Awa 12 da Ficewar Gwamna, PDP Ta Gudanar da Zaben Fitar da Gwani babu Shi

Awa 12 da Ficewar Gwamna, PDP Ta Gudanar da Zaben Fitar da Gwani babu Shi

  • Jam'iyyar PDP ta ce babu ja da baya kan gudanar da zaben fitar da gwani domin ta tsaida 'dan takarar gwamnanta
  • An gudanar da zaben ne a yau Talata 2 ga watan Disambar 2025 duk da ficewar Gwamna Ademola Adeleke na Osun
  • An samu barazana a wurin taron, lamarin da ya so jawo matsaloli yayin da jami’an tsaro ke cewa sun magance hakan

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Osogbo, Osun - Awa 12 kacal bayan Gwamna Ademola Adeleke ya fice daga PDP, jam'iyyar ta gudanar da zaben fitar da gwani.

Shugaban PDP na Osun, Sunday Bisi, ya bayyana cewa jam’iyyar ta sanar da cewa za ta gudanar da zaben a ranar Talata, 2 ga Disamba.

Bayan ficewar gwamna, an gudanar da zaben fitar da gwani a Osun
Gwamna Ademola Adeleke wanda ya yi murabus daga PDP. Hoto: Governor Ademola Adeleke.
Source: Twitter

A ranar Litinin, Bisi ya shaida wa wasu ‘yan jarida cewa rikicin da ya jawo dakatarwa da korar manyan shugabannin jam’iyyar, cewar The Nation.

Kara karanta wannan

Atiku ya gana da shugabannin ADC, ya fada masu shirin da za su yi gabanin 2027

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

PDP ta fitar da dan takararta a Osun

A yau Talata 2 ga watan Disambar 2025, Adebayo Adedamola ya lashe tikitin takarar gwamna na jam’iyyar PDP domin zaben gwamnan Osun na 2026.

Adedamola ya samu kuri’u 919 daga cikin kuri’u 957 da aka kada wanda shugaban kwamitin zaben fitar da gwanin, Humphrey Abba ya sanar, cewar Vanguard.

Abba ya ce:

“An samu kuri’un da suka baci guda 20. Mun shaida muku tun da farko cewa ɗaya daga cikin ‘yan takarar ya janye.
"Dan takarar da ya samu sauran kuri’un shi ne Adebayo Adedamola da kuri’u 919, kuma ya zama wanda ya yi nasara.”
PDP ta yi nasarar gudanar da zaben fitar da gwani a Osun
Shugaban PDP a Najeriya, Kabiru Tanimu Turaki. Hoto: Kabiru Tanimu Turaki.
Source: Facebook

Matsayar PDP bayan murabus din gwamna

Ana ganin cewa rikicin jam'iyyar ya sa Gwamna Adeleke ya yi murabus kuma ba zai sake neman takarar kujerarsa a karkashin PDP ba a zaben gwamnan Osun.

Sai dai a martanin da PDP ta kasa ta fitar ta bakin sakataren tsare-tsare, Hon. Theophilus Shan, a cikin wata wasiƙa mai dauke da ranar 1 ga Disamba, 2025, jam’iyyar ta tabbatar da cewa zaben fidda gwanin za a yi shi kamar yadda aka tsara.

Kara karanta wannan

Gwamna Oyebanji ya canza shawara, ya dawo da mafi yawan kwamishinonin da ya kora

Wasiƙar ta ce:

“Bayan sanarwar da aka fitar ranar 28 ga Oktoba, 2025, game da zaben fitar da gwanin da kuma kammala babban taro da na daliget na kasa a Osun ranar 24 da 29 ga Nuwamba, 2025.
Jam’iyya na tunatar da jama’a cewa zaben fidda dan takarar gwamna zai gudana a ranar Talata 2 ga Disamba, 2025, a dakin taro na Atlantis kan hanyar zagaye ta Ring da ke birnin Osogbo, ƙarfe 10:00 na safe.”

An ba gwamna shawarar shiga AP

A baya, kun ji cewa alamu na nuna Gwamna Ademola Adeleke na Osun ya fara laluben jam'iyyar da zai nemi tazarce a karkashin inuwarta a zaben 2026.

Tsohon gwamnan Osun, Prince Olagunsoye Oyinlola ya ce ya fara tattaunawa da Gwamna Adeleke domin neman mafita.

Ya ce a shawararsa, jam'iyyar Accord watau AP ce ta dace Gwamna Adeleke ya nemi tazarcen a zaben gwamna da za a yi a badi.

Kara karanta wannan

Gwamnati za ta kwace filayen Ganduje, Patience Jonathan da wasu manya a Najeriya

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.