Shugaba Tinubu Ya Nada Sabon Ministan Tsaro bayan Murabus din Badaru

Shugaba Tinubu Ya Nada Sabon Ministan Tsaro bayan Murabus din Badaru

  • A jiya Litinin 1 ga wata. Disamban 2025, ministan tsaro Mohammed Badaru Abubakar ya yi murabus daga kan mukaminsa
  • Kwana guda bayan aukuwar hakan, shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya nada sabon minista wanda zai maye gurbinsa
  • Shugaba Tinubu ya dauko tsohon babban hafsan hafsoshi, Janar Christopher Musa domin rike kujerar ministan tsaro

​​Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

FCT, Abuja - Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya zabi wanda yake so ya nada a matsayin sabon ministan tsaro a Najeriya.

Shugaba Bola Tinubu ya dauko Janar Christopher Gwabin Musa domin ya dare matsayin sabon ministan tsaro idan an tantance shi.

Shugaba Tinubu ya nada sabon ministan tsaro
Janar Christopher Musa da Shugaba Bola Ahmed Tinubu Hoto: HQ Nigerian Army, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu
Source: Facebook

Bola Tinubu ya nada Ministan tsaro

Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da mai ba shugaban kasa shawara kan harkokin yada labarai da dabaru, Bayo Onanuga, ya sanya a shafinsa na X.

Kara karanta wannan

An gano wanda zai iya maye gurbin Badaru a matsayin ministan tsaro

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A cikin wata wasika da ya aikawa shugaban majalisar dattawa, Sanata Godswill Akpabio, Shugaba Tinubu ya sanar da cewa Janar Musa ne zai maye gurbin Alhaji Mohammed Badaru Abubakar, wanda ya yi murabus a ranar Litinin.

Wane ne Janar Christopher Musa?

Janar Christopher Musa, wanda zai cika shekaru 58 a ranar 25 ga Disamba, hafsan soja ne mai kwarewa wanda ya rike mukamin babban hafsan tsaro (CDS) daga 2023 zuwa Oktoba 2025.

A shekarar 2012 ya lashe kyautar Colin Powell kan ayyukan soja.

An haifi Janar Christopher Musa a Sokoto a 1967, inda ya yi makarantar firamare da sakandare kafin ya shiga College of Advanced Studies, Zaria wanda ya kammala a shekarar 1986.

Daga baya ya ya shiga makarantar Nigeria Defence Academy (NDA) a shekarar nan take, inda ya samu digiri a fannin kimiyya a 1991.

Ya kai matsayin 'Second Lieutenant a rundunar sojojin kasa a shekarar 1991, kuma ya yi fice a aikinsa har zuwa yau.

Kara karanta wannan

Babbar magana: Ministan tsaro, Mohammed Badaru Abubakar ya yi murabus

Manyan mukaman da ya Janar Musa ya rike

Daga cikin muhimman mukaman da ya rike akwai:

  • Babban jami’in ma’aikata 1 (GSO 1), horaswa/ayyuka, hedkwatar runduna ta 81
  • Kwamandan bataliya ta 73
  • Mataimakin darakta sashen tsare-tsaren rundunar sojoji
  • Wakilin Rundunar sojojin kasa a kwamitin Horaswa na rundunar Armor Corps
  • Mataimakin shugaban ma’aikata (horaswa/aiki), a Infantry Centre and Corps (2019)
  • Kwamandan sashe na 3 na rundunar Operation Lafiya Dole
  • Kwamandan sashe na 3 na rundunar Multinational Joint Task Force (MNJTF) a yankin Tafkin Chadi
Janar Christopher Musa ya zama sabon ministan tsaro
Sabon ministan tsaron Najeriya, Janar Christopher Musa Hoto: @HQNigerianArmy
Source: Facebook

Hakazalika an nada shi shugaban rundunar Operation Hadin Kai a shekarar 2021 daga bisani ya zama Kwamandan Infantry Corps, kafin Shugaba Tinubu ya nada shi babban Hafsan Tsaro (CDS) a 2023.

A wasikar da ya aike wa majalisar dattawa, Shugaba Tinubu ya bayyana cikakken gamsuwarsa da kwarewar Janar Christopher Musa, yana mai cewa zai kara karfafa tsarin tsaron Najeriya a wannan sabon matsayi.

Ministan tsaro ya yi murabus

A wani labarin kuma, kun ji cewa ministan tsaron Najeriya, Alhaji Mohammed Badaru Abubakar, ya yi murabus daga kan mukaminsa.

Kara karanta wannan

Shugaba Tinubu ya sa labule da babban hafsan tsaron Najeriya da ya kora daga aiki

A cewar wata sanarwa da hadimin Shugaba Bola Tinubu ya fitar, ministan ya yi murabus ne saboda dalilai na lafiya.

Murabus ɗin Badaru dai ya biyo bayan ayyana dokar ta-baci kan tsaro da Shugaba Tinubu ya yi, inda ya bayyana cewa za a ƙara fayyace manufar wannan mataki a nan gaba.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng