Tashin Hankali: Ƴan Sa Kai Sun Buɗe wa Dakarun Sojojin Ƙasar Nijar Wuta a Katsina

Tashin Hankali: Ƴan Sa Kai Sun Buɗe wa Dakarun Sojojin Ƙasar Nijar Wuta a Katsina

  • Wasu 'yan sa kai sun bude wuta kan sojojin kasar Nijar a lokacin da suka je dibar ruwa a garin Mazanya, jihar Katsina
  • An rahoto cewa, 'yan sa kan sun yi tunanin cewa dakarun na Nijar 'yan bindiga ne, ganin yadda suka shiga garin a ayari
  • Yayin da hedikwatar tsaro ta ce an shawo kan matsalar, masana sun fadi illar ƙarancin haɗin kai tsakanin kasashen biyu

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Katsina - A wani lamari mai tayar da hankali, ’yan sa-kai na yankin Mazanya a karamar hukumar Jibia, jihar Katsina sun bude wuta kan ayarin motocin sojojin kasar Nijar.

An rahoto cewa, 'yan sa kan Najeriya sun bude wa dakarun sojojin Nijar wuta ne a lokacin da dakarun suka shiga yankin domin ɗibar ruwa.

Kara karanta wannan

'Yan bangan Najeriya sun budewa sojojin kasar Nijar wuta, Hedikwatar tsaro ta yi bayani

An samu musayar wuta tsakanin 'yan sa kan Najeriya da sojojin kasar Nijar a Katsina.
Dakarun sojojin kasar Nijar suna tafiya a kan babbar hanya. Hoto: @ZagazOlaMakama
Source: Twitter

'Yan sa kai sun bude wuta kan sojojin Nijar

Shaidu sun ce lamarin ya faru ne da misalin ƙarfe 2:00 na rana, lokacin da sojojin suka shiga yankin a manyan motocin yaki hudu da wata Toyota Jeep, in ji rahoton The Cable.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

An ce 'yan sa kai da ke sintiri sun yi zaton cewa motocin dakarun sojojin na ’yan bindiga ne da ke kai hare-hare a yankunan Katsina da kan iyaka.

Saboda ba su da masaniyar zuwan sojojin, da kuma yadda suka ga ayarin motocin, an je 'yan sa kan sai suka bude musu wuta.

Sai dai, rahoto ya nuna cewa su ma dakarun sojojin Nijar sun mayar da martani, lamarin da ya jawo musayar wuta tsakanin bangarorin biyu.

Hedikwatar tsaro ta yi karin haske

A sanarwar da ya fitar, Daraktan Hulɗa da Jama’a na hedikwatar tsaro, Manjo Janar Michael Onoja, ya tabbatar da faruwar lamarin.

Kara karanta wannan

Mai martaba sarki da aka sace a Kwara ya gudo daga hannun masu garkuwa da mutane

Manjo Janar Michael ya bayyana cewa an shawo kan matsalar bayan tattaunawa da kwamandan dakarun Nijar da ke wurin.

Kakakin hedikwatar tsaron ya ce an ba wa sojojin ikon kammala ɗibar ruwa tare da komawa ƙasarsu ba tare da wata matsala ba.

A cewar hedikwatar tsaro, an gudanar da babban taron tsaro tsakanin manyan kwamandoji na kasashen biyu a ranar 1 ga Disamba domin karfafa haɗin gwiwa a kan iyaka.

Hedikwatar tsaro ta ce ta shawo kan matsalar bayan tattaunawa da sojojin Nijar.
Jami'an tsaro da suka hada da sojoji na gudanar da bincike a kan titi. Hoto: @ZagazOlaMakama
Source: Twitter

Bukatar duba alakar sojojin Nijar da Najeriya

Najeriya da Nijar, in ji sanarwar, suna da dogon tarihi na alakar tsaro, kasuwanci da hulɗar al’adu.

Manjo Janar Onoja ya kara da cewa kasashen biyu suna fuskantar barazanar ’yan ta’adda, masu safarar mutane, masu fashi, da sauran barazanar da ke shafar iyakoki, don haka ana bukatar tsauraran matakai na hadin kai.

Shahararren mai sharhi kan tsaro, Zagazola Makama, ya wallafa a shafinsa cewa irin wannan rashin fahimtar tsakanin dakarun kasashen na iya jawo mummunar barna.

Zagazola ya bukaci a kafa tsarin sintirin gwiwa, rarraba bayanan sirri a lokaci-lokaci, da daidaitaccen tsarin da zai hana irin rikicin Mazanya faruwa a nan gaba.

Kara karanta wannan

Sojoji sun yi musayar wuta da 'yan ta'adda a Kano, an nemi wasu mutane an rasa

Sojoji sun shafe kwanaki suna fada

A wani labari, mun ruwaito cewa, rundunar sojin Najeriya ta kaddamar da jerin hare-haren hadin gwiwa daga 29, Nuwamba, 2025 zuwa 1, Disamba, 2025.

An kashe mutane 8 da ake zargi da ta’addanci, an kama 51 yayin da aka ceto wasu 27 a fafutukar da ta shafi Arewa da Kudancin kasar.

Daga cikin nasarorin da suka samu, sojoji sun kwato bindigogi, harsasai, wayoyin sadarwa, wasu kayan da aka sata, abubuwan fashewa da kuma shanu 76 da aka sace.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com