatar da shirye-shiryen tsaro a Arewa, kuma yana da goyon bayan jama’a a yankin.
'Kokarin da Matawalle ke yi a harkar tsaro'
NSCI ta bayyana cewa yadda Matawalle ke jagorantar tsare-tsaren tsaro na gwamnatin tarayya ya kara kwarin gwiwa a al’ummomi.
Har ila yau, ta ce yana kuma tattaunawa da shugabannin yankuna ta inganta hadin kai tsakanin gwamnati da jama’a a kokarin kawo karshen matsalar tsaro.
Ta ce kasancewar Bello Matawalle a cikin gwamnati yana ba tsare-tsaren tsaro ci gaba, musamman a wannan lokaci da ake fama da matsalolin tsaro.
Kungiyar ta jaddada cewa ana bukatar shugaban ka da ya canza shi domin ci gaba da aiwatar da dabarun tsaron kasa, kamar yadda Vanguard ta ruwaito.

Kara karanta wannan
Guinea Bissau: Gwamnatin Tinubu ta faɗi halin da Jonathan ke ciki bayan ya maƙale

Source: Original
Shawarar da kungiyar ta ba 'yan Najeriya
Sanarwar ta kuma yi nuni da mahimmancin kiyaye hadin kai da karfafa amincewa da hukumomin gwamnati, tare da bukatar Shugaba Tinubu ya ci gaba da mara wa mukarraban da ke aiki tukuru baya.
Shettima ya ce:
“Muna ganin cewa ci gaba da amfani da kwararru masu gogewa yana da matukar muhimmanci ga nasarorin da ake samu a fannoni daban-daban."
Kungiyar ta kuma bukaci ‘yan kasa da kafafen yada labarai da su mayar da hankali wajen tattaunawa ta gina kasa, domin matsalolin tsaro suna bukatar hadin kai gaba daya.
A karshe, NSCI ta tabbatar da shirinta na ci gaba da aiki tare da gwamnati da sauran masu ruwa da tsaki domin samar da zaman lafiya da cigaba a yankin Arewa.
Badaru ya yi murabus daga mukaminsa
Mun ba ku labarin cewa Ministan tsaro, Mohammed Badaru Abubakar ya rubuta wasika ga Bola Tinubu domin ajiye mukaminsa a jiya Litinin 1 ga watan Disambar 2025.
Badaru ya yi murabus ne daga majalisar FEC ta gwamantin Bola Tinubu a jiya Litinin kuma shugaban kasa ya amince da hakan ba tare da bata lokaci ba.
Tuni Tinubu ya rubuta sunan tsohon hafsan tsaron Najeriya, Christopher Musa domin maye gurbin Badaru a mukaminsa.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Asali: Legit.ng
