Rigima Ta Barke a Majalisa, Sanata Goje Ya Ci Gyaran Akpabio kan Sanin Aiki

Rigima Ta Barke a Majalisa, Sanata Goje Ya Ci Gyaran Akpabio kan Sanin Aiki

  • An samu rigima a majalisar dattawa bayan Sanata Muhammad Danjuma Goje ya soki Shugaban Majalisar, Godswill Akpabio
  • Sanatan na jihar Gombe ya zargi Akpabio da yin abubuwan da suka sabawa dokokin majalisa yayin zaman ranar Talata a Abuja
  • Goje ya yi barazanar kin amincewa da duk wata tattaunawa da Akpabio ke yi a kujerarsa, yana mai cewa irin wannan tattaunawa "ba ta halatta ba"

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Abuja - Majalisar dattawa na ranar Talata 2 ga watan Disambar 2025 ya rikice bayan Sanata Danjuma Goje ya yi maganganu.

Sanatan APC daga Gombe ta Tsakiya ya yi wa Shugaban Majalisar, Sanata Godswill Akpabio, raddi mai zafi game da shugabancinsa.

Goje ya kalubalanci Akpabio a majalisa
Sanata Danjuma Goje daga jihar Gombe. Hoto: The Nigerian Senate.
Source: Twitter

Abin da ya haɗa Goje, Akpabio rigima

Rahoton Vanguard ya ce Sanata Goje yana zarginsa da aikata abin da ya sabawa dokokin majalisa.

Kara karanta wannan

Shugaba Tinubu ya nada sabon Ministan tsaro bayan murabus din Badaru

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Rikicin ya barke ne bayan Akpabio ya shiga zauren majalisa, ya karɓi kujera daga mataimakinsa, Sanata Jibrin Barau na APC daga Kano ta Arewa.

Daga bisani, bayan ya zauna a kujerar, Akpabio ya kira Sanata Opeyemi Bamidele da wasu shugabanni su matso kusa da kujerar domin wani gajeren taro.

Wannan mataki ne ya fusata Sanata Goje, wanda ya mike nan take yana mai cewa ba a yarda ayi irin wannan tattaunawa a cikin zaman majalisa ba.

Ya ce:

“Mai girma Shugaban Majalisa, abin da kake yi na saba aikin majalisa, Kana dakile ayyukan majalisa.”

Akpabio ya kira Goje ya zo wajen kujerar domin ya haɗu da su, amma Goje ya ki yarda, yana mai cewa ba zai shiga abin da ya kira “haramtaccen taro” ba.

Ya kara da cewa komai ya tsaya cak, babu harkar majalisa da ake yi yanzu saboda ganawar da suke yi ba bisa ka'ida ba.

Kara karanta wannan

Babbar magana: Ministan tsaro, Mohammed Badaru Abubakar ya yi murabus

Kokarin Akpabio na sasanta lamarin bai yi tasiri ba, domin Sanata Goje ya dage cewa sanatoci da aka gayyato wajen kujerar su koma wurinsu domin majalisa ta ci gaba yadda doka ta tanada.

An ci gyaran Akpabio kan shugabancin majalisa
Shugaban majalisar dattawa, Sanata Godswill Akpabio. Hoto: Godswill Akpabio.
Source: Facebook

Kokarin Akpabio na fahimtar da Goje ya ci tura

Akpabio ya ce ya za a tattauna ne kan batun gaggawa da ke shirin faruwa a fadar shugaban kasa da misalin karfe 1:00 na rana, cewar The Nation.

Sai dai duk bayanin bai sauya ra’ayin Goje ba, wanda ya ce:

“Ba zan zo ba. Abin da kuke yi ba doka ba ce. Ba zan shiga ciki ba.”

Akpabio daga baya ya bayyana cewa yana sauri ne zuwa wurin kaddamar da Tambarin Rundunar Sojojin Najeriya da za a yi a fadar shugaban ƙasa.

Zaman majalisar ya ci gaba bayan 'yar tangarda, amma tashin hankalin ya kara tabbatar da cewa akwai sabani mai karfi tsakaninsu kan yadda ake tafiyar da majalisa.

Akpabio ya shawarci Kiristocin Najeriya

Kun ji cewa Godswill Akpabio ya yi magana game da albarkar da Ubangiji ya yi masa a rayuwa bayan daga shi zuwa wannan matsayi.

Kara karanta wannan

Sanata Barau ya kausasa harshe kan harin 'yan bindiga a Kano

Ya ce samun mukaminsa har zuwa Shugaban Majalisar Dattawa bai yiwu ba sai da tagomashin Allah.

Ya bayyana cewa ko karamin gudummawa ga aikin coci na da lada, yana mai sanar da shirin kaddamar da sabon wurin ibada a Majalisar Tarayya.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.